Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 34

Chapter 34

A Tsakanin Soyayya Book 1 Complete Hausa Novel – Aliyu’s Romantic Journey Begins 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

tace "Aneesa wankan kike kome naji shiru" "A.....Amm...." muryan Aneesa dataji chan kasa na breaking sosai tana kiranta yasa Ammi ta tura kofan a rude ta shiga, Aneesa datagani kwance a kasan bayi kaman ma tafadi ne jikinta na rawan sanyi sosai duk kumfan sabulu jikinta tana kokarin tashi takasa yasa tama manta bayi take tsabagen rudewa tasaki salati. "innalillahi wa innailaihi raji'un, Aneesa" tai maganan tana tsugunnawa agurguje ta dagota a tsorace bama ta damu da abinda ke jikinta ba tasata ajikinta ganin yanda jikinta ke rawa, tace "Aneesa, ke Aneesa menene eh?" kasa magana Aneesa tayi sai jikinta dake dake masifaffen rawan sanyi idanunta na kukkulewa, ganin haka yasa Ammi tarike ta gam da hannu daya ta sa dayan hanunta a bucket din tadebo ruwan wankan ta watsa mata ajiki ta ijiye tasaba sabulu a soso jikinta na rawa ta shiga wanke mata jikin gabaki daya dan tafadi abayi sai rawa jikinta yake da ace zata saketa da zubewa zata sakeyi akasa, agurguje Ammi ta wanketa ta daura ye jikin nata tana rike da ita tasa dayan hanunta taja zanin ta dake kan kofan bayi ta daura mata ta kwance kallabin kanta tayafa mata tundaga kai har kirji ganin sanyi takeji tarikota gam tabude kofa suka fito, daki ta shiga da ita tawuce dakinta da ita akan gado tazaunar da ita da sauri tai sip ta jawo daya daga cikin dogayen rigunan ta zuwa tayi ta dagata a inda take rawan sanyi tace "sannu kinji, sa rigan" saka mata rigan tayi tacire zanin tayar sanan ta kwantae da ita taja bargon kan gadon tarufa mata, tawuce dakinta da gudu tadauko wani bargo takara mata amma dudda haka rawan sanyin take, fita Ammi tayi da sauri tadauko paracetamol da ruwa ta shigo ta zauna gefenta dagota tayi tace "sannu, sha magani" paracetamol guda biyu ta ballo tasa mata abaki tabata ruwa da sauri ta sha jikinta narawa tasake kwanciya tana nishi. "Aaa...m" da sauri Ammi ta tsugunna tana shafa kanta tace "sannu Aneesa, zazzabin yamma ya sauka akan ki, baccin magriba babu kyau" tashi Ammi tayi tarufo window dakinta ganin sanyin yaki sanan ta zauna tana shafa kanta tana kallonta hawaye nata ruwa a idanunta. Sai wajajen tara sanan taga rawan sanyin yaragu tafara sauke ajiyan zuciya ahankali bacci yasake dauketa jikinta zafi sosai, tagumi Ammi tabuga tana kallonta takai kusan 2min ahaka sanan tawuce tadauro alwala dadduma da hijabin nata tadauko tadawo dakin Aneesan ta shimfida tayi sanan tai shafa'i da wuturi bayan ta idar tabuga uban tagumi tana kallon Aneesan dake sauke ajiyan zuciya ahankali, bataso ta tasheta dan batasan kozata tashi da rawan sanyin ba amma kuma tanaso ta tadata taci abinci, abinci ma na rage rashin lafiya, tafi awa daya zaune tana kallonta kafin dan gyangyadi yay gaba da ita. Not edited. _IN kika karanta baki biyaba Allah ya isa, in kinason karanta littafin nan kiyi subscribing just 300_ Yunkurin amai da Ammi taji yasa tabude ido daga dan baccin daya saceta da sauri tana kiran sunan Allah. "Bismillahi" tajuya tana kallon Aneesa dake kwance yanda tabarta tana yunkurin amai sosai amma babu abinda ke fitowa, kan gadon Ammi tahau ta dagota da sauri zafin jikinta dataji saida yasa Ammi taji tsoro jikinta yafi wuta zafi. "innalillahi, Aneesa, Aneesa menene meke miki ciwo eh? Fadamin" Ammi tai maganan tana shafa fuskarta tana rungumota jikinta, kasa magana tayi sai nishi datake sama sama kaman wacce ke shirin mutuwa bamata gane me Ammi kecewa, yunkurin amai tasake yi hakan yasa Ammi tace "babu komi acikin ki, sannu nahada miki kayan shayi kisha bazan baki tuwoba kinji, nahada miki tea? Kokuma nafita waje nasamo yaro yasiyo miki tsire da fanta?" Ammi ta tambayeta cike da damuwa tana dago kanta, jini taga yana fitowa daga hancinta idanunta na kafewa alamun tasamu. "innalillahi!" Ammi tabuga uban salati mai kama da ihu cikeda tashin hankali, saikuma ta shiga jijjigata tana kiran sunanta. "Aneesa, Fateema" ganin bata motsi yasa Ammi ta shiga kalle kalle cup din ruwan data kawo mata dazu ta dauka ta debi ruwan ta yayyafa mata a fuska tace "tashi tashi kinji bari naje na kira Abdul mai keke yakaimu asibiti" nishi tayi tabude ido ahankali hakan yasa Ammi tai cupping face dinta takirata dukta rude tace "Aneesa na, karki kara rufe ido kinji bari na kira mai keke nakaiki asibiti kinji, ina zuwa" tadau wayan Aneesan data gani agefen gado tana kunna tourch tawuce tafita hartana bugewa da kofa ta kunna haske, sillipas tasaka tawuce zaure tafita tabude kofa tafita daga gidan ganin babu mahaluki kodaya a anguwan su yasa ta kalli wayan Aneesan da sauri sha biyun dare tagani harda minti uku, hannu tadaura kan bakinta ta taushe kukan dake shirin zuwan mata ta kalli cikin gidan nasu yanzu yazatayi? Yarta mara lafiya zata bari ita kadai cikin ciwo da wanan tsakar gidan kokuma she should go ahead ta dandara gidansu Abdul mai keke ne? Hawayen daya zubo mata ta share da sauri tarufo kofar gidan nasu tareda tofa ma kofar gidan bismillah ta shiga haskawa tana tafiya da sauri danba wuta har gidansu Abdul tsayawa tayi tana bubbuga kofar gidan tana kiran su. "maman Abdul, salamu Alaykum, Maman Abdul, Abdul, Abdul" ta shiga kwalama mutanen gidan kira tana ihu, takai kusan minti bayar sanan taji kara kaman an bude kofa daga cikin gidan akace "waye da tsakar daren nan?" muryan ta narawa sosai tace "maman Abdul nice, maman Aneesa ce, dan Allah kutaimaka min Aneesa batada lafiya, Abdul zakidan tasomin yazo yakaimu asibitin General" bude kofa maman Abdul tayi tana haska fuskan Ammi da tocula tace "subhanallahi, aiko Abdul bayanan, kumama ai yadena parking keke agida agarejin su yake parking kinsan wacce yakema aiki da keken tace ya dinga parkin agareji, ya jikin nata" hijabi Ammi tadaura kan fuskarta tana kokarin hana hawayen dake shirin zubowa waje, dafa ta Maman Aisha tayi cikeda tausayinta tace "kiyakuri maman Aneesa ciwon da ba dadi sam wlh, gashi khalili na kyanda dana rakaki bakin titi munsamo abin hawa, babansu kuma kinsan baidawo daga tafiyaba, kiyakuri kinji ki dandara bakin titi kisamo abin hawa Allah yabata lpy, kiyakuri" Maman Abdul tai maganan tana zare hannun Ammi daga fuskarta, gyada mata kai Ammi tayi tajuya da sauri tai hanyar titi tana goge kwalla tana addu'a Allah ya tsare mata Aneesan ta. Abakin titin ta tsaya babu wasu motoci sai tsirarru dasuke gittawa aguje, hawaye Ammi ta shiga share wa uncontrollably sai kallon agogo take yanzu karfe sha biyu da rabi, minti a shirin da bakwai kenan databar Aneesa ita kadai agida, ganin wani mota na zuwa da gudu tasan shima zai iya cewa bazai tsayaba yasa yafada titi tana kuka sosai dataji yazomata kawai dan hankalin ta a mugun tashe yake tana dagama motan hannu alamun motar ta tsaya. Bodyguard din Dady ne dake tuki ya kalli dayan bodyguard din dake gefenshi yace "who is that woman? Get your gun" da sauri Dady dake bayan mota yana daddanna laptop idanunshi sanye da medicated glass jin suna magana get the gun yasa yadago kai, idanunshi ne suka sauka kan matar daya hango kan titi tana kuka sosai tana musu alamun su tsaya, ganin bodyguard din yakara gudu sosai yana shirin ya kwashe

Table of Contents

Chapters

78 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});