Chapter 78
Chapter 78
Wanda ya gaura ye parlor gaba daya wato k'amshin Asma'u kenan. Jahid yazo ya wuce ni ba tare da yace min komai bsla ya futa, kallo na bishi dashi cike da mamaki! Lokaci guda fad'uwar gabana ya tsananta jiki babu k'wari na k'araso gurin su, granny ta mike Da sauri hade da rike hannuna muka nufi wani bedroom Kallo ya bisu dashi har sai ds suka shige, sannan ya mike zaune hade da dafe kansa yana tunanin irin zaman da zasuyi da Asma'u a cikin gidansa. Gefan gado ta zanar dani ta zauna muna fuskantar juna da ita, a nutsu tace"Aminci Allah ya tabbata agare ki yarinyar kirki." Hannunta ns rike sosai Nace "Tare dake granny, jikina na bani akwai wani Abu ni kam na kasa fahimtar inda maganar Ku ta dosa ke da Jahid." Granny ts girgiza kanta take naga k'walla ns zubo mata. Tafin hannuna na sanya na goge mata INA kallonta cikin mamaki nace"Granny don girman Allahu ki Sanar dani meke faruwa."? Kai tsaye tace",Sanar dake abunda yake faruwa ya zama dole domin an shiga Hakkin ki, mun so kanmu da yawa, to amma ni ina ganin gata akai miki Wanda ko bayan babu raina zaki gode min da wannan alkairin da nayi miki, ina so kiyiwa magana ta kyakyawan fahimta." Nace"Insha Allahu." Granny ta gyara zaman ta sosai ta kwashe dukaninin abunda yake faruwa tsakanin Jahid da mahaifiyar sa da yanda Granny taje har gida domin ta nusasshe da ita ta ci mata mutumci da yanda suka yanke hukunci ita da Jahid din kan auran ta ya koma kan Amjadu domin ta kula da baby Aysha........... Tun kafin granny ta karasa maganar ta hawaye suka wanke fuskata ina mamakin wannan yankan kaunar da suka yi min yanzu Abunda Jahid zai min Kenan? Yaudara kiri-kiri Innalillahi, Jahid ya munafurce ni, yayi min abunda ban taba tsammani ba, ni tunda Amjadu ya auri Mimi a rayuwata ban tab'a kawowaa zai zama mijina bs shine babu Neman shawara babu komai suka yanke min Wannan hukunci kamar wata 'yar tsana. Idan Momyna ta hana shi auranena CE masa akayi Neman kai nake yi da kaina kawai zai sanya a d'aura min aure da Amjadu Wanda a halin yanzu muke buga tsaka dashi saboda rashin jituwa ta yaya zaman aure dashi zai yiwu..... Hawaye kawai nake zubarwa ina kallon granny nama kasa cewa komai. Take itama naga ta fara share hawaye tace"Hak'ika ba'a kyauta Miki ba Asma'u amma kiyi hak'ura Insha Allah zakiyi alfahiri da Wannan auren." Ina Kuka Nace " Granny Yanzu meye ma'anar kawo ni gidanan bayan an San Abunda akayi min. Cikin sigar rarrashin granny tace" Dole s kawo ki gidan auran ki ko ba yanzu ba, kwai da mun yanke wannan sha'awar ne da Yayarki Hauwa dashi kanshi Mujahid din domin yin hakan shine zai kawo kwanciyar hankali da zaman lafiya ba tare da jama'a sun fahimci abunda yake faruwa ba, kinga wani zai iya fada miki haka cikin gidan Ku babu shakka Zaki shiga fargaba da tashin hankali a lokacin Wanda hakan zai jawo hankalin mahaifiyar ki ya tashi har jama'a su fuskan ci akwai matsala saboda haka da yardar Allah kin shigo gidan auran ki zaki zauna a karkashin mijin ki kamar yanda ko wace mace take yin biyyayar aure." Kuka na fashe dashi sosai nace"Granny idan akai min haka ba'akyauta min ba, shikensn sai kace wata 'yar tsana ni akwai abunda zanyi a gidanmu yanzu " granny tayi murmushi Wanda iya kadai ce tasan ma'anar sa tace." Duk abunda zakiyi a gidanku ba kamar nan gidan ba, domin nan shine gidan ki halak malak sai kin fi sakewa kiyi yanda kike so saboda haka ki kwantar da hankali ki insha Allahu kome kike manta a can nasan zasu kawo miki shi har gidan ki." Kwata-kwata bana son yin jayyaya da tsohuwar yasa nayi mata shiru kawai ita kuma ta mike da sauri tana fadin "Bari inzo yanzu." Tana futa na kwanta ka bed din hade da fashewa da Kuka mai tsananin gaske, Wannan wace irin kaddara ce ni Asma'u. " Baby Aysha dake wasa can karshen gado ta rarrafo ta yaye jikina tana kallon yanda hawaye suke tsere a kumatuna. Cike da tausayi ns rungume yarinyar a jikina Mimi ns tuno lokacin naji kamar in bita in huta da wannan rud'un na duniya. Kuka sosai nake yi mai futar da sauti.!Cikin wannan hali suka shigo suka same ta. Amjad daga bakin kofa ya tsaya ya soka hannunwan sa cikin aljuhu fuskarsa babu walwala ko ta kwabo kallon su kawai yake yi yayin da yake jin kukan ta yana masa wani irin zafi a zuciya. Mamaki yake sosai ko kukan me take yi idan hakane shima sai ya Dora hannu aka yayi ta kuka ko ya samu sassauci Cikin zuciyarsa tunda dai bata fishi jin ciwon abunda ya faru ba, don dai Jahid ya wuce komsiba gurin shi shiyasa kawai yayi masa shiru domin har yanzu shi da si magana ta fatar baki bata had'asu ba sai dai ido kawai. Granny ta karasa gadon ta dauke Baby daga jikinta tana kokarin mikar da ita zaune, tace"Kiyi hakuri Asma'u ki tashi zaune ga Mijin ki ya shigo ina so in hada Ku guri guda in muku fad'a kukan bashi da amfani kuma INA me tabbatar miki da cewar kukan nan da kike yi zai zama alkairi a rayuwar ki." Jin Granny tace ga mijinta ya shigo ya sanya fad'uwar gabanta ya tsananta tana tsoron ta kalleshi wai a matsayin miji domin ta lura da kallon banzan da yayi mata tun farkon shigowar ta gidan.... Shi kam Amjadu a zabbaban kamshi turaran Asma'u da ya d'umame dakin shine ya same shi yana nema ya sanya shi cikin wani yanayi..... *2/12/2019*
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78