Chapter 60
Chapter 60
Aliyu dama kinsan shine" girgizama Mama kai tayi tace "Dady yazo gidanmu wurin baba ranan shine yace nazo naga Aliyu innaumai ahada auren mu, wlh ina ganinshi yau naji ina sonshi sosai kuma wai bayasona" tsaki Mama takaraja tace "Allah na sonki ne yasa yace miki haka, me zakiyi da miji a matsayin Aliyu? Yaron daya rako maza duniya kina ganinshi haka koke a matsayin ki na mace kin fushi karfi, inda nabar Hajar tsaf zata iyamai lilis billahillazi, ki gujema kanki Aliyu ina miki fada, bari kiga neje nadubo Rauda da ciki kota tashi ga kawarki nan zata fadamiki waye Aliyun in kunne yaji ganganjiki ya tsira idan ma bakiji ba mamanki zan kira wlh" tai maganan tana tafiya. Ahankali Aliyu yabude kofar falon Abdul ne kawai a falo yana kallon kwallo su Mami duk suna sama, shigowa yayi yamaida kofan yarufe yakaraso tsakiyan falon da sauri Abdul yatashi zaune yace "kai dama Barkono anan...." alamun Aliyu yamai dayay shiru hakan yasa yay shiru yana murmushi shima murmushi Aliyu yayi yana kallon ko ina nace "ina take?" sama Abdul ya nunamai da hannu yace "sun tafi sama tareda Ihsan" gyadamai kai yayi ya ijiye books din kan center table, alamun tafiya dayaji yasa ya dago kanshi Aneesa ce ke saukowa daga stairs tana sanye dawani baby pink hijab iya guiwa daga gani irin nazaman gidan nanne tasa wata yar shimi da straight skirt mai tsagu ta gefe daya, fuskanta da dan lema lema alamun daga wanka tafito kaya kawai tasa tana tafiya ahankali, tundaga kan yatsun kafafun ta dake dauke da fararen kumba yake kallo gasunan ajere gwanin ban sha'awa yake kallo har zuwa kan side slit din skirt din da idan tana tafiya yake fito da fatar yar kafarta dakeda kwanta cen gashi kaman irin yarannan dabasu san wahala ba wani irin serious murdamai cikin shi yayi dayasa yadauke idanunshi daga kan kafar nata yamaida kan fuskarta sabida wankan datayi har wani extra glow fuskarta yakara kan normal glow dinta karasa saukowa kasan tayi batare data kalli indama sukeba shi dama Abdul kallon match abinshi yake baima kufada itaba hanyar kitchen dinsu tayi ahankali tabude kitchen din ta shiga, kallon stairs Aliyu yayi ganin babu mai zuwa yasa yatashi daga kan kujeran yay kitchen bude kofan yayi ya shiga da sauri Aneesa dake kokarin daukan plate ta juyo suka hada ido maida kofan yayi yarufe ya shigo kitchen din dauke kai tayi daga kallonshi dan wani irin haushin shi takeji tadau kulan da Ammi tace ta zuba mata abincin ta gudun karyay sanyi tadau chokalin dinan abinci zata diba, ahankali ya tsaya agefenta yana kallon abincin datake shirin diba murya chan kasa yace "Aneesah nah!" wani abune taji yatokare mata zuciya sabida yanda yakirata kokarin diban abincin take tamasa a plate takasa hakan yasa ta ijiye kulan cikeda tsiwa ta kallai tace "karka kara cemin Aneesan ka, no karma kakara kiran sunana, na fadamaka baruwan ka dani, kuma ka koma inda kafito kabarmana dakinmu, su baby kakide, mutum kato dashi ana cemai baby, a'a ba baby baibo" ta harari bango tajuya tadau kulan abincin with annoyance kaman shi yamata laifi tana kokarin diba, dudda shi ba ma'abocin yin soyayya bane but from the look all he sees is jealousy a fuskan Aneesa so that means Aneesa na sonshi harma tana kishin shi, wani irin dadin yaji, hannunshi yamika ya fizge kulan abincin datake yin dambe dashi da sauri ta kallai tana kokarin danne feeling of kukan da takeji tamikamai hannunta cikeda masifa tace "kabani kulana" make mata kafada yayi yana karanta sakonni daban daban dake kwance akan fuskanta, cikin fushi tace "zan hadaka da Ammi na, kabani kulana nace" sake make mata kafada yayi ya ijiye kulan kan fridge dake bayanshi kafin ahankali yatako yazo dab da ita yana kallon fuskanta kasa jure kallon dayake mata tayi ta dauke kai ta matsa gefe zata wuce tafita da sauri yatare ta ta kusan fadawa kirkin shi hakan yasa takoma baya da sauri zuciyata na boiling takasa daga ido ta kallai sabida kwalla daya taru a idanunta, cikin wani murya chan kasa mai kama dana lallashi yakira sunanta. "Aneesa" hannu tasa da sauri kanta akasa ta share hawayen dasuka dan zuvo dan bataso yaga hawayenta taki dagokai. Ahankali yace "I love you so much Fateema, you are the only one in my heart, ke kadai zuciyata ke tsananin kauna daga ranan da idanuna suka ganki, I love everything about you, am sorry the way I treated you back then, please kibani dama na nunamiki irin son danake miki, zaki aureni Aneesa?" batare data kalleshi ba tace "Allah kyauta na aureka" lumshe ido yayi dan ya tsani kalman, Murya chan kasa yace "kina sona?" cikeda tsiwa tace "banson ka, mezanyi da masifaffe" ita kanta batasan mesa takemai tsiwa hakaba kuma bahalinta bane kawai tsiwan zuwan mata yake, dan murmushi yayi tareda cizan bottom lips dinshi yana kallonta yace "to mesa kike kishina?" da sauri tadago idanunta dahar sundan chanza kala ta kallai tace "me ruwana dakai dazanyi kishinka? Allah kyauta" murmushi yayi tareda dan juyamata gira yace "okay tunda bakisona bari inkoma wajen maisona nama barta ita kadai nabiyoki" wani irin kashine ya tokare mata makogoro batason ta furta kalaman dasuka cikamata baki amma saida suka fito. "kamafi ruwa guda, su baby kakide, ba baby ba bobo rubbish" ta finciki plate din datadan zuba rice aciki kafin ya fizge kulan tazo zata wuce kaman zata fashe, fashewa yay da dariya ya kama hijabinta da sauri tajuyo ta kallai idanunta sun cika da hawaye sosai tace "ka sakenmin hijabi kona cire maka hijabin na barmaka" dan ware manyan idanunshi yayi cikeda tsokana yace "zaki iya bari naganki da dan singlet din dake jikin ki?" da sauri ta kalli jikinta tayaya yagane singlet tasaka ajiye plate din abincin tai da sauri ta maida hannayenta tacikin hijabin tana turo hijabin gaba dan ya kwanta mata ajiki dayake hijabin robaroba ne karyaga jikinta ta ballamai harara zuciyanta na tafarfasa tace "kawuce kabarmana kitchen dinmu kona hadaka da Ammi na" ta kawad dakai tana kunkuni tace "wanan katoton ne wai baby" murmushi yayi sosai yace "inba ga tsoroba kifada da karfi naji" ko kallonshi batayiba, daukan kulan abincin ta yayi cikeda tsokana yace "bari na kaima babyna abincin nan" da sauri tadago kanta ta kalli kulan daya dauka yana rufe marfin da kyau hawaye ne suka cika idanunta gam tare kofan tayi tareda mikomai hannunta tabude baki zatai magana saiga hawaye sharr sun zubo da sauri tasa hannu tashare hawayen tace "wlh bazaka kaima wata abinci naba, Ammi ta dafa ta ajiyemin, babu wacce zata cim.....mi...." takasa magana sabida yanda bakinta ke rawa saiga wasu zafafan hawayen sharrr da sauri ta daura hannunta akan fuskanta tarufe fuskanta tana kuka mara kara bataso yagani hawaye nabin hannayenta, wani irin rawa zuciyan Aliyu yafara jiyake kaman yakamata ya rungume ta and assure her cewa ita kadai yakeso ita kadai ne azuciyanshi, ahankali ya ijiye kulan akan fridge ya tsugunna ahankali tareda kai guiwanshi kasa yana kallon fuskanta yanda har lokacin take kuka sabida yanda kafadarta ke rawa, hannayenshi yakai ahankali ya daura akan guiwowinta hakan yasa ta janye hannunta daga kan fuskarta daya gama wankewa da hawaye idanunta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78