Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 7

Chapter 7

A Tsakanin Soyayya Book 1 Complete Hausa Novel – Aliyu’s Romantic Journey Begins 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ka kadota dan kasha gajiya ga Rauda aku kuturu ce" dariya tafashe dashi taboye fuskarta abayan Aliyu tace "Yayan mu ai banda surutu ko" dan murmushi yayi yace "don't mind Dad ya iya shairi" hararan su Dady yayi yawuce yafita daga dakin, abincin ya kalla yace "go and bring another fork let's eat together" , ware ido tayi saikuma tanunamai cikin ta tace "kar cikina yafashe ni nakoshi, ci karage saina rufe nakai kitchen" daukan fork din yayi yafara ci ahankali, kafeshi da ido tayi ganin yamata bala'in kyau, rabonta dashi kusan 1yr kenan yanzu, ya kara kyau ya kara kiba, yakara cika da zati, gadan gemun daya tara dan kadan dake shining tsabagen gyaran dayakeji, sosai tai nisa akallonshi bama tasan harya gamaba saida ya dungure mata kai sanan ta farga tareda kyalkyace dariya takalli abincin tace "harkagama harya isheka dan wanan zakaci?" ruwa yadauka yakai baki yace "yeah, am ok, dauka kikai kitchen kidawo" dauka tayi tai hanyar kitchen shikuma yacigaba dashan ruwan goran dake hanunshi, dawowa tayi tasake zama kusada shi kaman zata cinyeshi tun tana karama take mugun son Ya Aliyu, shima haka yakeji da ita duk cikin kannenshi itace ta isa tazo bangarenshi ta shiga ko ina tafito, tun tana karama inhar yana nan yana daukanta sufita yasiyo mata abubuwa dayawa sudawo, ita kemai girki ta gyaramai bangaren shi, da ita kadai yake shiri duk fadin gidansu, tashi yayi daga kan kujeran da sauri ta tashi itama, hanunta yakama sukai hanyar bedroom dinshi abakin gado ya zauna ya nuna mata daya daga cikin akwatunan da bodyguard suka shigomai dashi yace "take it to your room" wani irin murmushi tamai ta tashi da sauri tai wurin akwatin, zama tayi a kasa ta kwantar da akwatin tabude, turarukan matane guda hudu adan mini fine bag, sai wani kit da sauri ta dauka ta bude agogo verosky ne da bracelet dinshi, ihu tayi dan tadade tanason abun batada shi, sauran kayan kuma riguna ne masu kyau na mata ciki da singlets, cikin tsananin farin ciki ta dago kai dan tamai godiya taga haryay bacci yana saukar da numfashi ahankali. Murmushi tayi ta kwashi kayan ta mayar cikin akwatin ta hadasu tsaf tarufe ta tashi takaraso gaban gadon daya ke kwance ta tsugunna ta kafamai ido tana tunani, sosai takeson Ya Aliyu sama da duka yan uwanta, su 21 ne yaran Dady, Ya Aliyu shine first born agidan, itama ta girma batasan maman shiba but Anty Hajar tasanta dan tana around 6yrs ta rasu, hawan jini yakasheta, Mama ta taba fadamusu Aliyu yakusan haukacewa da Ummin shi tarasu dan ya shaku da maman shi sosai, bayan Ya Aliyu sai Maman su ta haifi Anty Hajar, sai ta haifi har maza biyu amma duk suka rasu bayan sunzo duniya, sai ita, sai kaninta dukansu mata guda 6, amaryan Dady yaranta mata guda uku, sai ta tsakiyar itama yaranta mata guda Takwas, bawasu manya bane dayake gasan haihuwa ake agidan, daga ita sai Anty Hajar ne kawai manya duk sauran yaran yarane basu wani tasaba. Deep down tausayi sosai Ya Aliyu kebata bana wasaba gidan nan kowa ya tsaneshi harda Maman su itacema oga, she's sure ayanda Mama ta tsaneshi inda zata sami hanyar kasheshi zata iyayi, ita tarasa meyay musu meya tsaya musu? Maiya kare musu wanan mugun tsana haka daga ina? Gashi baima dawani magana, bayama kulasu sabida yanda ko kaunar ganinshi basayi duk sun rabashi da kaninshi, itama da karfi da yaji tanunama Mama itafa saita kula Yayan su koda ba mahaifiya daya ta haifesu ba ubansu daya ai, kuma jini guda ke yawo ajikinsu, Ya Aliyu is just somehow that she can not even define, he's very cool saiyaga daman kulaka zai kulaka, sanan yanada fushi yanada bakar zuciya but he's always keeping calm baimaso yana fushi, gashi baida kwari komi ahankali yakeyi sanan shi mata basama gabanshi, shi kawai gashi nanne soo somehow, sa'oinninshi maza by now suna cikin kogin soyayya koma sunyi aure sun ijiye iyali shiko batamaga alamun sha'awan aure tattare dashiba ko halinsu Mama ne dayagani yasa yadauka duk haka mata keda bakin hali ya tsani aure oho but she just wish, hope and pray Ya Aliyu will meet the love of his life soon and experience that feeling of knowing someone out there is dying for you, is crazy for you, and can do anything for, love feeling is just the best ne, tarasa mesa duka matan Dady dukansu ukun bazasu soshi and hold him like a Son ba why, yanzu kenan duk yaron da mahaifiyar shi zata mutu tabarshi haka zaiyi rayuwa kowa na kyaranshi? This isn't right at all. Tashi tayi ahankali jikinta duk yay sanyi taja jakanta tareda kashemai wutan dakin tafita ta rufemai kofan falo tawuce part dinsu, ahankali tabude kofar su gudun kar Mama taji ta maida kofar tarufe sanan tadaga akwatin dan karyay kara tai dakinsu, bamata kunna wutaba ta lallaba ta ijiye akwatin gefen gadonta ahankali kaman munafuka, fincikota dataji anyi saida tadan saki gajeren fitsari kunna wutan dakin akayi taga Yayarta Hajara ne tsaye jikin kofa sai maman su data mugun daure fuska tana rike da ita, sosai jikinta yafara rawa hakan yasa tace "M...Mama menayi?" hannu Mama tasa ta dauke ta da lafiyayyen mari ihu tabude baki zatayi Maman su tace "wlh, wlh kikamin ihu ubanki yaji ya shigo dakin nan saina miki abinda bantaba mikiba tunda na haifoki duniya" gyada mata kai tayi tsabagen rudewa tasa hannu takama bakinta tana kuka sosai mara kara, cikin mugun fushi Maman su tace "wato dan ubanki tunda Aliyu yabar garin nan nahuta yanzu yadawo kin fara, Rauda ni, ni, ni nan uwarki karimatu in tsugunna in haifoki kifito tanan Rauda" ta daura hannu gaban zanin jikinta tace "nasha azaban nakuda na kwana biyar, bayana kam har tofin yaasin akamini tsabagen yanda kika shirya karyashi kafin ki fito, sanan dakika tashi fitowan kika fito ta kafa nasha bakar azaba nice yau Rauda kike nunamin wani kasurgumin katon banzan namiji, mai kama da basamuden chan yafi ni ni mahaifiyarki, iyye Rauda? Nasaki ki daukomin zanin gado, Rauda ni zaki watsarma da wankakken zanin gadona fari kal akasa sabida kinga Aliyu, dan ubanki ciki daya kuka fito da Aliyun?" shiru Rauda tayi bata bata amsaba sai uban hawaye dake fitowa daga idanunta, cikin tsananin fushi Mama takara kamo gaban rigan ta bakinta na kumfa tace "kibani amsa, ciki daya kuka fito da Aliyu?" girgiza mata kai tayi cikin kuka tace "Yayan mune Mama" wani mahaukacin mari Mama takara sharara mata tace "dan ubanki menasha taraku nake fadamuku? Aliyu ba dan uwanku bane, babu ruwan ku dashi yanda baida uwa hakama baidaku, kuba yan uwanshi bane, haka zai karake rayuwanshi baisan dadi da soyayyan dan uwaba, ku dauka ko jini vaku hada dashi ba, yaron da ubanku ya fifitashi kan kowa na gidan nan uban me za'ayi dashi eh?" cikin kuka sosai Rauda tace "amma Mama shi aka fara haifa a gidan nan, kafin dukanmu, kuma Dady na nuna yafi sonshi ne sabida duk kunki bama marayan yaron soyayyar mahaifiya dukkun tsaneshi, maiya muku? Bai taba zaginki ba, bai taba miki rashin kunya ba, inya gaisheki baki amsawa bama kya kallonshi saisama yadena, duk kun rabashi da kowa, Anty

Table of Contents

Chapters

78 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});