Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 39

Chapter 39

A Tsakanin Soyayya Book 1 Complete Hausa Novel – Aliyu’s Romantic Journey Begins 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Fateema" cikeda damuwa yace "shikenan nasan yansun nan muna kaiwa kasuwa za'a siye, dazaran an siya zamu taho Sulejan, kome ake ciki kidinga sanar dani, Allah kara sauki, Allah bata lafiya, karki damu zamu iso kimin dare idan na iso za'asan meza ayi" gyadakai Ammi tayi tace "Allah yakawo ku lpy Baffa" ta katse wayan. Abakin asibitin ta sauka rike da katuwar jakan dake hanunta takarasa cikin asibitin da saurinta har dakin su, bude kofar tayi tana kallon manya manyan ledoji data gani kan kujera saikuma kwalin yogurt data gani da cup kan drawer ga Aneesan na bacci peacefully, karasawa ciki tayi bayan ta mayar da kofan tarufe ta ijiye abubuwan datazo dashi tana bude ledojin data gani manya manyan madara da milo ne sai kellogs cornflakes da manya manyan chocolates da biscuits harda minti mai tsinke da wasu abubuwan ma da batasan mesuba, maida ledojin tayi ta ijiye inda suke takai hannu tashafa fuskar Aneesan ahankali, bude ido Aneesan tayi ta daura kan fuskar Ammi da sauri tai yunkurin tashi taimaka mata Ammi tayi tana murmushi tace "oyoyo Aneesa, nadawo" ta rungume ta tana shafa bayanta kafin ta dagota ta jinginar da ita da bangon gado tace "meke miki ciwo yanzu?" murya chan kasa kaman na wacce ke mura ta nuna cikinta tace "cikina Ammi" dan murmushi Ammi tayi tace "sannu kinji hala yunwa ce, bari na kawo roba ki wanke baki na soyomiki kazanki kici , su Baffan kima na hanya zasuzo anjiman nan" Ammi tai maganan tana shiga bayi tadauko wani roba tabude jakan datazo dashi taciro brush da maclean da kanta ta wanke mata bakin tass sanan takoma bayi ta zubar da komi tareda wanko hannu tafito tana sake kallon kayan tazo gaban gadon ta zauna tana dauko kulan abincin da takawo tace "waye yakawo kayan nan Aneesa?" manyan ledojin Aneesa ta kalla kafin ta dauke kai tace "wani ne" shiru Ammi tayi bata kara cewa komiba dan atunanin ta mutumin jiyane yakawo, ta zuba shinkafa a plate tasa mata tsokan soyayyen kajin har guha uku tamika mata ta ijiye kulan akasa tareda daukan spoon takarbi plate din daga hanunta tasa chochalin tadebo abincin zatakai bakinta akai knocking kofar tareda shigowa. Dady ne ya shigo dakin yana sanye da manyan kaya shdda bugagga da hula sai kamshi yake Dr biye dashi murmushi yayi sosai cikin ba'a yana kallon Aneesan dake tanuna shinkafan ahankali yace "lallai y'ata tasami lafiya tunda gashi har baki yabude tanacin abinci" dan murmushi Ammi tayi tana gyara hijabin jikinta Allah yasa bata cireba tace "ina kwana Alhaji" kafin ma ya amsa ta kalli Aneesa dake cin abincin da Ammi tasamata abaki ahankali tace "bazakiyi gaisuwaba, Alhaji shiya taimaka mana jiya yakawoki asibiti" hadiye abincin Aneesa tayi ahankali tadago dara daran idanunta cikin dan karamin muryanta tace "ina kwana Abba" wani irin murmushi Dady yayi yanda Aneesan ta kirashi Abba saiyaji ta masifan burgeshi daga gani anbama yarinyar tarbiya mai kyau zuba yay har gaban gadon yace "lafiya lau y'ata ya jikin?" ahankali ta gyadamai kai. "lafiya lau Abba" murmushi Dady yasake yi yace "gud girl, babu abinda ke ciwo ko? Ko asakeyin allura ne?" da sauri ta girgiza kai tai kaman zatai kuka, dariya Dady yayi hakan yasa Ammi ma tadan murmusa koba komi maison naka abun kaji dadi ne, dariya Dady yayi ya kalli Dr daketa murmushi yace "tokanaji ko likita Ya'ta batason allura karka kuskura kamata" ya kalli Aneesa yace "idan Dr yamiki alluran zan dawo anjima kinfadamin kinji" da sauri ta gyadamai kai tana murmushi sai taji inama shi baban tane tanason Baba sosai tana bala'in son Baba, dan juyawa Dady yayi ya kalli Ammi da kanta ke kasa yace "cigaba da bama y'ata abinci ai baki koshi ba ko?" gyadamai kai tayi tana murmushi, Dady ya juyo ya kalli Ammi datamai kyau sosai dan tasaka wani maroon hijabi yace "kinji ko" dan dago kai Ammi tayi ta kallai hada ido sukayi da sauri tasauke nata tana kokarin debo rice din a spoon tace "angode Alhaji, Allah yasaka da alkairi, Allah yabiya bukatu yasa damu duka a gidan Aljanna" atare daga Dr har Dady sukace Ameen, Dady yasake kallon Aneesa daketa kallonshi tana murmushi yace "zan tafi anjima zan dawo nasake dubaki kinji, ki dinga jin maganan mahaifiyar ki kinji sanan kowani nagani aka baki kisha ki warke sabida kar mahaifiyar ki taitai shiga damuwa kinji" dago kai Ammi tayi ta kalleshi yanda yay maganan yatabata har zuciya, gyadamai kai Aneesa tayi ahankali tace "saika dawo, Allah yabada sa'a Abba" murmushi Dady yayi yanaji kaman yamaida yarinyar yarshi yace "Ameen nagode da Addu'an, muje Dr" Dr ya kalle Ammi yace "idan tagama ci ki danna alarm din gefen gadon nan zanzo" to Ammi ta amsa Dr yabi bayan Dady da sauri har wajen mota yarakashi Dady yamai kyauta mai tsoka sai godiya yake sanan ya shiga motan bodyguard yarufe yakoma gaba yatada motar suka bar asibitin, Dady sai tunani yake dan yaje shashin Aliyu bayanan ina yaje this early morning? Sai kirashi yake baya shiga. _duk shegiyar data fitar min da littafi waje Allah ya isa, duk kuma wacce ta karanta batare data biyaba Allah ya isa, ban kuma yafeba_ [4/5, 8:09 AM] Hijabi_muslimah🙌: _*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_ _IN BETWEEN THE LOVE_ ❤ _Lies another love_❤ _✍🏿M Shakur_ 2⃣7⃣ Saida suka fara tsayawa sukai isha'i sanan suka shiga asibitin, sallama sukayi tareda bude kofan dakin har lokacin Ammi na zaune kan kujera tana kallon Aneesan, zama sukayi abakin gadon sunama Ammi sannu, ahankali Ammi tace "nakawo abinci Alhaji?" girgiza mata kai Baffa yayi yace "bari tukunna yanzu akwai maganan damuke so muyi" dan gyara zama Ammi tayi tace "to Baffa" dan shiru Baffa yayi saikuma yace "Maman Aneesa tsawon wanan shekarun damukai tare tun ina miki kallon matar kanina yanzu kallon kanwata na jini nake miki wacce nakeda iko da ita koba hakaba?" gyadamai kai Ammi tayi tace "hakane Alhaji" gyadakai Baffa yayi cikin nuna gamsuwa da amsan data bayar yace "tsawon wanan shekarun dakika nuna kezaki rike Aneesa bazaki bamu itaba dudda naji haushi amma ban takura mikiba, kikazo kikace ke zaman rainon yarki zakiyi bazakiyi wani aure ba shima ban takura miki ba na barki, ayau nakawo miki wata babbar magana da bazan boye mikiba sonake yau kibani girmana a matsayina na mahaifin yarki sanan waliyinta, kimin biyayya sanan kisani kome nakeso nayi abu mai kyau ne agareki sanan abinda zai ban kwanciyan hankali ne kinajina" gyadamai kai Ammi tayi ahankali gabanta nadan faduwa, dan shiru Baffa yayi yana kallon fuskarta ganin yanda ta natsu duk tabashi hankalin ta tana sauraronshi yasa yace "sonake kiyi aure maman Fateema" da sauri Ammi tadago kai ta kallai cikin wani irin yanayi na damuwa tace "aure Alhaji?" "e, aure maman Fateema nakeso kiyi, aure rufin asirin mace ne, yarinya dake duka dukan ki nawane da zaki ce zaki zaune ahaka ke bazakiyi aureba zaki dinga kula da yarki ne angayamiki hakan zaiyu ne? Banda ma haka amusulunce hakan baida kyau, kin taba tunanin yanayin da zaki shiga duk randa zaki aurar da Fateema kiyi watanni shekaru baki ganta ba kintaba tunanin yanayin da zaki shiga yanda zakiyi coping?" shiru Ammi tayi tana kallonshi takasa magana, dan murmushi Baffa yayi yace "to

Table of Contents

Chapters

78 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});