Chapter 43
Chapter 43
rame haka?" lumshe ido yayi kafin ahankali yabude idanunshi harsun dan chanza launi sunyi ja murya chan kasa cikeda damuwa yace "please tashi ka shirya" yanda duk yay wani iri yasa Abdul yaji tausayin shi dan yaga son yarinyar a idanunshi hakan yasa yasauka kan gadon ahankali yawuce ya shiga bathroom baiwani jimaba ya watso ruwa yafito ayanda yabarshi yazo ya tarar dashi yawuce wajen wardrobe dinshi shiryawa shima yayi cikin manyan kaya kaman na Aliyun yay kyau ya feffesa turare yajuyo yace "let's go" tashi yayi ahankali hannu Abdul yamika mai yace "car key karkazo ka kashe ni ahanya hakanan banyi aure na more ba" dan murmushi yayi saikuma ya yatsine fuska yazaro key yabashi karba yayi suka wuce suka fita, kallo Momma tabisu dashi kafin ma su karasa saukowa daga stairs tace "sai ina haka yan samari?" Abdul zaiyi magana Aliyu yarigashi yace "yanzun nan zamu dawo Momma" tabe baki Momma tayi tace "kwaji dashi kayan tusa, intai tsami maji, adawo lpy" wucewa sukayi suka fita suka shiga Abdul ke driving har asibiti, saukowa sukayi sukai ciki suka shiga reception, nurse din jiyace tana ganin Aliyu tagane shi da sauri tafito daga bayan kanta tasha gabansu tace "Sir barka da zuwa, kunsha bambam ne da patient din koba ita kazo nema ba?" gyada mata kai yayi ahankali, da sauri tace "ai bamasu dade da tafiya ba, an sallame su, wlh ansalame su suntafi gida, saida ma nataya namanta daukan jaka namusu rakiya har mota" shiru Aliyu yayi duk yaji ba dadi, ganin yama kasa magana yasa Abdul yace "thank you bari mubisu" ya kalli Aliyu yace "let's go" binshi abaya Aliyu yayi suka fita ganin duk yanda Aliyun yayi yasa yace "kasan gidan sune?" gyadamai kai yayi. "inane?" ahankali yace "Suleja, Sulejan mu?" gyadamai kai yayi daidai sun karaso mota suka shiga Abdul yay reverse suka fita daga gidan. Tunda suka isa gida Ammi ta shiga kitchen tafara hada musu abinci itakuma Aneesa dasu Baffa suna falon su suna mata fira danji da ita suke bana wasaba Baffa ma da kanshi yafita yasiyo mata gyada dafaffa gwangwani biyu aiko sai ci take aranta sai murna take ashe haka akeji da mutum idan yay rashin lafiya ko wash tace sai an tambaye ta meke damunta. Shigowa Ammi tayi da manyan kulolin tuwo ta kalli su Baffa tace "akawo miya Alhaji kuci yanzu" girgiza mata kai yayi yana tashi saga gefen Aneesa yana kakkabe riga yace "bari mudan shiga gari nida Na Sani, bayan isha maci kokai zakaci yanzu?" girgixa mai kai Na Sani yayi yace kinji ko, yajuyo ya kalli Aneesa yace "mezan siyo miki inzan dawo?" washe baki tayi tace "Baffa kashu nakeso" hararanta Ammi tayi tace "aikin kenan kwadayayya" rufe fuska tayi da hannu tana murmushi Baffa yadaga ma Ammi hannu yace "kinga, kinga ki barmin diya tahuta yaushe duka duka tafarfado dan haka dole taci tasha abinda takeso, zan taho miki dashi, anjima ai wayanki kinada kati ko" gyadama Baffa kai tayi tace "to kimin flashing danna tuna" da sauri tace "to saikun dawo Baffa" wucewa sukayi suka fita ta kalli Ammi tareda kyalkyalcewa da dariya kwafa Ammi tayi tace "zan cinmiki ne" tawuce tafita daga murya tayi tace "Ammi nazo nataya ki?" daga kitchen Ammi tace "sha zamanki, nama gama kaye kayen kitchen zanyi" Ammi tadau tsintsiya tana gyara kitchen din dan ansoma kiran magrib, turo kofar gidansu da akayi yasa ta ijiye tsintsiya ta leko tsakar gidan wani dan yaro ne yakara so tsakar gidan, fitowa Ammi tayi daga kitchen din tana kallon yaron tace "kai lafiya baka iya sallama bane" murmushi yaron yayi yana jan hanci yana share majinan kan hancin shi yadaga murya yace "Assalamu Alayyykummm wai ance Aneesa tazo awaje" da sauri Ammi tace "injiwa ye?" "nima bantaniba" yay maganan yana goggoge majina da hannu tsumman dake jikin window kitchen dinsu Ammi taja tadan barki kadan tazo gaban yaron tace "zo ashare majinan" sharemai majinan hancin tayi dana hannun shi sanan ta wanke mai hannun da ruwan dake cikin bucket din gaban rijiya tace "wai ance waye?" da gudu yaron yajuya yafita, yaye labulen bakin kofar su Ammi tayi tadaure fuska tace "waye yazo neman ki?" zuru zuru tayi tace "nima bansaniba Ammi" baki Ammi tabude zatai maganan saiga yaron ya shigo da gudu yace "wai yace Yusuf security ne" dan zaro ido Aneesa tayi tace "laaa Yusuf, Ammi mai budema mutane kofan shagon mune, security, hala Madam ta aikoshi" dan jimm Ammi tayi kaman mai tunani kafin tace "dauko hijabi kije kecemai rashin lafiya kikayi saisa basu ganki ba" gyadamata kai tayi takoma falon tadauko baby pink hijabinta har kasa dayay mata kyau fuskanta yay dan fayau aciki ta zura kafanta a slippers batare data tsaya saka safa ba tawuce tafita ahankali tabude kofa tafita, a kofar gidansu taga Yusuf Security zaune kan dan machine dinshi dama uniform dinshi bai chanza ba zuwa kayan gida, ganin Aneesa tafito yasa yasauko daga kan machine yana murmushi yana kallonta daidai lokacin Abdul yayi parking next to kofar gidansu Aneesan daga shi har Aliyu sun zubama on Aneesan data fito daga gidansu tana tafiya ahankali ido, karasowa gabanta Yusuf yayi cikeda damuwa yace "lafiya baki zuwa aiki Aneesa? Maiya same ki fuskan ki duk yay wani iri haka kin kumkumbura idanunki sun fada ciki" ahankali tace "rashin lafiya nayi yau aka sallamoni daga asibiti, ya akayi kasan gidanmu" cikeda damuwa kaman zai hadiyeta danso yace "innalillahi Aneesa rashin lafiya, no wonder tunda nadena ganinki nadena jin dadin rayuwana wlh ko aikin bayamin dadi sam sam, na damu iya damuwa shine nace bari kaga ko bango duniya kike inhar a Sulejan nanne saina nemo gidanku naji ko lafiya" dan murmushin yake tamai koba komi yay kokari tunda har yay tattaki yazo yaji ko lafiya, dan murmushi tasake yi tace "nagode" yanda tai murmushin tana dan juyakai yasa yaji zuciyar shi ya narke ahankali yace "wayyo Allah na, murmushin ki na haukata min zuciya da kwanya" gimtse fuska tayi tana kallonshi ganin haka yasa yasaki dariya yana daga hannu yace "maida wukan to, haba Aneesa sarkin masifa, ke baki bari ta tafasa balle to kone ba'a dan zolayan ki" Ahankali Abdul dake kallon su Aneesan batare daya kalli Aliyu ba yace "is she the one Leo?" jin shiru Aliyu bai amsashi ba yasa ya juyo ahankali ya kallai su ya gani yana kallo idanunshi sunyi ja sosai kirjinshi na bugawa da sauri sauri danko shi yana ganin yanda kirjin ke sama da kasa tagaban rigan, da sauri yace "Leo, Leo are you okay?" wani irin bude kofa Aliyu yayi yafita daidai lokacin Yusuf ya zura hannu a aljihun wandon shi yaciro dari biyar ya mikama Aneesa yana murmushi yace "ga wanan asai su lemu asha Aneesa" da sauri ta girgixa kai tajuya zata shiga gida tace "kabarshi nagode, saida safe" hannu yasa yakama hijabinta yace "a'a wlh saikin karb......" wani wawan mari aka dauke shi dashi dayasa Aneesa dake kokarin bude kofa juyowa da sauri dan bama tasan yarike mata hijabi abinka damai dogon hijabi, hada ido tayi da Aliyu da idanunshi sukai jajir yana wani irin kallonta, Yusuf dafe kuncin shi yayi dan marin ya mugun shigan shi yana kallon fuskan Aliyun, dauke kai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78