Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 35

Chapter 35

Babban Yaro Book 2 Complete Hausa Novel 1,212 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ki zab'a min miji Wanda kike so Amjadu na bar wa Mimi ." Umma tace." Asma'u kina jin abunda Kawun Ku yake fada ko akan ki kina jin irin cin mutumcin da yake min ko.? Nace" Umma duk naji kiyi hakuri ki kyalesu dama ba yau suka saba miki cin mutum ci. Ni nasan yanda zanyi insha Allahu Mimi bata da miji sai Amjadu ki kwantar da hankalin ki." Hannun d'iyar tata ta rike tare da fad'in"Ubangiji Allah yayi miki albarka Asma'u Yanda kike min biyyaya Allah ya baki 'yaya masu biyayya kema, yanda kike ceci rai ubangiji Allah yasa Annabi ya cece ki kema." Wasu zafafan hawaye na hau sharewa lokaci guda tausayin kaina ya kama ni, wani irin hali na shiga a lokacin ta inda naji gwara min mutuwa da rayuwa Allah-Allah nake naga Mimi a gidan Amjadu ko ma samu hankalin mu ya kwanta, Alluma ajirin fi musibati wa aklifni kairan minha itace addu'ar Dana ke ta maimatawa a zuciyata tare da Innalillahi wa inna ilahi raji'un, lokaci guda naji zuciyata tayi sanyi na kalli Umma tare da fadin"Don Allah Umma kar a kara tayar da maganar nan domin I Dan Mimi taji to wani tashin hankalin ne, Umma kija kunnen Ya Aminu a kan hakan." Umma tace"Nima abun ya soma damuna Asma'u Insha Allah zan ja kunnen sa, ke dai Allah yayi miki albarka insha Allahu yanda kika sanya ni farin ciki kema 'yayan ki zasu sanya ki." Bacci ne ya soma fizgar sa kad'an-kad'an yaji ringing din wayar sa, cikin kunnen sa, dalili airpic din dake manne a kunnen sa, a hankali ya dauki wayar dake saman k'irjinsa yana dubawa. Mik'ewa yayi da sauri ganin numbar da ta kirashi. Ba tare da ya cire airpix din ba ya latsa wayar tare da fadin"Salamu alaikum." Murya Asma'u yaji sama-sama ta amsa da wa'alaikasalm. " gabansa ya fad'i sosai lumshe idonsa yayi hade da cije leb'anshi fargabar abunda zaiji daga bakin ta yake." Kai tsaye yaji tace"Barka da yamma." A hankali yace." Barka ya kike Husnah."!! "Lafiya.'! Tafad'a babu wani sassauci ta cigaba da cewa " Yanzu Kawu Yunusa ya bar gidanmu bayan ya Sanar damu sak'on ka." "Owk" shine abunda Yace yaja bakinsa yayi shiru yana sauraran ta. Ta cigaba da cewa" Allah ya kadddara ni ba matar ka bace, ina yi maka fatan alkairi idan son da kake min na gaskiya ne, to a madadina da aka zab'a akan Mimi ni na hak'ura ka mai da maganar auranmu kan 'yar Uwata domin ceto rayuwar ta.". Wani irin gumi ne yake tsayaya daga jikinsa bakinsa yayi wani irin daci ya soma Jin zazzab'i na shigar shi, jin abunda take cewa, amma da yake NAMIJIN duniya ne, muryarsa a tsaye yace." Meye hujjar ki ta fad'ar haka, shin nine bakya so ko kuma akwai wata manufa taki."? Cike da dakiyar zuciya tace." Eh duk biyun ne bawai bana sonka ba ne, Mimi tafi ni sonka bayan haka kuma kayi mata alk'awarin aure ka yaudare ta da kalaman ka hade da zakin bakin ka, kayi kwance kwance ka lasa mata Zuma a baki daga baya kuma kace ka fasa auran ta, shin baka tunanin halin da zata shifa ko kuma kana so mu rasa ta, son da Mimi take maka zai iya kashe ta."! Wani irin yammm!! Yake ji a jikinsa tsigar jikinsa tana Mik'ewa jin abunda yarinyar take fada, a kausashe yace." Shine Hujjar ki."! ? "Eh shine Hujja ta." Ta fada babu wasa a cikin maganar ta." Ajiyar zuciya ya sauke minti uku tsakani yace."Shikkenan tunda haka kika Zab'a mana ni dake muyi rayuwa na karb'i Mimi a matsayin mata kamar yanda kika bukata, Allah ya sa haka shi yafi alkairi.". Da sauri nace"Ameen auran Mimi alkairi ne a gare ka insha Allahu." Kashe wayarsa yayi ba tare da yace min komai ba. Lokacin naji damuwar da ke cikin raina ta ragu burina kawai inga Mimi gidan Amjadu mu huta da wannan masifar, duk abunda ya faru tsakanina dashi na Sanar da Umma ita ma taji dadin yanda ya amunce lokaci guda. Hannusa ya sanya ya dafe kansa dashi lokaci guda kansa ya shiga Sara masa wani irin bakin ciki da damuwa sun taro sun tsaya masa a mak'ogwaro da kyar yake had'iyar yau!! Sosai yake jin bakin ciki da takaicin zafafen maganganun da yarinyar ta watsa masa lallai inda ranka kasha kallo wai shine yau 'ya mace take furta cewa bata son sa baki da baki yarinyar ma k'arama irin Asma'u. *14/November/2019* [11/15, 10:20 AM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO* *MALLAKAR_ BINTA UMAR* *LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA SAI TA CI SHI* *52* Yana zaune a gurin hannunsa saman goshin sa granny da Iyami me aikinta suka shigo parlor Iyami ta nufi daining tana gyara gurin, ita kuma Granny ta k'araso kusa dashi da sauri ganin yanda yake cije bakinsa yasa ta dafa kafadar sa, tare da fadin"Kar ka sake ka sanya damuwa cikin zuciyar ka har ta haifar maka da wani ciwon ni dai a ra'ayi na nafi so ka auri 'yar bak'ar yarinyar a cikin su biyun naga kamar tana da kunya da hankali." Ta k'arashe maganar ta a tausashe. Da kyar ya iya bude bakinsa yace." Tace bata sona Granny. " Zama tayi kusa dashi cike da mamaki tace" Amma Wannan anyi 'yar banza ta samu namiji me zafi da kwarjini kamar tace bata so, in banda ma Matsalar ka nasan ko mata dozin aka aje maka zaka iya dasu, amma wannan yarinyar ta bani haushi wallahi. " Kwanciya ya gyara hade da lumshe idonsa shi kadai yasan abunda yake damun zuciyar sa. Granny kuwa mita take tayi tace"Tun farko sai da nace maka kaje ka nemi auran Hafsatu ka kiji kaga ni ai abunda nake guje maka." A hankali yace." Granny magana ta wuce a halin yanzu insha Allah jibi za'a d'aura min aure da Ma ko wacece na yadda haka Allah ya shirya min." Tace"Tunda dai kayi niyyar auran mata biyu mai zai hana ka hada da Hafsatu nasan in kayi magana baza su ki ba." Jajayen idonsa ya bude ya sauke su a kanta, fuskar shi a murtuke yace." Ki k'yaleni da wani zance Inji da guda d'ayan ma ni da ba cikkakiyar Lafiya ba." Hararasa tayi tace"Au! Ashe munafurci ne yasa kace zaka hada mata biyu hummm! Kai dai ka sani ma kanka." Shiru yayi cikin zuciyar sa Yace ." Granny in batayi wasa ba zai sauke fushinsa akan ta yanzu juya mata baya yayi ta gaji da mitar ta tashi daga gurin. Wayoyinsa duk kashe su Yayi domin baya bukatar damu a halin da yake ciki ji yake zuciyarsa tana iya bugawa ta tarwatse. Sai daf da magari ba ya tashi daga kwanciyar da Yayi kai tsaye masjid ya nufa yayi sallolinshi tare da addu'ar Neman zabin Allah ya futo daga massalaci Jama'a na ta mik'o masa gaisuwa Amjadu bashi da wulakanci sosai ya tsaya ya gaisa da mutane, cikin ikon Allah yana shiga gidan yaji zuciyar sa tayi

Table of Contents

Chapters

78 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});