Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 63

Chapter 63

A Tsakanin Soyayya Book 1 Complete Hausa Novel – Aliyu’s Romantic Journey Begins 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

daki tace "ainazaci afalo kikecin abincin shine nace barina biyoki" girgiza mata kai Aneesa tayi, cikin yar siriruwan muryanta tace "a'a, mukoma daki" juyawa Ihsan tayi sukai sama. Ahankali ta zauna kan gadonta rikeda plate din abincin tana murmushi tana juyawa tana tunanan kalaman Aliyu dake ratsa mata zuciya, tana wani irin karajin maimaicin kalaman shi a kunnuwanta, tabatan da akayi yasa tadago kanta da sauri Ihsan ne kaman zatai kuka tace "kinki kulani, ba Momma tacemin mun zama friends ba, kodai bakisona ne a matsayin kawarki" da sauri Aneesa ta girgiza kai tareda ajiye abincin agefe ta zare hijabin jikinta ta ijiye tace "laaaa, no bahaka bane ina sonki a matsayin kawata sosai ma" murmushi Ihsan tayi cikedajin dadi tana kallon jikinta, wani milk color shimi tasaka ya kwanta a jikinta bulbul ya bayyanar da kirjinta sosai kaman zasu yaga sufito, murmushi tayi tace "to yaushe zakizo gidanmu ki kwana?" ahankali Aneesa tace "nima bansaniba amma zan tambayi Ammi da Abba insun barni zanzo I promise" murmushi Ihsan tayi tace "to shikenan dau abincin ki to kici hudu takusa zaku koma islamiya kumako" gyadamata kai Aneesa tayi ta faracin abincin haka Ihsan keta mata hira babu labarin makarantan su dabata bataba harta cinye abincin hira takemata, kwalama Aneesa kira da Ammi tayi yasa ta amsa da sauri. "na'am Ammi" daga tachan Ammi tace "kin manta zaki islamiya ne ko" da sauri ta kalli agogo hudu saura minti biyar, da sauri Ihsan tace "la mun manta tashi da sauri ki shirya" tashi tayi ta shiga bayi tadauro alwala tazo tai sallan la'asar sanan tai wajen wardrobe dinta, wani dogon rigan yar kanti tadauka baki ne color tasaka, tazaro wani clean ironed mustard color hijabinta har kasa tasaka tasaka safa sanan tadauko wani dan babban jakanta ta kwashe littatafan da aka bata aciki ta rataya ta kalli Ihsan dake ta binta da kallo itadai tanason wanan Aneesan tarasa mesa, waya Aneesa ta mikamata tace "gashi samin number ki zamu dinga WhatsApp" sakamata number Ihsan tayi sanan tarakota suka fito afalo sukaga Ammi da Momma sai hira suke Momma tace "har anfito yan islamiya to adawo lafiya" Ameen tace tana kallon Ammi dake binta da kallo batare datace mata komiba, turobaki tayi a shagwabe tace "Ammi bazakimin addu'a ba" dariya Ihsan tayi tace "laaaa ashe kina shagwaba katuwa dake" murmushi kawai Ammi tayi tace "wanan Ihsan, aina kosa Allah yakaimu ranan aurenta nayi na tarkatata nakaita gidan mijinta nagaji" kaman zatai kuka tace "niba inda zani ina tare da Ammi na" dariya dukansu sukayi Ammi tace "bazaki wuce kitafi ba kin tsaya surutu sai kinyi latti, kyasha dukan latti, adawo lafiya to Allah kiyaye, banda wasa kuma adage da karatu" bye tama Ihsan sanan tawuce tabude kofa tafita daga dakin already taga har yara sun cika wurin motar ana jiran driver yazo yabude su shiga, ahankali take tafiya tana nufan parking space din kaman ance ta daga kai da Aliyu suka hada ido dake gaban shashin shi yana mata wani irin kallo yay folding hannunshi a kirji, dauke kai tayi kirjinta na bugawa tarasa mesa kirjinta ke bugawa duk inta ganshi kasa daurewa tayi tadan dagokai ta kallai sake hada ido sukayi har lokacin itayake kallo kaman zai cinyeta da idanu, samin kanta tayi da dagamai hannu kaman wata yar koyo taimai waving hand din alamun bye da sauri ta kalli hannun nata kaman ma batasan lokacin data dagashi ba, dan murmushi yayi tareda lumshe ido yabude su ahankali yana kallonta ahankali yay waving nata back irin waving dinan na yaron dabayason maman shi tafita, dauke kai tayi da sauri tadena kallonshi dan hakanan taji yawani irin bata tausayi kaman zuciyanta da nashi na communicating, kaman zuciyanshi nace mata karki tafi kidawo ki zauna dani. Karasawa wajen motan tayi har direba yabude yaran duk sun shiga Hajar ne kadai agaban motan, wani matsiyacin kallo tama Aneesan tace "gasu agola nan anzo" daidai Aneesa takaraso wajen Rauda dake cikin motan dan ciwon cikin yasaketa sosai yanzu tace "kai Anty Hajar wlh babu kyau fa" ta kalli Aneesa datai kaman batajisu ba tasakin mata murmushi tace "shigo ki zauna Aneesa" murmushi itama tamata dan sai yanzu ne tagane Rauda itace yarinyan data taimaka ranan data fara ganin Aliyu sarkin kallo sai kallonta yake kaman baitaba ganintaba, shiga cikin motan tayi ta zauna kusada Rauda, Hajar ta shigo itama sanan direba yarufe kofan yakoma gaba ya shiga yaja. Ahankali Rauda tasa hannunta takarbi hannun Aneesa data danyi wani zanen lalle ta around kumbunan ta tace "wow Aneesa wanan wani irin zanen lalle ne? Bbu kodaya a hannunki saita wurin yatsun ki it really looks nice, waya miki ya bala'in burgeni, waya miki?" murmushi Aneesa tayi tana kallon yatsun nata zanen datayi ne da bikin Ammi saitama Ammi kuma lalli mai kyau, ahankali tace "ninayi" "iyye kin iya lalle ne daman?" gyadamata kai tayi tace "na iya, kinaso namiki?" da sauri Rauda ta gyada mata kai tace "inaso mana, sosai ma" ahankali Aneesa tace "shikenan duk randa kika shirya zan miki wanda ma yafi wanan kyau" washe baki Rauda tayi tace "nagode, Awani aji aka saki dazu a hadda?" ahankali tace "aji hudu, islamiya ma aji hudu" bangaje mata kafada Rauda tayi cikeda jin dadi hira irin na kawayen nan tace "iyye ajinmu daya ashe, nima dazu dasafe cikina keta ciwo saisa banjeba wlh" ahankali Aneesa tace "sorry Allah ya sawake" cikeda damuwa Rauda tace "kema kinayin ciwon ciki idan zakiyi?" gyadamata kai Aneesa tayi batare datai magana ba she's not just comfortable sabida Hajar dake wurin, dan tana ganin yanda Hajar ke hararanta itada Raudan kaman ta bubbuge su, cikeda damuwa itama Rauda tace "sannu kinji Aneesa, ance inkai aure yana denawa" "dalla malama kimana shiru ko kina maganan iskanci agaban yara" Hajar tafada cikeda masifa, cikin tsiwa Rauda tace "to wai me ruwanki dani Anty Hajar, yaran sunsam menake cewa ne, kinamin wani ihu saikace nayi dake" ta harari gefen side din Hajar din, murmushi Aneesa tayi hakan yakara harzuka Hajar tace "dan ubanki nikekema rashin kunya?" cikeda rashin kunya Rauda tace "karki kara zaginmin uba nidai, Dady na nagida yana hutawa abinshi kina duramai zagi, kuma ai badake nakeba daga ina firana da kawata saikiyi ta zagina, dakenayi? Neman tsokana kawai" kwashe wa da dariya yaran motan sukayi, wani mugun kallo Hajar tamusu hakan yasa at ukai shiru, Hajar tai kwafa tace "zamu koma gida kaman Mama taji komi" dauke kai Rauda tayi tacigaba da hira ta da Aneesa batakara cemata komiba harsuka kai makaranta suka tafi ajinsu a binsu. *** Wuraren magrib suka shigo gidan, derevan su yay parking yafito tareda zagayowa yazo yabude musu, saukowa sukayi Rauda ta dubi Aneesa data sauko bayan ita tace "saida safe ki gaishemin da Mummy, gobe zanzo na gaisheta kinji, bari naje part din Ya Aliy...." fizgan hannunta Hajar tayi kaman tafizgo barauniya tace "dan ubanki bazaki ba, ba Mama tahanaki zuwa bangaren shiba" cikin tsananin jin haushi Rauda tace "wai me haka Anty Hajar, wlh kisakeni kona hadaki da Dady me ruwanki dani sai samin ido kike kina sauraron conversation dina" cikin fushi Hajar tadunkule hannu ta sakin mata mugun dundun abaya da har Aneesa saida tajishi har cikin ranta sabida karan dayayi dumm!

Table of Contents

Chapters

78 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});