Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 29

Chapter 29

A Tsakanin Soyayya Book 1 Complete Hausa Novel – Aliyu’s Romantic Journey Begins 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

tafara aiki, shigowa bakery Fatima tayi ta tsaya a bayan Aneesa tace "nike miki magana zaki wuce kiyi gaba abinki?" ajiye whisk din dake hanunta Aneesa tayi ta kalli Fatiman tace "Fati wlh idan baki fita daga harkana ba zan miki mugun jina jina, saurayin ki Yusuf babu abinda zanyi dashi ko shine namijin karshen duniya kifita daga harkana nagaya miki" itama ihu Fatima tayi tana mata tafi aka tace "eh, eh, kema kifita daga harkana ihu mayyar saurayi, saurayi snatcher" Aneesa zatai magana taji wayanta na kara da sauri tai wajen jakan ta tabar Fatima na surutan ta, ciro wayar tayi daga jaka ganin Aliyu ne yasa bata dauka ba ta maida ta ijiye tareda jan dan karamin tsaki tawuce ta koma ta shiga buga egg dinta da whisk bata kara cema Fatima komiba harta gaji da bala'in tafita daga wurin, cakes tafara hadawa tasaka a oven sanan ta shiga yin dough nasu chicken pie. Wuraren sha daya ta gama bakin almost 100psc tai recording ta dauko tafito takawo ma Fatima agaban kanta takoma tafito da sauran sanan tawuce backyard ta wanko hanunta da kafarta sanan tafio tanaji wayanta na ringing tasan Aliyu ne yasa batama bi takan wayan ba tawuce tafita tai sama tawuce office din Madam, knocking tayi aka bata izinin shiga bude kofan tayi ahankali ta shiga Madam ta dago daga rubutun datake ta tsareta da ido tace "Anesh na you" gyadamata kai Aneesa tayi tace "good morning ma" ajiye biron Madam tayi tana dauko wani paper tana dubawa tace "morning, why are you here? Menene yakare a store dama naga sugar yay kasa da corn flour, menene babu?" dan sosa gefen fuskarta tayi dan dagajin yanda Madam ke magana tadauka wani abune babu tazo fada, mayar da kanta kasa tayi tana wasa da yatsunta ahankali tace "Ma, ummm dama, dama sonake naje nai registration din jamb nariga nagama baking shine nazo daukan permission dinki naje yanzun nan nadawo saina cigaba da komi" nan da nan dan annurin dake kan fuskar madam ya bace tace "dole saikinje yaune?" dan rage murya tayi tace "Baban mu yace naje yau" wani kallo Madam tamata tace "baban ku?" gyadamata kai tayi tace "eh kanin baban mu" dan tsaki Madam tayi tace "ince dan nasan babban ku yamutu, kinyi baking abinda zai isa" da sauri ta gyadakai tace "eh bazan wani dadeba tunda rana batayiba lokacin ne ake cika wurin yanzun nan zan dawo" tsaki madam takaraja dan ko kadan bata so ta tafi tace "okay nabaki 2hrs,yanzu is eleven by 1 ko highest 1: 30 kodawo kobaki gamaba dan I can't stand loosing customers due to your negligence again yau" gyada mata kai tayi da sauri ta tsaya tana jiran tabata izinin fita, buga taburin madam tayi tace "bazaki wuceba bakisan time dinki kikeci ba" da sauri tajuya tafita daga office din tawuce kasa ta shiga rigan aikin da hijab din tacire tadau dogon hijabinta tasaka sanan tadau wayarta dake kan saman jaka tana dubawa 20miss calls datagani yasa tace "20" bude wayan tayi da sauri ta shiga gabaki daya 20 miss calls din duka na Aliyu ne, maida wayan tayi cikin jaka tace "to menene yaketa kirana haka" dan murmushi tayi taunawa da yace she's his friend tawuce tafita daga dakin tace zan kiraka anjima inmun koma gida, Fatima nata kallonta kaman zata hadiyeta wajen kofa tayi da sauri Yusuf yabude mata yana kallon fuskarta yace "ina zaki Aneesa?" batare data kalleshi ba tace "inda ka aikeni" tayi wucewarta, binta da kallo yayi yarike baki dama Aneesa bata da kunya? Yatambayi kanshi kwafa yayi dan duk Fatima ce taja Aneesa dake bala'in girmamashi ta raina shi haka. Keke napep ta tare tace "Suleja ICT center zaka kaini malam" "hamsin, hau muje" hawa tayi dan batason tsayawa ciniki da masu abin hawa har gaban ICT center taje taga students dayawa duk yan registration din jamb, kudin tabiyashi ta wuce ta shiga ciki wayarta dake cikin jaka sai ringing yake. Ciki ta shiga ko ina dalibai da kyar tasamu taje gaban kanta daya daga cikin ma'aikatan ta gaida tace "malam dan Allah nazo registration ne yaya zanyi?" zufan daya cika goshin shi ya goge dan wajen is so crowdy dudda akwai manya manyan fankoki amma kaman bakomi wani takarda ya nunamata yace "keji ki rubuta sunan ki, za'ayi ta kiranku according to numbers ne" gyadamai kai tayi tace "nagode" tawuce da sauri wajen paper dataga wasu dalibai na rubuta sunansu tsayawa tayi abayansu suka gama sawa sanan taciro byro daga jakanta ta matsa tareda daukan paper number 178 anan zata sa suna, kambu mutane har nawa agabanta itada awa biyu madam tabata sunanta tarubuta kaman wacce ke tsoron paper duk tunani ya kasheta. "Fateema Rufa'i Mai Kwato!" da sauri ta daga kanta jin ankira full name dinta ware ido tayi ganin wani malamin su daya koyar da ita tun daga SS1 a makaranta har zuwa SS3, shine malamin further mathematics dinsu, Malam Auwal Mazimaziz haka yan makaranta suka radamai ko maganan shi ake idan kace Malam Auwal baza'a taba ganewa ba saidai kace Mazimaziz kokuma kace dy/dx daga wani bene taga yake saukowa rikeda wasu takardu da yawa a hanunshi yana kallonta dogon namiji ne handsome black dashi yana sanye dawata faran yadi kanshi da hula yana kallonta murmushi tayi sosai tana kallonshi harya karaso mutumin data tambaya dazu yaje wurinshi yabashi takardun sanan yakaraso ta inda take akunyace tace "good morning Malam" murmushi yayi shima yace "good morning Fateema" murmushi tayi tace "Malam dama kananan" dan hararanta yayi yace "look at you tunda kukai waec da Neco muka sallameku kin kara waiwayan school kizo kidubamu ne? Inda kinzo aida kin gani ai mara zumunci kawai" a kunyace tarufe fuskar ta da Hijabi ita tai mamaki ma dayake mata fara'a haka Mazimaziz ai shine the most wicked Teacher a makarantan su, ko sajent saiya sallama mishi a iya duka, gashi ko test dinshi kafadi saiyay duka sunci dukanshi a makaranta kaman ba gobe. "jamb kikazo siya?" tambayar dayayi ya katse mata dan tunanin dataje da sauri ta gyada kai tace "eh nazo ai registration amma mutane nice number one hundred and seventy something" dan murmushi yayi yana zama akan kujeran gaban kantan yace "banda abinki ai da sassafe ake zuwa dan dalibai nada mugun yawa anan" dan zaro ido tayi kaman zatai kuka tace "bansani ba ne wlh" dan shiru yayi yana kallon fuskarta yanda tai kaman zatai kuka tana kallon wajen yanda aka cika ko ina. "Fateema" da sauri ta juyo ta kallai mikewa tsaye yayi yace "lemme see you off, kizo gobe da sassafe as early as seven zansa wani yay miki, ko yanzu ma aiki yamai yawane danasa yay miki but kizo gobe as early as seven fa kina jina" gyadamai kai tayi tana binshi abaya suna kukustawa dan fita daga wurin tace "okay sir" fitowa sukayi tana biyeda shi wani irin mummunan faduwa gabanta yayi Aliyu tagani tsaye yana sanye da jeans black dawani sky blue shirt yadan bude boturin kirjinshi idanunshi sanye da bakin glass ya rungume hannunshi a kirji dayake rikeda wayarshi Samsung galaxy fold, yana facing cafe din, yan matan premises din Cafe sai kallonshi suke dan yay bala'in yin kyau kaman bature,

Table of Contents

Chapters

78 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});