Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 8

Chapter 8

A Tsakanin Soyayya Book 1 Complete Hausa Novel – Aliyu’s Romantic Journey Begins 1,205 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Hajar ma bata gaidashi duk kun hana kaninshi gaidashi saidai idan sunga Dady ne zasu gaidashi, haba Mama kiji tsoron Allah, _d'a na kowane_ maiya muku eh? Idan yanzu kika mutu akamana haka yaya zaki dingaji akabari" shaketa Mama tayi ahaukace jitake kaman ta kashe ta tace "nikike kirama mutuwa Rauda akan Aliyu? Ba dangin iya bare na Kaka, saidai ke kimutu baniba kinji shegiya wacce ta debo jinin dangin ubanta mai bakin zuciya" ganin idanunta na juyawa yasa Anty Hajara da itama take mugun jin haushin kanwar nata sabida taurin kanta tazo ta cire hanun Mama daga wuyanta tace "ya isa haka Mama" cikin fushi da mugun masifa jikin Mama har barbar yake tace "Hajar ki barni na kasheta, baidai tafison wani kato akan uwarta ba, goben nan zakiji kishiyoyina sun faramin habaici na haifi munafuka, zataci ubanta ne saisa gwara ai aurenta da Khamis ta tattara tabar gidan nan ta tafi gidan mijinta nahuta inba hakaba bakin cikinta zai kasheni ne, dama Khamis din yacemin gobe zaizo yadauke ki kufita kibishi kufita dan kin gama zaman gidan nan balle kije kinama wani kato girki kega kuku yakarata chan daci a restaurant shidai da gidan ubanshi ba amma wlh bazaici abincin gidan ubanshi ba zan gyara miki zamane Rauda" ahankali Hajara trying to calm Maman su down tace "ya isa Mama kiyakuri, Bazata sakeba" dan shiru Maman tayi tana kallon yanda Raudan taduka tana kuka sosai mara kara kafin tai kwafa ta kalli hadadden akwatin data shigo dashi tace "kuma shegen akwatin nan kona shege zanyi" tasa hannu zata dauki akwatin da gudu tarike akwatin cikin kuka tace "Mama dan Allah ki barmin abuna" hannu Mama tasa zata fizge akwatin tarike gamgam tana kuka, cikin kunan rai Hajara tace "wai bazaki saki akwatin ba Rauda kanin ubanki ne yabaki akwatin, kisaki akace" cikin kuka sosai ta girgiza musu kai taki saki dan son abubuwan ciki takeyi sosai, Mama jitayi kaman ta kashe Rauda tahuta zata jibgeta Hajara tai sauri ta tare tasa hannu ta daki hanun Raudan tace "sake shegen akwatin" ta hankadeta tareda fizge akwatin tamikama Mama dan ayanda taga mama tasan zata iya jima Rauda ciwo ayanda ta zuciyan nan. Karban akwatin tayi ta kalli Raudan dake kuka kaman zata mutu tai kwafa tajuya tafita daga dakin tsaki Hajara tayi ta balla mata harara tahau kan gadonsu cikeda takaicin Raudan tai baccinta, sosai Rauda taci kuka harta godema Allah ahaka bacci yay awon gaba da ita awurin. [4/5, 8:05 AM] Hijabi_muslimah🙌: _*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_ _IN BETWEEN THE LOVE_ ❤ _Lies another love_❤ _✍🏿M Shakur_ 3️⃣ _How to subscribe_ _*zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turamin evidence of payment to WhatsApp number na 07012181461 sainai adding dinki a group din danake posting*_ _*zaki iya turo katin MTN 300 ta WhatsApp number na 07012181461 sainai adding dinki a group danake posting*_ _Free page_ Da asuba ya tashi da kyar shima sabida alarm din gefen gadonshi ne daya saita yatadashi, tashi yayi ya shiga bathroom, yadade aciki kafin yafito cikin wani blue bathrobe, zama yayi abakin gado ya shafa manshi mai kamshi a tsanake sanan yatashi wardrobe dinshi yaje yabude yaciro wani black belted cotton poplin cargo trouser da wata farin logo print t-shirt na Ambush yadauko yasaka, yabude bangaren rigunan sanyin shi yana tunanin wanda zai saka kafin yajawo wata logo embroidered wool fleece jacket itama ta Ambush, yasaka rigan tazauna ajikinshi tamai kyau sosai, yadau designers turarukan shi ya fesa sanan ya shimfida dadduma yay salla yana sallame wa yaji ana bugamai kofa, yatsine kofa yayi sanin mayun nanne, da kyar cikin isa da izza yace "come on in" bude kofa bodyguard din yayi rikeda wata yar karaman tray da small mug of hot coffee kekai, karasowa gabanshi yayi ya ijiye tray kan dadduman yace "have this sir, we are leaving in the next 10min" daure fuska yayi yace "where is d other guard? Lucas is his name right?" yay maganan yana mai alamu da yatsa ayangance, gyadamai kai bodyguard yayi yace "yes he's Lucas, I left him outside he's packing out luggage to the car" yatsine fuska yayi as usual yatashi daga kan dadduman yahau kan gadon yazauna yamai pointing coffee da yatsa alamun yabashi ysha, daukan coffee yayi da sauri ya mikamai karba yayi yakai bakinshi yay sipping dan ficili ya zare daga bakinshi batare daya kalli Guard dinba yace "where is my phone? Dad dina yakirani?" "your phone is here sir" yakarasa kusa da bedside lamp yadau wayarshi dat was lying there yadauka ya danna wayar dababu any security lock ajiki yace "No sir, babu miss call din kowa" dan kwafa yayi baisake cewa komiba yacigaba dashan dan coffee ayangance sanan ya gama yatashi ahankali yay gaba bodyguard din ya gyara ko ina sanan ya kashe wuta yabiyoshi waje harya shiga mota yawuce ya shiga gaba suka wuce Airport. Sai fushi fushi yake sabida Dad baikiraba shikuma bazai kirashi ba saisama yabarma bodyguard din wayar dan yasan in yana hanunshi zai iya yakirashi, ya tsani British Airways dan sunada wani banzan dabi'an batarma da mutum luggage saisa tun jiyan yasa suyi booking air France, sai tunanin uban zaman dazaiyi cikin jirgin yake inhar basuyi stopover ba flight dinshi is 18hrs flight inkuma jirgin ya tsaya for fueling ko cleaning kokuma wani dai emergency, kokuma weather issue zasu iya 20hrs or more than sef saisa he came prepaid yasa kayan sanyi idan ya shigama he will request for a blanket or showel duk wanda suke danshi gaskiya shi bazai saka pyjamas din airline ba, kuma yanada matsalan jin sanyi sosai, checking in sukayi suka karbi ticket sukai departure lounge basu wani dadeba suka fara boarding karfe 7:15 jirgin su yadaga sai kallon lokacin yake yana kokarin hararo wat time is it yanzu a Nigeria, dan Nigeria is almost 9hrs ahead of California, dan murmushi yayi ganowa dayayi yanzu darene a Nigeria probably hala Dad yay bacci saisa bai kirashi ba. 8:40 na dare jirgin su yasauka a Abuja, fitowa sukayi kana ganinshi kasan yagaji sosai saukowa suka farayi bodyguard dinshi biyeda shi, wuraren Tara suka gama komi suka fito ta arrival sai kalle kalle yake ya tsaya chak dan baiga wani nashiba baiga wani direban gidansu ba baiga Daddy ba, wani irin haushi ne yakamashi yamikama bodyguard hannu alamun yabashi wayarshi, karban wayan yayi dayariga ya kunna mai ya shiga dialog Dan kiran Dad dinshi, fizge waya yaji anyi daga hanunshi da sauri yadago kai wani magidanci ne kamansu daya sak dan shima farine sol alamun tsufa daya bayyana tattare da magidancin ne zaisa kawai kagane ba yan biyu bane uba da d'a ne, dudda fushi yake da Dad amma baisan lokacin dayasaki wani murmushi ba yawani irin rungumeshi ba so tight yace "Daddd dy" murmushi sosai mutumin yayi yana bubbuga bayanshi yace "na'am Aliyu na, sarkin zuciya, Aliyu an mazajena" dariya daga shi har Aliyun sukayi sanan yasake shi ahankali yana kallonshi kaman yanda yake kallonshi yace "muje kahuta kagaji da yawa karka fadi" sukai wajen mota bodyguard na binsu abaya, motoci biyune bodyguard suka shiga dayan Daddy da Aliyu kuma suka shiga motar Daddy, kwanciya yayi ya daura kanshi kan cinyar Dad yana yatsine fuska, kallo baban

Table of Contents

Chapters

78 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});