Chapter 38
Chapter 38
tace."Ni kike cewa 'yar iska." Ko a jikina nace"Yo idan ba 'yar iska bace ke mecece ke. Har da zaki kirani a waya kice na nema miki alfarma gurinsa ya aure ki, ni meye hadina dashi meye damuwa ta dashi, idan auran ki zai yi sai ya nemi amincewa ta tare na ganku ban San sanda kuka had'u ba, saboda haka kar ki kara kira na a waya mtssssss." Kashe wayar nayi ina jin wani mugun takaici lallai ma guy nan Dan rainin hankali ne, haka kawai na tsinci kaina da mugun jin haushin sa dashi da 'yar iskar budurwar tasa, tsaki kurrum nake Tabkawa. Hibbah ta kalleshi ranta a mugun b'ace Tace"Kaga abunda ka janyo min ko.? Na lura yarinyar nan bata da kirki wallahi sai na koya mata zama a garin kano har ni zata bude baki ta gayawa magana irin wannan."!! Dariya yake cikin ransa yace." Indai wannan yarinyar ce halinta ya wuce yanda kike tsammani. A zahiri kuwa cewa yayi "Idan kinga abunda kikayi kina iya tafiya." Hibbah ta mike ranta a bace ta dauki Jakarta tana fadin"Wato ka gama more ni kana ji wata yar iska na zagina kaki ka dauki mataki shikkenan. " murmushi yayi yadan Sosa sumar shi, yace." Nima rarrashin ta nake yi kin San itace ruhina bana son abunda zai b'ats mata rai!!.. Hibbah ta fashe da wani irin kuka me cin rai lallai namiji kanin Ajali kamar ba yanzu ya gama sukuwa a kanta ba ya kwashi romonta amma dubi yanda yake gasa mata magana me zafi.! A fusace!! Ta futa daga parlor . Tsaki yaja me k'arfi hade da zama cikin kujera yana fad'in "Sai kace ni ns kirata 'yar iska zata zo ta dame ni da kukan banza." Zama yayi yana shawarwari da zuciyarsa me. Zaiyi ya kuntatawa zuciyar Asma'u kan abunda tayi masa lallai ta dauki bashi domin bazai tab'a yafe mata ba halin da ta sanya zuciyarsa a ciki zai nuna mata shi namijin duniya ne jarumi zai danne sonta cikin zuciyarsa kamar bai tab'a yi ba, sai tagane kuranta zata gane wautar da ta tafka a rayuwar ta. Bayan Sallah Jama'a aka d'aura auran Asma'u da Mimi a babban masacin juma'a Mai Martaba sarki ne ya karb'i wakilcin Amjadu duk da cewar akwai wakilan sa, d'aurin auran ya samu halatar manya manya mutane sosai abunka da na Jama'a garin labarin d'aurin auran Amjadu ya baza garin kano da ma kewayen ta, 'yan jarida sun samu abinyi,da kyar ya samu ya futo daga cikin jama'a ya shiga mota ba tare da b'ata lokaci ba ya umarci doh, ya wuce dashi gidan granny saboda yasan in gidansa ya wuce wata Matsalar ce Jama'a gami da 'yan jarida baza su kyaleshi ba. *15/November/2019* [11/16, 10:02 AM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO* *MALLAKAR_ BINTA UMAR* *LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA SAI TA CI SHI* *53* To gidan granny ma cike yake da 'yan uwa da abokanan arzikinta sun zo taya ta farin ciki mutanan Chadi ma suna kan hanyar zuwa, aikuwa suka yi masa caaa! A ka masu tsokanar sa nayi masu fad'a masa magana nayi a fakaice Inna Suwaiba take yar masa da magana yak'i d'iyar ta Hafsa gashinan ya kwasowa kansa kara da kiyashi, wad'anda suka San akwai maganar sune suka fahimci inda ta dosa basu dad'in abunda tace ba ko babu komai ai matar mutum kabarin sa ce, Granny ma bata ji dadin abunda Inna Suwaiba take yi ba, tunda tazo gidan take yar da haibaci sai kace k'aramar yarinya. Shi dai shigewar sa yayi bedroom din granny don har ga Allah baya cikin nutsuwar sa ballanta ma ya fahimci Abunda Innarshi take nufi ****** Wallahi duk makiyin mu idan ya kallemu sai mun burge shi, munyi kyau ni da Mimi har mun gaji duk inda muka wuce cikin jama'a sai kaji suna fad'in "Wai wacece amaryar ne tsakanin su biyu sai da a nuna Mimi kawai amma lokaci guda baza ka ban bance mu ba, sai hotona muke da k'awayenmu, ko wacce da k'atuwar wayar ta, nima hannu na rike da wayarshi da ya bawa Mimi mai muguwar camera mai fidda mutum nasa Munnu ta dinga d'aukar mu hoto ni da Mimi, wacce take cikin tsananin farin ciki da annushuwa. Umma ita da jama'ar ta sai hidima suke yi aunt Hauwa kuwa ai ba'a ganinta, tun da safe da suka gama rigima da Mimi kan wani magani tazo dashi cikin jarka wai lallai Mimi sai ta shanye shi, Mimi taki shine take tayi mata masifa, nice na lallab'ata ina fada mata amfanin maganin a jikinta sannan ta dauka tasha, magani iri-iri aunt Take dirkawa Mimi wai lallai sai tayi ni'ima ni kuwa dariya kawai nake musu mussaman in naga Mimi na kuka tana shan magani. Yanzu ma gidan kawarta ta tafi wai zata karbo wani turare duk dai Mimi ake so tayi amfani dashi kafin a kaita dakin mijinta. Dakinmu cike da 'yan uwanmu da k'awayenmu sai surutu kake ji ana shewa zan can aure kawai mukeyi ina gefe ina sanja kayana wayar Mimi tayi kara, dama tana kusa dani ina dubawa naga heartbeat nace" Mimi zo ki d'auka. " da sauri tazo ta karb'i wayar daga hannuna, ihu! 'Yan dakin suka sa, suna fadin"Da Alama ango ne ko."? Gyada kaina nayi nace." Shine ya kira yaji lafiyar amaryar shi" suka fashe da dariya hade da tafawa suna Fadin "hohh-hohh Yau Mimi zata ji maza."! Ita dai futa Tayi daga dakin tana murmushi. Yana kwance kan bed din granny ya cire babbar rigar jikinshi daga shi sai singlet da dogon wandon arniyar shadda da yayi futar d'aurin auren sa, da ita, juyi kawai yake yi zuciyarsa babu dad'i, ji yayi kawai yana sha'awar jin muryar Asma'u yasan hakan ba dai-dai bane, to ya rasa ya zaiyi da zuciyar sa, wacce take nema tafi karfinsa a kan Asma'u, wayar sa ya dauka ya kira numbar Mimi yana fatan Asma'u ta dauka kamar ko da yaushe, sai dai sab'anin haka Muryar Mimi yaji tana yi masa sallama, lumshe idonsa yayi hade da d'an cije lips d'insa na kasa, yace." momyna ya hidima."? Mimi ta damkewar wayar sosai wani irin dad'i na ziyartar zuciyar ta, a hankali tace." Alhamdullahi." "Ok babu wata matsala ko." "Eh babu mungode sosai da Hidima" murmushi yayi kawai yana jin tausayin yarinyar yasan so masifa ne, abunda yake ji a halin yanzu yasan shi take ji a zuciyar ta dole ya girmama mai sonshi yace." Haka nake so, Idan anjima Ku shirya akwai Walima da abokina masu mak'otaka dani suka shirya min,zan aiko a dauke Ku a mota OK." Mimi tace." Insha Allahu. Kokarin kashe wayar yake tace" ko in bawa Asma'u wayar ne." ? Girgiza kansa yayi kamar tana kallonsa yace." K'yaleta kawai Momyna zamu gaisa idan anjima OK." Kafin Mimi tace Wani Abu ya kashe wayar yana jin wani mugun daci a bakinsa, ko wane ango yana farin ciki ranar d'aurin auransa mussaman idan ya tuna amaryar sa, amma shi ranar d'aurin sa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78