Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 54

Chapter 54

A Tsakanin Soyayya Book 1 Complete Hausa Novel – Aliyu’s Romantic Journey Begins 1,205 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ta dauko wani babban liver da kidney ta shiga yankasu so take tai liver and kidney source, sosai aiki ya kankama. Wayarta data daura kan saman fridge ne ya shiga kara da sauri ta waigo tana kokarin kashe tap din datake dauraye plate, murmushi tayi taja towel tana goge hannunta tace "hala Ammi nane" karasawa tayi tadau wayan da saurin ta ganin ba Ammi bane number ne yasa ta tsaya tai turus tana kallo tadan turo baki tace "waye wanan? Ashema ba Ammi na bane, ni idan yan lalle ne koma kunzo gidanmu mubar gidan" tai maganan tai picking call din tareda dakaiwa kunnenta, cikin siriruwan muryanta tace "Hello, hello waye?" lumshe ido Aliyu yayi har chan cikin zuciyan shi yaji muryan nata wani irin ajiyan zuciya ya sauke mai kara dahar saida Aneesan taji, faduwa gabanta yayi hakan yasa tai shiru batare data kara cewa komiba, murya chan kasa irin na wanda ke cikeda damuwan nan sosai Aliyu yace "am sorry Aneesa, am sorry for what happened the last time I came, I...i...was...jea..." katse wayan Aneesa tayi tareda kashe ma wayan gabaki daya ta ijiye kan saman fridge din kirjinta na racing har lokacin ba tadawo daidai ba tarasa mesa mutumin nan nada wani irin strong effect akanta ita bata taba ganin namijin da ko magana yake mata saitaji wani iriba, cikeda tsiwa tace "ni me ruwana dakai dazaka wani cemin sorry, koma kazo gidan namu basai inka kara ganinaba, masifaffe kawai, sai yima mutum ihu akai kaman wani uban mutum" tajuya ta cigaba da aikinta tana kwashe Irish din tana zubawa Awani hadadden kula sanan tana hada source kuma. "iyye me daughter na take dafamana haka?" jin muryan Dady yasa tajuyo da sauri yana ta bakin kofan kitchen din a tsaye murmushi tayi tadan dukar dakai tace "ina kwana Abba" shigowa kitchen din Dady yayi yace "ai har sama naje banganki ba nace waya daukemin ya, ashe kina nan, naga kin gyara ko ina tun karfe nawa kika tashi haka?" murmushi tayi tace "tun asuba na tashi Abba shine bayan nagama komi na daura muku breakfast" sosai Dady yaji yanason Aneesa sanan yakara son Ammi dan abinda yaranshi mata basu iyaba kenan yanzun nan ma yaje yatada yaran kowani daki dan su shirya hadda yau lahadi, ji yayi kaman yama kwaso duka yaran yabama Ammi tabasu tarbiya irin wanan databama Aneesa, he wish tuntuni yamasan Ammi ya aureta, karasowa gaban gas din yayi ya shafa kan Aneesan yana kallon abincin yanda yay kyau sosai cikeda murmushi Aneesa tace "na zubama Abba?" murmushi Dady yayi yace "a'a saina dawo daga kaiku makaranta zanci, ai kinkusa gamawa ko?" gyadamai kai tayi da sauri tace "eh nagama miyan, wanan Irish din dake wutane na karshe" gyadakai Dady yayi yace "gud, kina gamawa kije kiyi wanka ki shirya hadda zan kaiku, inkin fito zan kawo miki lunch box daga store saiki zuba naki ciki dan tawas yayi babu lokacin da zaki zauna kici inkinje makaranta sai kici" cikin murna sosai tace "to Abbana, nagode" murmushi shima Dady yayi duk inta cemai Abbana dadi yakeji sosai gatada yawan godiya kaman maman ta, wucewa yayi yafita yay part dinshi, tundaga falo yaga falon yay tsaf tsaf abinda matayen shi basayi Kenn saidai mai aikinshi yamai, murmushi yayi yanabin ko ina da kallo yay bedroom akan dadduma yaga Ammi sanye da hijabi tana karanta wani littafin zikiri nashi, ganin Dady yasa ta rufe ahankali ta ijiye ta mike tsaye tana kallonshi yanda ya jingina da kofa yay folding hannu a kirji yana kallonta, [14/03, 08:14] Aishat Muhammad: Karasowa tayi har gabanshi hanunshi daya rungume takamo takai bayanta kafin ahankali ta shige jikinshi ta rungume shi murya chan kasa tace "ina kwana yallabai na" lumshe ido Dady yayi yana shafa tattausan bayanta murya chan kasa yace "best greeting ever, morning Yallabiyar Yallaban ta" dan dariya dukansu sukayi atare dan yanda Dady yay maganan was damn funny, yana rungume da ita yay wajen wardrobe dinshi yabude wani fitinannen shadda mai ruwan sky blue yaciro nashi da nata dinkaku nata doguwan riga an mata stone work daga sama zuwa kasa murya chan kasa yace "ataimaka a shirya ma yallabai cikin kayan nan" murmushi Ammi tayi batare data ce mai komiba ta cire hijabin ta shiga shiryawa kaman yanda shima Dady ya shiga shiryawa cikin kayan yana kallonta, rigan kaman an aunata juyowa Ammi tayi ganin ita yake kallo yasa ta nuna kanta tace "aunani kayi batare da nasani ba ne Alhaji na" dan dariya Dady yayi yace "dole nasan ya abinda nakeso yake tahonan kiga" yaja hannun Ammi zaunar da ita yayi agaban kujeran madubi ta zauna sanan yakoma wajen wardrobe din wani dan akwatin sarka yadauko yadawo yaboye a bayanshi yace "rufe idanun" kulle ido Ammi tayi ahankali yabude akwatin wani sakan zinare ne mai bala'in kyau yaciro ya sanya mata ahankali Ammi zata bude ido yace "a'a ba yanzu ba" da kunne da awarwaro yasaka mata yana kallonta ta madubi yanda tai kyau ahankali yace "bude idanun" ahankali Ammi tabude idanunta tana kallon kanta amadubi yanda sakan zinaren yamata kyau wani irin dan ihu Ammi tayi ta rufe bakinta tana zaro ido ganin gold sarka ajikinta kafin ta tashi da sauri tafada jikin Dady da gudu tana tsalle kaman wata yarinya tace "is so beautiful, so gorgeous, oh I love it, thank you mijina, abin alfahari na" yanda ta kanannade Dady yasa yaji yana neman zaucewa cikin dishashewan murya yace "zaki hanani kai yara makaranta ko Rukayya kike min wanan abu haka wash Allah" dariya sosai Ammi tayi ta daga shi tareda tashi dashi zaune tace "tubanake" dariya Dady yayi yadau mayafi ya yafamata da kanshi kayan data cire ya linke yasaka a wardrobe dinshi yakama hannunta yace "muje" fitowa sukayi daga dakin sunyi kyau bana wasaba har store compound din ya kaita yana nuna mata komi kafin ya dauko new lunch box na yanmata da kuma goran bottle na yan gayun yaran nan karba Ammi tayi daga hannu shi ta tayashi rikewa sanan suka fito sukai shashinta, daidai lokacin Aneesa ta sauko tana sanye da dogon rigan atampa milk da gold sai wani milk color hijabinta mai hula har kasa ganin Ammi yasa tai wajen Ammi da gudunta Dady na dariya yazauna kan kujera, kallonta Ammi tayi tace "ina zaki kika shirya haka" murmushi tayi tace "Abbana ne yace na shirya zai kaimu hadda" ahankali Ammi ta kalli Dady intace bataji dadi ba tai karya yanda Dady ke nuna ma Aneesa so yasa ta cikin yaran nashi da gaske shine yafi komi yimata dadi a lamarin, batare da Dady ya kalleta ba yana kallon TV yace "bazaki je kibama yarinya na abinci ba sai kinsata latti tawas harta wuce da minti goma" murmushi kawai Ammi tayi cikeda son Dady ta kalli Aneesa tace "muje kitchen din, mekika dafa haka yaketa kamshi?" binsu da kallo Dady yayi harsuka shiga kitchen yanajin yanda suke hira Aneesa na dariya Ammi ma nadan dariya, hada mata abincin Ammi tayi sanan ta hada tea tajuye agoran Ammi sai kallon Aneesan take the joy she's seeing a fuskar Aneesan kadai yasa taji she can withstand koma wace irin kaddara ce inhar daga gidan nan just so wanan happiness dinan bazai gushe

Table of Contents

Chapters

78 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});