Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 54

Chapter 54

Babban Yaro Book 2 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

. Nace"Wallahi haka yace domin hakan shine mafuta. Take naga hawaye yana kokarin zubawa a idonta, muryar ta na rawa tace"Banji dadin wannan labarin ba Asma'u, nifa idan naji ance za'a yiwa mace me ciki aiki sai naga kamar mutuwa zata yi Nace"Umma ki daina wannan tunanin insha Allahu Mimi zata sauka Lafiya ." Shiru tay min tana goge hawaye. A fakaice. Zuciya ta naji ta karya nima na meke da sauri jin hawaye yana kokarin zubo min mutukar nayi kuka a gaban Umma to itama kukan zata yi. Dakinmu na shiga na tube kayan jikina yunwa nake ji sosai domin ban samu damar cin abunci da granny ta girka ba saboda fargaba. Da d'aurin k'irji na futo nace"Umma Allah yasa da akwai ruwan zaki a Fula's Wanka zanyi." Ba tare da ta kalle ni ba tace"Da akwai cikin babban Fula's din nan." Kicin na nufa da sauri na hada ruwan zafi a bokiti dauka nayi na shiga band'aki. ******* Tsanin azabar da Mimi ta sha a wannan daran ya d'agawa Amjadu hankali domin kuwa a zaune suka kwana Mimi rungume a jikinsa, kamar ranta zai futa rik'on shi kawai take ya YAFE mata. Saboda tausayin ta bai San sanda ya fara zurarar da hawaye ba, rungume ta yayi tsam!! A jikinsa yana tofa mata addu'oi. Sai daf da asubahi bacci ya dauke ta, shi kuwa dungurgur ya kwana a zaune yana kallonta sai da yaji kiran sallahr sannan ya mike toilet ya shiga yayi Wanka ya futo tsaf shirin massalaci yayi yazo ya tsaya kanta, bacci yaga tanayi sosai, cike da tausayi yake kallon fuskarta inda idonuwan ta suka zurma cuki [11/22, 8:02 AM] BintuUmarAbbale: Ko da ya dawo daga massalaci Mimi bata tashi ba, bai tashe taba sai ya zauna kusa da ita hade da rik'o hannunta ya rike tam! Ya k'urawa fuskar ta ido, Cikin zuciyar sa ya jinjinawa mata da irin wahalar da suke sha yayi d'aukar ciki da haihuwa. Ya minti talatin a zaune a gurun yana sakawa da kwancewa, kana ya mike ya dauko wayar sa yana kunnawa sakkoni suka dinga shigo wa Sam bai bi takan su ba, numbar Mujahid ya kira. Mujahid yace." Gashinan zuwa gidan. Kashe wayar sa yayi ya futo parlor lokacin granny ta futo tana kicin tana hada musu kalaci zama yayi a cikin kujera cike da damuwa. Jahid yana shigowa ya ganshi a hargitse zama yayi kusa dashi ya bashi hannu suka gaisa, yace."yana ga duk ka wani furgice ne."? Ajiyar zuciya Amjad ya sauke yace." Jahid yanzu haka Momy take shan wahala jiya kwanan zaune muka yi na tausaya mata wallahi." Jahid yace." Dole kam abun tausayi CE, dama abunda ya kama ta ayi mata kenan." Ajiyar zuciya ya sauke a karo na biyu yace." Da har na fara tunanin futa da ita waje a duba ta." Murmushi Jahid yayi yace." Kar ka damu Aboki duk abunda kake tsammanin za'ayi mata k'asar waje insha Allahu zamu yi mata zan tsaya tsayin daka kan almarin ta kasan sai asibitin mu muna da likitoci k'wararru so kar ka damu." Gyada kansa yayi yace." Yaushe za'ayi aikin." ? Jahid yace." Insha Allah ranar Monday za'ayi." Saura kwana uku kenan."? Jahid yace." Eh saura kwana uku. " OK Allah ya kaimu nagode K'warai. " Nan granny ta futo daga kicin ta same su, suka gaisa da Mujahid cikin barkwanci sannan ya bar gidan Amjad din ta kalla a nutse tace" Aishatu ta tashi ne."? Girgiza kansa yayi kamar wani maraya. Granny tace"Sai hakuri ka kwantar da hankalin ka naga kamar ka tada hankalin ka, insha Allah komai me wuce wa ne." Shiru yayi mata kawai. Ita kuma ta wuce daining domin shirya kayan breakfast. ******* A gajiye na dawo daga makaranta na zube rumfar Umma cikin gajiya da ishirwa nace"Wallahi Umma da nasan zan sha wahala haka da ban dauki azimin nan ba, kinga yau juma'a anyi rana mutuka ." Tace"Hakane ai zaki samu lada sosai. " lumshe idona nayi kawai ishirwa Duk ta dame ni, so nake a idar da sallahr la'asar nayi wanka ko zanji dadin jikina. ********* Tunda motar shi ta shiga prison din, masu gadi da ma'aikatan gurin suke murna da zuwansa dama duk karshen wata yake ziyartar su, irin wannan ranar ta juma'a bayan sakkowa daga sallahr juma'a. Daurarru dake kulle suna hangoshi ta tagogin dakunan su. Murna da farin ciki ya ishe su. Bayan motar shi wasu manya manyan motoci ne na company *Dangote* suka dinga shigowa cikin prison din, dukaninsu suna dauke da kayayyakin abunci na'ui ka daban-daban. Ba tare da b'ata lokaci ba, 'yan jarida dake gefe guda suka mike domin fara'a aikunsu, dama duk wannan ranar sukan kasance a gurin da suka San yana zuwa kai ziyara, matasa majiya k'arfi ne suka fara sauke kaya suna ajewa inda aka tana da Yana cikin mota Duk yana kallon abunda yake faruwa da irin hayaniyar da ake a gurin. Sai da suka gama kwashe kayan tsaf, sannan ya futo daga motar Aikuwa 'yan jarida suka yi caaaa! A kansa basu nemi suyi magana dashi ba, amma sun baibaye shi suna d'aukar hotonsa hade da vidio duk wani motsi NASA sai sun dauka duk inda ya sanya kafa sai sun bishi. Ofis din shugaban gurin ya nufa. Suka bishi a baya sai da suka ga ya shiga ofis din sannan suka dakata, Rambo da doh-doh suka tsaye bakin kofar suna zare ido. Hamshakin mutum ne zaune kan kujerar sa sai juyi yake, kana kallonsa zaka San bashi da imani fuskarsa a murtuke take leb'anshi baki kirin kana gani kasan yana shan taba da abunda ba'a rasa ba, yana da manya manyan idanu,hanci sa yana da fad'i amma ba sosai ba, sannan yana da kiba dai-dai misali. Duk wani Abu da yake faruwa ya na gani ta CCTV Duk ta hasko masa komai da zuwan Amjadu gurin da yanda mutane suke ihu da yanda 'yan jarida suke turereniya akan sa, duk ya ga komai. Wani irin b'acin rai da kyashi duk suka dame shi, mugun haushin yaron yake ji saboda ya zame su kadangaran bakin tulu. Abun mamaki suna hada ido da Amjadu din yaji gabansa ya fad'i, Yaron yana da kwarjini da haiba, take ya gyara zama yana masa barka da zuwa Kafin ya zauna hannu ya fara mik'a masa suka gaisa a muntunce. Sannan Amjadu yace." Fatan duk na same Ku lafiya."? Alhaji Gali yace." Lafiya lou Alhmdullahi Ashe ka dawo gari. " Babu walwala a fuskarsa yace." K'warai kuwa jiya na dawo insha Allah." Kamar gaske Alhaji Gali yace." Ka cika Dan halak me son talakawa abunda gomnati ya dace tayi bata yi kai gashi kayi mungode K'warai ubangiji Allah ya kara k'arfin a arziki. " Amjadu ya bashi hannu suka gaisa, yace." Naga muna daf da shiga wata me albarka ga kayan abunci nan insha Allah daf da sallah zan turo musu kayan sawa." Alhaji Godiya yake kamar gaske. Amjadu ya Mike hade da yi masa sallama ya futa. Yana futa Aljani Gali ya dauki wayarsa ya fara kiran me girma governor, sai da ya kira sau kusan uku sannan aka dauka, da sauri Alhaji Gali yace." Allah ya tai make ka?" Governor ya gyara zama kan kujrrarsa Cikin ginshera yace." Tare

Table of Contents

Chapters

78 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});