Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 18

Chapter 18

A Tsakanin Soyayya Book 1 Complete Hausa Novel – Aliyu’s Romantic Journey Begins 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

_Suleja_ Motar datagani Honda pake kofar gidansu yasa taji gabanta yafadi ahankali tafito daga keke napep din taciro kudinshi naira dari tamikamai karban kudinshi yayi yaja keken yay gaba, ahankali take daga kafafun ta tana kara kakkabe hijabin dayay butu butu da kasa ta shiga gidan da sallaman ta, ahankali tana kallon tsakar gidansu da aka shimfida babban tabarma wasu maza magidanta guda biyu zaune kan tabarman duk sun kafeta da ido saikuma Ammi datagani zaune kan yar kujeran tsakar gidan abakin kofar dakinsu idanunta sundanyi ja sosai kaman wacce taci kuka tagodema Allah, ganin yanda Aneesan ta tsaya chak ita bata gaidasuba ita bata karaso cikin gidaba yasa Ammi tace "bazaki shigo ki gaida Baffofin kiba kin tsayawa mutane aka kina kallon mu kaman kinga dodanni" dan murmushi tayi akunyace dan yanda taga idanun Ammi yasa ta manta da kowama dake tsakar gida kanta akasa ta shigo har cikin tsakar gidan gaban tabarman su ta tsugunna tana wasa da bakin hijabin ta ahankali tace "ina kwana Baffa, ina kwana Kawu" mutanen duk kamaninsu daya saidai kana ganinsu zaka gane wa da kani ne daya yafi daya manyanta babban cikin ne wanda suke kira da Baffa wanda tunda ya shigo yake kallonta ahankali yadaura hanunshi saman kanta yana kallon fuskanta yace "Fatima, zauna dakyau" yay maganan yana kallon yanda ta tsugunna sabida karta gaji, gyara zama tayi ta zauna kan tabarman inda yake nunamata da kyau tana gyaggyara hijabi ganin ta natsu yasa yace "tuntuni mukazo mahaifiyar ki tacemana kinje kasuwa mun tsaya mugakine kafin mukoma kadunan, ya kike Fatima?" kanta akasa tace "Alhamdulillah Baffa ina lafiya" kunyanshi takeji sosai bana wasaba, murmushi yayi ya gyadamata kai yace "Allah yamiki albarka kinji ko," gyadamai kai tayi tace "Ameen Baffa, nagode" gyadamata kai yayi shima yace "ki kula da kanki kinji, ki tsare mutuncin ki, ga mahaifiyar ki nan kidinga mata biyayya kinji, in sha Allah zan kokarta nadinga zuwa akai akai ina dubaki ko dayake mun riga mun gama wanan maganar da mahaifiyar ki" dayan magidancin ya kalla yace "mikomin wanan jakan Sani" yar babban jakan dake kusa dashi magidancin yadauka yamikamai karban jakan yayi yabude ciki kwalin waya na Tecno pop2 yaciro yamika mata yace "ga wayanan nakawo miki kome kike bukata ki kirani kinfadamin kinji koda bandashi duk randa Allah ya horemin zanyi miki, sanan ga wanan" yasaka hannu a aljihun riganshi yaciro kudi yan dubu daidai har na dubu bakwai ya mikamata, ahankali tasa hannu ta karba yace "naji amfara registration din jamb kije kibiya muga ya Allah zaiyi kafin nan dawani tsayayye yafito mu aurar dake, kije kibiya cikin satinan dan naji ance idan kabiya dawuri ana turaka center a garinku ko Sani?" gyadamai kanin nashi yayi yace "eh hakane Yaya" kallonta yayi yace "masha Allah kije kiyi kinji, gakuma wanan" ya kara mata dubu uku yace "ki ajiye kidinga kashewa ahankali ahankali kinji Fateema, Allah yamika albarka, Allah yamiki albarka, dawata matsalan?" girgizamai kai tayi ahankali tace "babu Baffa, nagode Allah saka da alkahairi, Allah amfana" murmushi yayi sosai yace "bakomi kidena min godiya Fatima ni mahaifinkine so kidenamin godiya kinji, zamu tafi yanzu kome kikeso ki kirani kifadamin ga wayanki nan" ya kalli Sani yace "tashi mutafi Sani" mikewa duk sukayi Sani yasa hannu a aljihu, dubu biyu yaciro yamikama Aneesan yace "ga wanan ki kara kan wanda Yaya yabaki, ki kula da kanki kinji" akunyace ta karba tace "Allah amfana Kawu" wajen Ammi data zauna tana kallon su tayi tace "Ammi kinga abinda su Baffa suka kawomin" murmushi Ammi tace "akashe lafiya, jeki ajiye a daki kizo kirakasu" daki ta shiga Ammi ta dubesu kaman yanda suke kallonta suma tace "angode Alhaji, kuma kuyakuri idan abinda nace yamuku zafi yabata muku rai, Allah ya kiyaye hanya sanan agaida mutanen gida, mungode" tana maganan tabude kofa ta shiga daki, girgiza kai Baffan yayi yadubi Sani yace "muje Sani" sukai zaure, a falo Aneesa tahadu da Ammi tace "Ammi muje rakiyan ganinan na ijiye kayan a dakina" girgiza matakai Ammi tayi tace "yi maza kidawo ni ina nan" tsayawa tayi turus tana kallon Ammi ganin duk tayi wani iri, murmushin yake Ammi tamata tace "yi sauri mana kin tsaya kina kallona suna jiranki awaje" fita daga dakin tayi tai waje duk suna tsaye jikin mota murmushi tamusu takaraso tace "Allah ya kiyaye hanya, Allah yakaiku lafiya Baffa agaida kowa" gyadamata kai sukayi atare sukace Ameen, Baffa yace "wuce kikoma cikin gida, Allah miki albarka" Ameen tace tawuce ciki kaman yanda ya umurceta yayinda suka shige mota Sani ke tuki sukabar anguwan. Da sauri ta shiga falonsu hijabin jikinta ta zare tawurga kan kofa tai wajen Ammin ta, zama tayi kusada ita tana kallon fuskarta tace "Ammi na menene? Maiya sami idanunki sukai ja? Kuka kikayi? Mesu Baffa suka gayamiki daya bata miki rai har kikai kuka?" tai maganan cikeda damuwa sosai, yatsa Ammi tasa ta dungure mata kai tareda kakalo murmushi tace "wayace miki kuka nayi eh uwar tsegumi? Toba kukanai ba kwaro ya shiganmin ido dazu saisa idanuna sukai ja, tashi ki dauko sabuwar wayar taki kisaka chaji kinga sun kawo wuta" murmushi tayi dudda tasan da abinda Ammi ke boyemata amma saita share taje ta dauko kwalin tazauna kusada ita tana bude wayan daga kwalin wayan tazauna gefen Ammi tana bude kwalin, fuskarta Ammi ta kalla idanunta suka sauka akan gefen bakinta daya kumbura, hannu ta takai ta taba wurin cikeda mamaki tace "maiya sameki anan Aneesa?" dan zaro ido tayi takai hanunta ta taba wurin sai a lokacin taji zafi shiru tayi takasa magana hakan yasa Ammi tace "maiya sameki anan? Fada kikayi a kasuwa? Eh ina magana kinyi shiru" dan matsawa tayi gefe kadan tana turo baki dan tasan bakaramin aikin Ammi ba ta maka mata duka tace "Ammi wata yarinya fa na taimaka" "kika taimaka wani irin taimako eh spider girl?" Ammi tai magamam cikeda tuhuma, shiru tayi tana zazzaro dara daran manyan idanuwanta dan lashe pink lips dinta dataji are so dry tayi tace "Ammi wani nefa keta janta akasa ya barka mata riga shine na shigan mata daga karshe ma yayanta yazo yako rama mata sanan nadawo" gyadakai Ammi tayi tanamata wani irin shegen kallo tace "aahh ba shakka Spider girl" kasa daurewa Aneesan tayi dudda fada Ammi take mata saida tai dariya sabida yanda Ammi tafadi spider girl din, tallabe mata keya Ammi tayi tace "nikike ma dariya inai miki magana" tabe fuska tayi kaman zatai kuka tana kallon Ammin, Ammi tace "wato saisa kika dade kenan ashe ko daman, Aneesa" Ammi ta kirata cikin kakkausar murya tace "banhanaki shiga shara ba shanu ba eh? Aneesa ina gujemiki matsala bakiji, baki fahimta, bakiji, wai yaya zanyi dakene iyye? Maisa bakijin magana na?" kaman zatai kuka tace "yakuri Ammi bazan karaba to" "yimin shiru anan haka kullun kike cewa, Aneesa karkije kajawo mana bala'i wataran, Allah duk randa kika kara Baffan ki zan kira nafadi mai abinda kikeyi dama sunce ban baki tarbiya mai kyau kinga saisuga balaifina bane" kallon Ammi take tunda tafara masifan hakan yasa tace "Ammi haka sukace wai baki bani tarbiya da kyau?" hararanta tayi tace "wuce kije kisaka waya achaji malama kizo kidaura abincin rana" gyadamata kai tayi ta tashi daga kan kujeran

Table of Contents

Chapters

78 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});