Chapter 3
Chapter 3
da saurin baki kuma bata kaurara murya tana da zaki don haka Ku cikin mata dubu ta shiga zai iya gane muryar ta. Wani kiran na kara kwala wa Mimi tare da fad'in"Mimi wai ki ba kya ji ne, Habibin ki ne fa kiyi sauri kar ta katse........ Muryar matar Naji tana fad'in" D'iyar arziki sanun ki kinji Ubangiji Allah yayi miki albarka nagode mutuka zaki auri jikana duk da lalurar da take damun sa....ko da yake naji yace." Kema baki da lafiya, kuyi hakurin insha Allahu zamu shiga mu futa Dom......Kafin ta karasa naji yo muryar sa Yana fad'in"Nifa ba cewa nayi ki wani jawabi ba, cewa nayi Ku gaisa da My wife dina kin tsaya wani zance."!! Ji nayi tace" Matsa ka bani guri don Allah , ai wannan yarinyar ta isa a jinin na mata saboda tayi jahadi.... Dariyar shi na jiyo Yana fadin"Sai kiyi ai."" Ta cigaba da cewa"Allah yayi miki albarka kinji ko." A hankali nace" Ameeen amma bani bace budurwar tashi tana band'aki ni Sunana Asma'u ita kuma Mimi in ta futo za'a..ban k'arasa ba Mimi ta shigo dakin. Nace." Yawwa ga Mimi nan. wayar na mik'a mata na futa daga d'akin. Kwata_kwata ban fuskanci komai ba Dan gane da maganganun da matar take,cikin zuciyata dai nake cewa"K'ila sunyi wata hira ne shi da Mimi tace mishi bata da lafiya, tom ni dai a iya sanina Mimi bata da wata cuta wacce bamu San da ita ba, asalima Mimi bata fiye yin ciwo ba, sai shekara-shekara take zazzab'in nan Wanda ake fama dashi. Cikin zuciyata Naji tausayin ta, kuma nayi alk'awarin sai na tambaye wane ciwo ne yake damunta Wanda har ta kasa fad'ar shi a gida ta tafi waje tana yad'awa... Tsintsaya na dauka na hau share-share dama Umma bata nan taje suna sai mu kadai a gidan. Ta futo daga d'akin sai kace wata Mara gaskiya, kallonta nayi, ni yanzu tausayi take bani ganin yanda ta hada kanta da babban aiki. Sam yanzu na daina jin haushin ta, nace" Kun gama ne " zama tayi kusa dani tare da fadin "Eh, Ashe kakarsa ce wai take so mu gaisa shine ya kira ni." Cike da nazari nake kallonta nace"Mimi wane irin lalura ce dake da har kika kasa fad'ar ta a gida, kika fad'awa saurayi Wanda baki da tabbacin zai aure ki."? Yanda na tsare ta da ido ina tuhumar ta sai ka rantse da Allah uwarta ce ni ko yayarta. Cike da mamaki take kallona tace." Ban gane abunda kike nufi ba."? K'wafa nayi cike da takaici nace"dama baza ki gane ba, naji wannan matar tana fad'in"Zata je ta nemo miki magani dake dashi kuma kinyi jahadi tunda zaki aure shi." Ranta a d'an b'ace ta kalle ni tace"Kinga Asma'u ya zaki tasa ni a gaba kina min wata tambaya kamar wata uwata, ni babu wata magana da mukayi dashi. " Nace" Ok k'arya nayi kenan."!? Tab'e baki tayi tace"ke kika sani kuma" a hasale nace"To ki kiyaye wallahi duk inda kike tunanin wannan guy ya wuce gurin, naga soyayya ta rufe miki ido kina nema ki futa waje ki tona mana asirin gida, duk lalurar da ke damun ki nasan kika fad'awa Umma zata yi miki magani iya iyawar ta, ke da kanki Kin san kafin tayi min Abu tayi miki sau dubu me zai sa ki watsa mata k'asa a ido kije ki zauna kiyi tunani da kyau kafin kowa yasan abunda yake damun ki ita yafi kamata ta sani, amma..........Kinga Asma'u.!'" Mimi ta fada tare da D'aga min hannu a fusace ! Ta mik'e tsaye. "Gwara ki nuna min cewar a gidanku nake zaune,Asma'u gwara kiyi min gori saboda ina zaune a karkashin inuwar Ku, amma ina so ki San wani Abu kin San dai nima ba daga sama na fad'o ba ina da Iyaye ina da dangi masu rufin asiri Ubana yana Raye a duniya sai dai kice ba a gari yake ba, tom insha Allah Allahu zan bar muku gida Asma'u kada wataran ki ce sai na biya Ku kud'in hidimar da iyayen ki suka yi min tun ina jaririya hakan ma na gode." Dugu ta shige dakinmu tana kuka!!! Jikina ne yayi sanyi Mimi daga magana zata yi min wata fassara ta daban, tunda muke da Mimi mu kwana mu tashi guri guda bamu tab'a fad'a na cacar baki ba,ko mu fadawa junanmu munanan kalamai, nice dama mafad'aciya in taga na hau sai ta sauko ko ta maida abun wasa,Mimi bata tab'a gaba dani idan inayi ma dariya take min, tayi min magana har in gaji in sauko. Mik'ewa nayi na bita dakin namu na tsaya bakin k'ofar shiga, ina kallonta tana ta had'a kaya tana kuka, Babu yabo babu fallasa nace" Mimi daga magana zaki yi min wata fassara ta daban, har kike had'a kayan ki, Mimi kina da wani gidan ne bayan wannan? Baki da Uwa da ta wuce Umma kuma baki da 'yan uwa sama damu, idan abunda na fad'a ya b'ata miki rai Allah ya baki hakuri." Nafada ina shigowa d'akin..... Akwatin da take had'a kayan na d'auke ina fad'in"So kike yau Yaya Aminu ya kusa kashe ni a gidanan kenan? Ko so kike Umma ta tsine min.? Kiyi hakuri bazan k'ara yi miki magana irin wannan ba." Mimi mai saukin kai da saukin hali tace." Kin kasa fahimta ta ne Asma'u amma na fada miki babu wata magana da mukayi dashi wai bani da lafiya, idan bani da lafiya sai kin Riga kowa sani tunda tare dake muke kwana muke tashi a daki daya." Domim a zauna lafiya nace"Nagane yanzu mybe shima yana tsokanar kakar tashi ne." Ta goge hawayen ta tare da fadin " ni ma nafi tunanin haka." Akwatin na d'auke na mai da ita inda take, nace"Tashi mu shiga kicin kar Umma ta dawo kin ga magariba ta kusa." Mik'ewa tayi muka futa daga d'akin. ****** *Amjadu* tun lokacin da Granny ta mik'o masa wayarsa bayan sunyi sallama da Mimi yake tunani Muryar yarinyar da yaji ta tayar masa da wani azabbanan fleengs sosai daurewa kawai yake amma yau yana ganin dole ya ragewa kansa damuwa saboda yadda yake jin mararasa na kullewa alamun sparm ya taru sosai. Lumshe idonsa yayi hade da Dan Mike k'afafun sa, jira yake gari yayi duhu a idar da sallahr Magariba yaje ya ragewa kansa damuwa. Domin had'uwar su ta d'azu ta tayar masa da sha'awa kausasan kalaman da tayi amfani dasu ne suka d'auke masa sha'awar ta a lokacin, tayi mugun b'ata masa rai. Granny ta mike tana fadin"kar dai kayi bacci nan da lokaci k'ankani zaka ji kiran sallahr magariba, shiru yayi mata bai ce komai ba, ita kuma ta shige kicin..... Nan massalacin jikin gidan yayi sallahr shi a gurguje ya dawo gidan ko zama bai yi ba, yace." Zan tafi ni." Granny tace"ga abunci can Iyami tana jera maka a daining ya kamata kaje kaci tukkuna. Girgiza kansa yayi yana d'an Sosa kunnen shi da key yace." Na koshi kinsa n bana cin Abu me nauyi da daddare damuna yake." Tab'e baki tayi, yace.' Gobe zan tafi chana kiyi min addu'a." Tace"Allah ya tsare min kai gaba da baya sai ka dawo." "Ammen suma ameen si ba
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78