Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 66

Chapter 66

Babban Yaro Book 2 Complete Hausa Novel 1,211 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

sauri na mik'a mishi wayar nace "Bari in dauko wayar tawa ka tura min wsp din don Baby Aysha amma da na daina yi." Dariya yake min har na futa daga motar. A tsakaice dai sai da Jahid ya bude min wsp dina da na rufe tun bayan rasuwar Mimi ya tura min dukanin. Hotonan baby Aysha, yace" kullum zai dinga d'aukar ta sabbin pictures Yana turo min sosai naji dadin haka na saki jikina sosai muka yi shirarmu nan yace insha Allahu a karshen wata yake so ya turo magabatan sa gurin Kawu Yunusa nace"Allah yasa nan mukayi sallama dashi ya tafi. Ko da Umma taga hoton baby Aysha tayi ta mamaki sosai sai taji sha'awar ganin yarinyar a zahiri tace." To tunda ya hamu ita ni zanje da kaina in duba ta ai hakan ba laifi bane." Umma da kin kyaleshi dai komai abunda baby Dole ta nemi dangin uwarta wallahi." Umma tace"Ai baza'ayi haka ba, domin bamu San munufar sa tayin haka ba, to koma dai menene abar shi da d'iyar shi yayi yanda yake so da ita." Shiru nayi ina raya wani Abu a raina Abunci naci nayi wa Umma sallama, kai tsaye dakinmu na nufa, na tube kayan jikina wata duguwar Riga na sanya a jikina mai uban kyau da tsada duk cikin kayan Mimi suke, hula na sanya a kaina na kwanta kan katifa, hade da rufe k'afafuna hotan baby na tsurawa ido ina murmushi nima wallahi na damu inga yarinyar a zuciya ta. Wsp na shiga na d'ora pic dinta kan df na, wsp din dake amfani a waya ta mai Gb ne ya nuna min Amjad na online wata zuciyar tace kiyi masa magana kawai tunda gashi a onile da sauri na shiga gurin shi naga ya sauka akai. Yanzu Df shi na kamo da sauri ina dubawa, pic dinshi ne da baby Aysha ya d'aga ta sama yana dariya hat tada dimple dinshi sai da ya futo saboda dariya itama babyn dariya take naji sun bani sha'awa, zuciya ta tace min "Shi yana Cikin jin dad'i har da dariya gashi ga 'yar shi hummm! Ai in da mutumci Amjad bamu cancanci haka daga gurin shi ba, message na tura masa kamar haka _" Duk d'an halak baya bance alkairi kuma tilas! Ace da mijin iya baba, duk talaucin mu, baby na tabbata sai ta neme mu, domin mune dai dangin uwarta."_ Tura masa nayi na kashe data ta, tsawon mintuna ashirin, na k'ara bud'e datar, ina dubawa naga har ya gani, sai naji wata fad'uwar gaba, messenges na cigaba da dubawa ina sauraron amsar sa, shiru kusan minti talatin kuma duk dubawar da zanyi sai inga yana online, bakin ciki da takaici suka ishe ni, abunda na tsana a rayuwa ta shariya guy nan yaga sakona zai wulakanta ni, lallai ya sanja sabbin halaye, ji nayi wasu zafafan hawaye na nema su kufce min. Kira ne ya shigo wayar tawa ina dubawa naga shine..... *26/11/2019* [11/27, 4:45 PM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO* *MALLAKAR_ BINTA UMAR* *LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA SAI TA CI SHI* *65* Cikin fad'uwar gaba na mik'e zaune sosai ina k'ara duba wayar tabbas shine ya kira ni. Cikin zuciyata nace to me zai ce min lallai ma, kin d'agawa nayi har ra katse wani kiran ya k'ara shigowa ina kallon wayar nan ma ta katse band'aga ba, sai da ya kira sau uku nak'i dagawa sannan ya hak'ura, kwanciya nayi ina sak'e-sak'e a zuciya ta, data ta kara kunnawa aikuwa sak'on shi na farko hannuna na rawa na shiga ina dubawa. Ga Abunda yace. _"Maganar ki gaskiya ne 'yan mata, Sweetheart bata da wani dangi sai ku domin kune iyayen ta, Abunda na kasa fahimta a maganar da kika ce duk D'an halal ba ya mance alkairi, shin wane alkairi kuka yi min da har na manta? Bayan nan kuma ina so in k'ara jaddada miki cewar Aysha d'iya tace domin nine k'ashin bayan Samar da ita, dukanin Ku baku da iko akanta, ni nake da iko akan kaya ta, so bana son damuwa don Allah daga yau sai yau karki kara yi min magana makamamciyar wannan, ina fatan kin fahimta? Kin turo min Jahid kan bukatar ki, to baki isa ba indai nine uban Aysha bazan tab'a Bari ki raine ta ba ballanta ki koya mata munanan d'abi'un ki, tabbas yanzu na tabbatar da cewa a baya nayi wauta da nake kokarin rabuwa da mace tagari a kanki , na tabbata Mimi alkairi ce a rayuwa ta, kuma duk macan da zan aura sai dai tabi bayanta wallahi,a halin da ake ciki yanzu soyayyar ta ta cika min zuciyata duk da bata Raye, ta inda nake yi wa mata kallon maza ciki kuwa har dake, saboda haka ki kiyaye fad'a min magana ko wace iri ce,ni Amjadu AbulAbbas ma nasara na shafe ki a babin rayuwa ta."_ ~AMJD ABUL ABBAS~ Wani irin gumi ne yake tsiyaya a jikina take wasu zafaffan hawaye suka kece min, Dana San wad'annan mugayen maganganun guy nan zai fad'a mun da ban mishi magana ba, hannuna na karkarwa nake bashi amsa..... Da sauri na tura masa, na kashe data hade da jefar da wayar kan Katifa na rungume filo ina tik'ar kuka harda sharb'e majina,wato ni guy nan yake nunawa iyaka ta kan abunda Mimi ta tafi ta bari gashi Ubangji ya zuba min kauna da son baby Aysha a cikin raina, nafi awa guda ina kuka k'asa kasa don kar Umma taji fa kyar na rarrashi kaina tare da alk'awarin cewar bazan kara shiga harkar shi ba har a bada..Data na k'ara kunnuwa ina tunanin zanga sak'on shi domin nasan na fad'a masa bak'aken maganganu Wanda suka fi nashi abun mamaki, ko da na duba sai naga yayi bloking d'ina, sak'on Dana tura masa Yanan yanda yake, ajiye wayar nayi ina da na sanin bud'e whatsp din inda nasan wannan bakin cikin zan riske, da kyar bacci ya dauke ni mai cike da mafarkin baby Aysha da Mahaifiyar ta. Ko dana tashi da safe sukuku na tashi jikina duk babu kuzari har Umma ta fahimci wan Abu amma bata ce min komai ba, saboda tana tunanin a jizanci ne irin na d'an Adam, sallama nayi mata na tafi makaranta. To ko A skull din ma kasa b'oyewa Munnu nayi sai da na fad'a mata komai kuma na nuna mata text din da ya turo min, Munnu ta dinga mamaki tsabar haushi da takaici yasa ta dinga zaginsa hotonan baby take dubawa sosai tana fad'in"Wallahi karya yake in Ku ya rabaku da ita mu bai isaba sai munje mu daukota Wallahi munganta ai wannan rashin imani ne ace kamar jinin Mimi sai dai mu ganta a hoto gaskiya bai isa ba."!! Yanda Munnu take masifa sai ya bani dariya nace"Munnu ni da zaki bi ta tawa da mun hak'ura wallahi duk son ki da baby baki kaini ba, amma na hak'ura na bar masa kayan sa kamar yanda ya fad'a d'in, nasan

Table of Contents

Chapters

78 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});