Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 19

Chapter 19

Babban Yaro Book 2 Complete Hausa Novel 1,217 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kallonsa ba daga k'arshe ma tashi nayi na bar gurin naje na tsiri ninkin kaya ina tunin yanda Allah ya dauka kashi a duniya 'yan da yake da kyauta da son talaka da yanda yake da farin jinin jama'a, yanda yake da ibada, amma yana aikata sabon Allah domin zina mugun aikine Wanda Allah ya hana shi, kawai sai na tsinci kaina da yi masa addu'ar shiriya naji wani irin tausayin shi, babu uwa babu uba ga makiya da d'umbun masoya gaba da baya, Allah ne kadai yasan abunda zai zama nan gaba, a fili nace"Ubangiji Allah ya kare ka daga sharrin ma su sharri Allah ya shirye ka shirin addinin musulunci yasa ka daina aikata zina." ****** Yau sati guda kenan da faruwar al'amarin Wanda yayi dai-dai da kwanaki goma da afkuwar al'amarin Auran mu komai ya dai-dai ta, tun ranar da ya kira wayar Mimi na kashe ban kara kunnawa ba sai yau, sun kawo wuta na jona ta a chaji. Mimi ta shigo dakin jikinta babu k'wari ta zube kan katifa. Binta nayi da kallo. Nace"Mimi kinga yanda kika rame kuwa."? Shuru tayi min Nace"Wallahi Ki yiwa kanki fada ni yanzu kin daina bani tausayi haushi kike bani wallahi, wai Amjadu shi kadai ne namiji a duniyar nan." Shiru dai tayi min bata ce min komai ba. Tsaki naja na futa daga dakin. *** Tun lokacin da ya kira wayar yaji an kashe bai Kara kira ba yasan Mimi baza ta kashe masa waya ba. Tabbas Asma'u ce shiyasa bai kara kira ba. Yana zaune gefan bed da wayar a hannunsa numbar ya kira sai yaji ta shiga har ta katse ba a dauka ba, kira ya kara yi a karo na biyu nan ma ta katse ba a dauka ba, a je wayar yayi hade da Jan tsaki a fili yace." Mata masu aji kenan." Mik'ewa yayi ya futa parlor. Mimi na kwance a dakin lokacin da yake kiran wayar tarin da take ne ya hanata d'aukar wayar har ta katse. Cikin wani irin mugun tari da galabaita ta mike zaune hade da dafe k'irjinta tana cigaba da tarin sosai wa [11/8, 6:21 PM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO* *Mallakar_BINTA UMAR* *LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD'IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA.* *45* Ni da Umma muka shigo dakin da sauri! Mimi na durkushe ta rike k'irjinta tana ta tari. Da sauri Umma taje ta rike ta ni kuma ns dauko ruwa hade da fasawa na dago kanta ina bata, k'arfin tarin ya hanata ta karb'i ruwan. Umma tace"Maza kije ki dauko gishiri a kicin. Cikin tashin hankali na nufi kicin din na dauko ledar gishiri Umma ta dangwala a hannuta ta sanyawa Mimi a baki tana Dan bubbuga bayanta hade da yi mata sannu. Mimi idonta ya rufe sosai take tari! Da haki tare da hawaye. Ni da Umma duk mun shiga tashin hankali. Nace"Wallahi Umma jiya da daddare haka ta dinga yi da kyar tayi bacci." Umma tace"Ikon Allah watak'ila busawar sanyin nan ne,. Nace"Ina jin hakane " cikin ikon Allah tarin ya lafa sai dai haki da take yi. Umma ta rungume ta a jikinta tana yi mata sannu Ya Aminu ne ya shigo dakin ya tsaya bakin kofa fuskarsa s daure yake tambayar menene? Umma tace"Mimi ce babu Lafiya in anjima ka siyo mata maganin tare saboda dare." Wani irin kallo yake wa Mimi daga bisani kuma ya tab'e bakinsa Yace. " Umma ki rabu dasu duk karya ne,nasan wannan'yar iskar ce take zugata." Umma ta bata fuska tare da fadin"bana son wannan halin naka Aminu ina ruwan Asma'u anan.? Futa yayi daga dakin ransa a bace. Nace"Umma shifa bazai taba ganewa ba tunda ya samu ya kubuta Mimi CE abun tausayi.' Shiru Umma tayi min, sai da taga Mimi tayi bacci sannan ta gyara mata kwanciya ta futa daga dakin jikinta duk babu k'wari. Kallon Mimi nake gwanin tausayi duk ta rame tayi Dan wuya k'irjinta sai sama yake yana kasa alamun tana jin jiki. Jikina babu k'wari na kwanta kusa da ita ina tunani Ringing din wayar naji wacce take jone a chaji na mike da sauri hade da dauka Babu sauk'i a murya ta nayi sallama Ajiyar zuciyarsa naji a hankali yace." Ya kike mata masu aji."!! Sama nayi da murya ta nace." Ina nan kallo kamar tsumma a randa, amma kasan da cewar zuciyar da ka yaudara da sunan so kake azabtar da ita tana cikin gararin rayuwa tana cikin halin ha'ulai kullum bata da sukun hawayen idonta ya kasa daina zuba....... Katse ni yayi kafin in karasa magana ta yace." Wannan wace irin banzar magana kike min kina yi kina daga murya kamar kina yi da sa'an ki, kiyi min magana yanda zan fahimci me kike nufi ." Haushi maganar shi ta bani saboda haka nace "Da Hausa nake maka magana ba da harshe nasara ba, nace" D'aya zuciyar daka yaudara tana cikin halin ha'ulai da damuwa saboda haka in ta shiga mugun hali to kai ne sila." Lokaci guda ya fahimci inda maganar ta ta dosa. Babu ya bo babu fallasa yace." Bani Momyna mu gaisa. " A hasale nace"Ya ina yi maka magana daban kana yi min wata maganar, Mimi dai na bacci Wanda muka samu ya dauke ta da kyar don haka bazan tashe ta." Na k'arashe maganar tawa a kufule! Wannan karon akwai sassauci a muryarsa yace." Nace kiyi min bayani dallah-dallah yanda zan fahimta ni har yanzu ban gane abunda kike nufi ba." Nace"Mimi na kwance babu lafiya tana jin jiki saboda sonka shine Abunda nake nufi. Ina jinsa yayi murmushi cikin nutsuwa yace." To waye mai laifi tsakanin ni da ita da iyayen Ku."? Da sauri nace "Kar ka sake ka zage mu ko kafad'i bak'ar magana kan iyayen mu." 'Yar dariya naji Yayi yace." 'Yan matana kenan, dags magana zan zage iyayen Ku cewa nayi waye mai laifi sai ki bani amsa ta." A fusace! Nace "Kai kasani." Yace."OK naji bani Momyna muyi magana. " "Kasan Allah bazan tashe ta ba wai me ma zaka fada mata ne bayan ka yaudare ta." 'Yar dariya yayi tare da fadin"Ina ruwan ki? Ke dai nace ki bani ita." Shiru yayi sai kuma ya cigaba da cewa"Kina maganar na yaudare ta, nifa ita nace s kawo wa kud'in aure akayi mistake aka kawo miki, bayan nan Kuma maganar Aminu ta futo, ai ni ne ma zan ce an yaudare ni an bani wacce bana ra'ayi." Tsaki! Naja na kashe wayar ganin yana nema ya Mai da mutane mahaukata. Ganin magariba ta kusa ne yasa na tashi Mimi domin baccin magariba babu kyau. Lokacin Ya Aminu har ya kawo magunguna dasu Lemo da ayaba sai kai wa yake yana kawo wa, in muka hada ido ya buga min harara. Muna idar da sallah na sanya Mimi a gaba taci abunci sannan na bata magunguna sai ta kwanta. Nida Umma muna addu'ar Allah yasa kar tarin ya kara sark'e ta. K'arfe Tara dai-dai naji ringing waya tsaki nayi Dan nasan wanene. Dauka nayi hade da sallama ba tare da ya amsa min ba yace." Ki futo yanzu ina jiran

Table of Contents

Chapters

78 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});