Chapter 40
Chapter 40
na lura bani kadai ce na shiga halin d'imuwa ba har da k'awayemu suma duk jikinsu yayi sanyi ganinshi narasa me yasa yake wa mutane kwarjini haka,mussaman mata. Addu'ar Neman nake cikin zuciyata, *"Wallahu galibun ala'amri."* wannan addu'ar nake yi cikin zuciyata domin ina ganin zuciyata zata iya tona mun asiri, a gurin, shiyasa na dauki alk'awarin bazan k'ara kallon inda yake ba, suna. Tafiya ana musu vedio da hotona har suka Isa gurin zaman su, muma muka samu guri muka zauna, sannan guri yayi shiru mai gabatar wa ya tashi ya gabatar da malamin da zai fad'a kar kam zaman aure da abunda auran ya kunsa Wa'azi yayi kyau kuma ya fad'ar kar sosai bayan ya gama. Masu rabo suka shigo suka fara raba wasu manya-manyan ledoji komai cikin nutsuwa akeyin shi, ko da wasa naki kallon inda suke zaune, hira ma muke yi da Maryam tana k'ara fada min Yanda Mimi tayi dace da miji tana fadin"Dole sai tayi da gaske domin akwai 'yan matan shi da suka d'aura arinyar akanta mussaman Alina." Nace"Dole kuwa Alina kinga ko zuwa bata yi ba." Maryam tace"Yaushe zata zo matar da tunda taji abun take tada Aljanu." Dariya nasa Ina rufe fuskata da hannuna kawai sai naga hasken flash dago kaina nayi da sauri, naga d'aya daga cikin abokan shi Wanda suka sanya kaya iri daya yana tsaye a kanmu nida Maryam sai daukarmu a hoto yake mussaman ni. Bata fuska nayi ina kallon shi, murmushi ya sakar min, tare da kashe min ido daya. Dauke kaina nayi ina Jan tsaki k'asa-k'asa. Gurin ya bari yana duba wayar shi, hotona yake dubawa Duk abunda yake faruwa tsakanin Mujahid da Asma'u a kan idonshi, yasan halin Mujahid akwai son matan tsiya gashi dai da auran shi, amma in yaga mata jikinsa har tsuma yake, yaji wani iri a zuciyarsa amma kallon da yaga Asma'u na watsa ma Mujahid din ya ji dad'i a zuciyarsa yace." Mata masu daraja kenan." Mik'ewa nayi daga gurin ina waige-waige Su Munnu na can baya an had'u da samari ana hira da ciye-ciye ganin na mike yasa Maryam mik'ewa muka fara ratsa jama'a tafiya zamu yi tunda dai an gama ango ya kawo amaryar sa gida domin na tsani kallon da maza suke min. Aikuwa ido yayi caaaaa! A kanmu ni kaina a jikina nasan kallona ake yi, cikin sauri sauri nake tafiya inda sassaan jikina yake motsawa, sai tsaki nake. Amjadu kuwa tun lokacin da ta mike tsaye ya karewa jikinta kallo kuma yaga yanda shatin jikinta ya futo ta cikin sharara din mayafin ta, sai yaji kamar ana soka masa kibiya a kahon zuciyarsa, mussaman. Yanda yaga maza da dama sun raja'a a kanta, gumi ya tsinke masa, lips d'insa ya tura a baki yana ji kamar ya hadiyi zuciyarsa ya huta da wannan bakin ci, Mimi ya kalla a sace ya ga Sam ita babu wani abun assha da dinkin ya futo mata dashi, ya rasa wace iri ce Asma'u me karuwan jiki, ko wane irin kaya tasa sai sun tona mata asirin jiki. Innalillahi wa'inna'ilah raji'un. " shine abunda yake nanatawa cikin zuciyarsa ko ya samu sassauci. Ganin duk sun mike ne suna kokarin futa daga gate sai hakan yayi masa dad'i mutuka wayar sa ya dauka yana kiran Rambo yace." Maza'a maida su gida shi da kansa zai kawo Mimi gida aikuwa haka aka yi, muna kokarin shiga mota ne sai ga Muhajid ya k'araso gurin, hade da kure ni da ido yana sakin wani murmushi, yace." Asma'u." Nayi mamakin yanda ya San sunana haka, babu yabo babu fallasa nace." Na'am ya kake."? Murmushi yayi Wanda na lura hakan d'abiar shi yace." Lafiya amma ba Lou ba, tunda na ganki na rikice na gigice na dimauce na rasa nutsuwa ta, Asma'u ina kaunar ki fisabillah." Ya k'arashe maganar sa har da kwantar da kansa, Su Munnu kuwa dariya suke masa, yace." Ina da mata da yara biyu ni ma'aikacin lafiya ne, ina aiki a nasarawa hospital ina fata zaki so ni kar kice na miki tsufa." Yanayin barkwancin sa da yanda yake da sakin fuska da wasa da dariya yasa na saki fuskata nace"Ashe dai ka sani ni kam kayi min tsufa bazan auri me mata ba." Marairaice fuska yayi hade da fadin "Don Allah kinji. " sai na tsinci kaina da sakin dariya har fararen hak'ura na suka bayyana Wanda yayi dai-dai da zuwan Amjadu gurin Hannunshi rike da na Mimi, ina ganinshi na dauke kaina da sauri gaba na lugude, ko kallonmu bai yi ba nida Mujahid ya fara magana dasu Rambo Wanda suke kokarin saka mutane a mota, Ina jin Mujahid nace "Aboki nifa nayi mata a gurin nan gaskiya naji dadin wannan ranar wallahi na tsinci dami a kala." Babu yabo babu fallasa ya kallemu dani dashi yayi wani killer smile As'usuel ya sosa kanshi tare da fadin"Kayi dace Aboki amma bakayi gaggawa ba, kuwa." Mujahid yasa dariya tare da fadin" Wane irin gaggawa kuma in tsaya kallon ruwa kwad'o yayi min k'afa." Kamar babu abunda yaje damunsa ya sanya dariya tare da fad'in"OK ni babu ruwana wallahi kai da Madam."! Mujahid din yace." Shareta ai ba da ita kadai zan zauna ba." Shiru yayi masa ya cigaba da magana da Rambo, ko da wasa ban kalli shi ba sai ma sauri da nayi na bude motar na shiga. Ina kallonshi ya rungume kafad'un Mimi a jikinshi lokaci-lokaci yana sumbatar goshin ta, hade da yi mata magana k'asa-k'asa, da sauri na kauda kaina dama tsautsayi ne yasa na kalleshi, Yanzu kuwa Allah Allah nake motar ta tashi mubar gurin. *16/November/2019* [11/17, 1:56 PM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO* *MALLAKAR_ BINTA UMAR* *LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA SAI TA CI SHI* *54* Sai ya tabbatar da motocin su sun tashi sannan yaja hannun Mimi suka bar gurin, cikin sauran abokan sa ya koma masu hoto suka dinga d'aukar shi da Mimi sai sunkuyar da kanta take cike da kunya shi kuwa rumgumeta yake jikinsa fuskar sa a sake, 'yan jaradi ma ba a bar su a baya na sai da suka zo ganin k'waf tare da d'aukar amarya da ango hoto da vedio walima tayi kyau sosai kuma ta k'ayatu, k'arfe 11:30 gurin yayi sauki jama'a duk sun a watse a gajiye yake sosai amma babu yadda ya iya dole ya maida Mimi gida. Hannunsa rike da nata babu um bare umum suka shiga mota tare Doh! Yazo da sauri, sai ya daga masa hannu alamun a'a baya ya matsa, yana d'aga masa hannu yaja motar suka futa daga Estate din.. Sai da ya hau kan kwalta sannan ya kalleta a fakaice yace." Momy kin gaji wannan idon naki akwai bacci a cikinsa."? Mimi tayi kasa da kanta tana wasa da hannunta tace." Wallahi na gaji sosai hankalina yayi gida." Cike da tsokana yace." Da har ina cewa kinzo kenan baza ki koma gida ba." Kauda kanta tayi cike da kunya, hira sama-sama suke yi da ita kamar wasu surukai har
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78