Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 42

Chapter 42

A Tsakanin Soyayya Book 1 Complete Hausa Novel – Aliyu’s Romantic Journey Begins 1,206 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

gida Aliyu yay horn, budemai gate gateman din yayi yana ganin Aliyu yahau washe baki yana dagamai hannu, shiga gidan Aliyu yayi yay parking da sauri gateman din yazo daidai Aliyu yabude mota yafito, washe baki Gate man din yayi yace "sannu da zuwa Alhaji yaushe kadawo Nigeria" dan murmushi Aliyu yayi yace "nadan kwana biyu" cikeda barkwanci gateman din yace "shine bakazo bikina bako, ko Abdul fa yaje a kauyen mu akayi, sunan matata Talatu mesa bakazo ba" "dalla chan kawuce kabama mutane wuri bazoba ba din" sukaji muryan mace daga bayansu tana magana, juyo dakai daga Aliyu har gateman din sukayi wata kyakkyawan budurwa ce mai kama da Abdul sosai kana ganinta zaka gane kanwarshi ce tsaye gaban tap din tsakar gidan, wani irin mugun kallo Aliyu yamata dayasa da sauri tajuya zatai backyard cikin kakkausar murya Aliyu yace "come back here" juyowa tayi ahankali kaman wacce kwai yafashe mawa aciki ta tako tazo ta tsaya a gefenshi, gateman din yanuna da hanunshi yace "say sorry" dan turo baki tayi tace "toni Ya Aliyu menayi?" da sauri gateman din yace "tabarshi Alhaji, basaita bani hakuri ba, haka muke wasa da Hajiya ai ni natafi" cikin fushi Aliyu yace "karkaje ko ina" tsayawa yayi dudda baiso ba, Aliyu ya kalli yarinyar yace "kinsan Allah Ihsan idan bakice sorry ba saina kakkaryaki anan sanan zan wuce ciki" idanun Aliyun ta kalla ganin da gaske yake kuma tasan zai iya dukanta dan Ya Aliyu mugu ne kaman ya Abdul yasa ta kalli gateman din tace "sorry" hararanta yayi yace "bacemin daga gani" da gudu tajuya ta shiga falon su, kudi yaciro daga aljihu dabaisan yawansu ba yamikama gateman din da sauri ya karba yace "innalillahi wanan kudi haka Alhaji, me za'ayi dasu?" murmushi yayi yace "gudunmawata, agaishe da Amarya" wani irin ihu gateman yayi hakan yasa Aliyu yajuya yay ciki yanadan murmushi, mamaki yake haryau gateman dinan bai chanza haliba, daga murya gateman yayi yace "Allah baka mata kyakkyawa wacce zata dinga saka farin ciki kaman yanda kasani yau nagode Yallabai" ganin Aliyu yama shige ciki a binshi yasa yajuya yana murna. Da sallama Aliyu ya shiga falon dayasha kayan alatu, wata kyakyawar matace zaune kan dogon kujera tadanyi kama da Dady kaman kanwar shi kokuma cousin dinshi, hanunta rikeda bowl din slice friuts ga Ihsan a gefenta idanunta sunyi jajir tana kumbure kumbure, hararan Ihsan din yayi yana tahowa yace "tashi daga wurin nan" tashi tayi daga kusada matar tai stairs shikuma Aliyu yazauna kusada Momma tareda karban bowl din fruits din hannunta yace "Momma na" tallabe mai keya tayi da hannu hakan yasa yadanyi kara. "aucch Momma zafi fa" hararan shi tayi tace "kamin laifi tunda kadawo bakazo ka gaidani ba sanan daga zuwanka zaka dinga cin zalun autana" yatsine fuska yayi yana kai fruits baki yace "Momma Ihsan batada kunya zan kakkaryata in batai hankali ba wlh" haba Momma tarike tace "ahhh lallai ba shakka to mafashi, kaji ko mafashi nace, daga kai har Abdul din duk wanda yatabamin auta saina rama mata wlh, yayyun banza yayyun hofi masu cin zalun kanin su kawai" dariya yayi sosai yatashi daga kan kujeran yana hawa stairs rikeda bowl din fruits dinshi batare daya tanka ba, Momma data binshi da kallo tace "gaurayen banza aje ayi aure anki sai mugunta, katada wanan mugafalin dabaida aiki sai bacci" dariya yayi yawuce wani daki na karshe a corridor, bude kofar dakin yay ya shiga hango Abdul dayayi yayi daidai akan gado yana bacci ba riga ajikinshi yasa yay kwafa yafito daga dakin ya kwalama Ihsan kira. "Ihsan" da sauri tafito daga dakinta tace "na'am, gani Ya Aliyu" "ehen get me a cold water, very cold one, wanda yafara kankara daga fridge" gyadamai kai tayi tasauka kasa ko 1min ba'ayiba tadawo rikeda ruwan sanyin a gora dayadan soma kankara tabashi tana kallon fuskar shi, bowl din fruit din yamika mata yace "take it to the kitchen" yawuce ya shiga dakin tareda rufo kofa, ahankali yake tafiya har gaban gadon yabude goran ya ijiye marfin ya kwantarda goran ruwan ya tsayayo abayan Abdul dake sharara bacci, ihu Abdul yayi tareda zabura yatashi zaune sabida masifaffen sanyin dayaji, fashewa da dariya Aliyu yayi yana komawa baya ya ijiye ruwan kan center table yana dariya sosai harda rike ciki, saukowa daga kan gadon Abdul yayi yadau ruwan yace "yasin saina rama" da sauri Aliyu yabude kofa yafita biyoshi Abdul yayi, Aliyu ya sauka da gudu ya zauna kusada Momma yace "Momma kinga Abdul ko zai watsamin ruwan sanyi" daidai Abdul ya iso shima ganinshi kusada Momma yasa yakasa karasawa wajen ya tsaya anan gaban stairs Momma dake kallonshi tace "kazo mana ishashe, sai shegen son bacci kaman zakara, ai koda baizo yatasheka ba dani dazo kaga ainihin tashi, nafadamaka bazaka kara bacci mai kyau agidana ba, kai aure kaje gidanka inkaga dama kai baccin kwana uku babu maidamunka kaida matarka ne, amma muddin anan gidanne to ko kagama baccin lafiya da lumana" yanda ya daure fuska yana kallon tijaran da Momma kemai agaban Aliyu yasa Aliyu ya fashe da dariya, keyanshi Momma ta tallabe tace "kaima harda kai ai" gwalo Abdul yamishi yace "Allah kara" turo baki Aliyu yayi kaman zai mata kuka, dan murmushi Momma tace "ga abincin ku chan a dining inkunga dama kuci, gaurayen banza" tashi Aliyu yayi sukayi sama abinsu ko takan abincin basubi ba. [4/5, 8:09 AM] Hijabi_muslimah🙌: _*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_ _IN BETWEEN THE LOVE_ ❤ _Lies another love_❤ _✍🏿M Shakur_ 2⃣9⃣ Zama sukayi akan gado Abdul zai fara masifa da sauri Aliyu yace "please jekai wanka inaso karakani hospital ne" da sauri Abdul yadaura hanunshi kan goshin shi yace "bakada lafiya ne Leo? Mekema ciwo?" girgiza mai kai yayi yace "am fine" "tome zakaje kayi a hospital?" kaman baiso yay magana yace "I wanna go see someone" kallonshi Abdul yayi irin anya Aliyu ne yay maganan nan kuwa dan yasan baida abokanai shi yanama shiga mutane ne dahar yasan wani dazaije dubawa a asibiti, ahankali kaman mai koyan magana yace "s...o..meo..ne? Someone Leo, waye someone kuma?" dan shiru Aliyu yayi yana kallonshi yarasa taya zai fadamai, dariya Abdul yafashe dashi yakoma kan center table yazauna yana daura kafa daya kan daya yana facing dinshi yace "shegen gora, koka fadamin gaskiya kokuma ko nan da chan like chan fa kofar dakina dinan da sunan rakaka wani wuri bazani ba, so tell me d truth" dan yatsine fuska Aliyu yayi yace "please now, kaga nagaji ni nai driving har nan hannuna duk sun sage karakani mana," da sauri Abdul yace "naji to tell me, who is someone, mace ne ko namiji?" hararan shi Aliyu yayi kafin yadauke kai murya chan kasan makoshi yace "mace" huuuuuu! Wani irin ihu Abdul yyi da ko Aliyu saida ya firgita yakoma cikin gado da sauri yace "are you okay me haka" hawowa gadon Abdul yayi da sauri ya dafa cinyar Aliyun yace "who is she? Yaushe kuka hadu Leo?" shiru Aliyu yayi kaman wanda ke tunani saikuma yadan numfasa yace "I just like her, she's just a unique being, her uniqueness yasa zuciyata zabota" kallonshi Abdul yakeyi yanda yake magana a yangance yana fitar da kalaman daidai dan murmushi yayi yace "itace batada lafiya saisa duk ka

Table of Contents

Chapters

78 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});