Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 21

Chapter 21

A Tsakanin Soyayya Book 1 Complete Hausa Novel – Aliyu’s Romantic Journey Begins 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

nace ni bana zuwa home service sunce dan Allah shine nace bari na kawo su wurinki" zama take shirin yi kusada Ammi tace "wuce kije ki karasa sharan ki" gyadamata kai tayi tafice daga dakin Ammi ta dubesu atare dukansu sukace "ina kwana Mama" cike da fara'a Ammi tace "lpy lau sannunku da zuwa" cikeda girmama amaryan tace "dan Allah Mama so muke Aneesa tabimu tamana nida dangina lalle dan Allah Mama, wlh bansan kowaba garin nan, da kyar nagane gidan nan shima kwatance aka mana yau za'a fara event din bikina wanda zan aura yau zai iso daga Chad shine za'a mai tabar damuke cema wushe wushe, dan Allah Mama kitaimaka mana" dan murmushi Ammi tayi tace "Allah ya sanya alheri yabada zaman lafiya" dan murmushi matan tayi tace "Ameen, nagode Mama" murmushi Ammi tayi tace "a gaskiya bana barin Aneesa zuwa home service lalle duk wacce keson lalli har gida ake zuwa tamusu anan agabana, sonake kome takeyi idanuna akanta tarbiyan ya mace saika saka ido sosai sanan ka kula ita kadai gareni, banso nacemiki a'a dan kallo daya namiki nagane you are so stress out, nayaba da hankalin ki ainun, zata biku amma da sharadi zaku dawomin da ita dan Aneesa batasan cikin Abuja ba, rayuwan ta komi anan Sulejan mune kin yarda?" da sauri Amaryan dawani murmushin annuri ya lullube mata fuska jin Ammi ta yarda tace "Mama namiki alkwari zansaka driver gidanmu yadawo da ita da acema lokacin am free dana dawo da ita da kaina kodan karamcin da kikamini amma zansa Baba lado driver yadawo da ita har gida namiki alkwari dama shiya kawomu yanama waje, I promise" murmushi Ammi tayi tace "shikenan karfe nawa za'a gama lallen?" dan tunani amaryan tayi kafin tace "gaskiya bansani ba Mama nida yan uwanmu ne sai kawayena guda biyu da basuma riga sun isoba dan ba'a garin nan sukeba amma dazaran tagama bazan bari ta bata lokaci ba zansa adawo da ita" murmushi Ammi tasake yi tace "shikenan nabaki amanan ta, please kisa mata ido karki bari tabar sight dinki, Aneesa wani zubin batada kai akwai neman fitina, please ku samata ido kunji" atare sukace "to Mama" duk suna murmushi ganin yanda matar keji da yarta, kwalama Aneesan kira Ammi tayi. "Aneesah" shigowa dakin tayi da saurinta duk suka bita da kallo Ammi tace "jeki shirya ki cire kayan nan, fara tattaro kayan lallen dakika siyo a kasuwa jiya kisaka ajaka saikije ki chanza kaya kizo kutafi" washe ma Ammi baki tayi tajuya da sauri tanajin dadi hakanan taji tanaso tabisu itama kodan taga family wayan nan kyawawan yan gayun yan matan kaman ma buzaye ne su, lallen ta tattaro dasu ledoji da sajen ta hada ajakanta da handglove tafito tabama Ammi, jakan Ammi takarba tana kara dubawa to make sure ta kwashi komi dan wani zubin Aneesa ta iya annoying mantuwa dazakaji kaman ka maketa itakuma ta wuce daki dan shiryawa, wani black fited gown tasaka mai kyau dan har jerin stones gareshi ta wuyan sanan tadauko wani ironed baby pink hijabinta mai hula ta zura ta zauna abakin gado tasaka safa akafa kafin ta tashi taje gaban madubin tadau kawalli ta zizara sanan tadau man baki ta shafa dayay kaman ta saka janbaki, ba karamin kyau tayiba wani irin asirtattcen kyau da only the seer kan see karamin jakanta ta rataya tafito falon hakan yasa yan mata suka mike, karasawa tayi gaban Ammi kaman zatai kuka tana kallon fuskarta, kwafa Ammi tayi tadau wayar daga gefenta tamika mata, wani irin murmushi tayi ta fada jikin Ammi tsabagen dadi tace "thank you Ammi na, bazan kara kona abinci ba kinji" gyadamata kai Ammi tayi tana tabe baki tace "common tashi kutafi kidenamin wani dadin baki, saikin dawo, ga jakan lallen" ta mika mata jakan lallen, karba tayi tace "bye bye Ammi na, kimana abinci mai dadi" yanda tai maganan yasa yan matan suka fashe da dariya, Ammi tace "aikin kenan acici kawai" murmushi tayi tareda rufe fuskarta da hijabi tawuce tafita daga dakin yan matan sukace "sai anjima Mama mun gode" "saikun dawo Allah sanya alheri" Ammi ta fada tana daga musu hannu fita sukayi daga dakin Aneesa na gaba har zuwa waje sukai wurin motar, baya amaryan tabude mata tace "shiga" shiga tayi ahankali amaryan ma ta shige, kanwar kuma ta shiga gaba suka rurrufe kofofin motar Baba lado yatada motar yaja tareda bata wuta, duk shiru sukayi sun ciciro manyan wayoyin su suna latse latse hakan yasa Aneesa tai wani murmushi irin nima inada soft touch dinan, bude jakarta tayi taciro tata tafara dannawa saikuma ta dago kai tana kallon abinda amaryan keyi awayanta ganin WhatsApp takeyi yasa takasa hakura dan matsowa kusada ita tayi tamika mata wayanta tace "Anty wai yaya ake WhatsApp dinan kinga wayata jiya Baffa na yakawomin inaso nai WhatsApp amma bansan wazai samin ba" murmushi amaryan tayi ta karbi yar tecno tana kallo tace "aiko wayan nada kyau" wani irin murmushi Aneesa tayi tace "nagode Anty, nima inason wayan wlh bansan haka touching screen keda dadi ba saida Baffa na yakawomin ita, jiyan nan nakusan raba dare ina tabe tabe, da yau nai niyyan naje shagon liti mai saida film din anguwan mu naira hamsin yake karba ya sassaka maka films awaya nace zanje asamin nima naita kallo abina" murmushi amaryan tayi ta kalli fuskan Aneesan hakanan taji yarinyar ta burgeta she's so pure at heart dan wanan wayan ne tecno takema murna haka, Allahu Akbar rayuwa kenan abinda ka raina shi wani kesamu yakasa bacci sabida tsantsan farin ciki, saisa akace kadena duban nasama dakai wanda yafika ni'ima sabida zaka kasance mara godiya ga Allah, by the time ka kalli nakasa dakai wanda kafishi saika godema Allah more and more which of the favors of Allah will she deny?? Alhamdulillah, Allah has been super good, Alhamdulillah, tasake godema Allah, dan ajiyan zuciya ta sauke tareda gyara zama tace "nagama bakida data bazaki iya downloading WhatsApp ba" hannu Aneesa tasa abaki tafito da manya manyan idanunta tace "laaaa sub ko? Kash ancene sub dari biyar dubu daya akeyi, inna koma gida nacema Ammi tabani kudi nasiyo" murmushi amaryan tayi tace "don't worry zan miki yanzu" kafin ma Aneesa tai magana tace "kiramin number ki" number Aneesa ta shiga kira mata ta tura mata katin dubu biyar sanan tamata subscription din 3gb, itadai Aneesa bamatsan meta keyi da wayan ba tadaiga tanata taba wayan, bude mata Gmail tayi screenshot din password din data bude mata dashi mai sauki sanan tamata setting up play store tai downloading WhatsApp tabude mata tsaf ta nuna mata sai dadi Aneesa keji sanan ta tura mata few movies din India datake dashi awaya wanda shine yawanci films dinta, dadi Aneesa kaman zata suma ta kudurta aranta yauko lallen dazata zanama wanga Amarya ko lallen matar sakin duniya ne sai haka. Gamawa tayi tsaf sanan tajuyo zata bata wayan gani tayi sai leka wayan take tasa yatsa abaki tana taunawa tana murmushi tsabagen jin dadi, dariya ne ya kwashe amaryan da karfi hakan yasa akunyace Aneesa ta zare yatsan daga bakinta tana murmushi, mika mata wayan Amarya tayi tace "gashi nan yanzu saisu fara WhatsApp ko ga films nan ma duk ke kadai" cikin murna Aneesa

Table of Contents

Chapters

78 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});