Chapter 47
Chapter 47
dake biyeda ita tafito itama, Ihsan ta kalla tace "jeki kiramin su suzo suci abinci" sama Ihsan tayi bata wani jimaba ta sauko tana dariya tace "Momma duk sunyi bacci ko takalma basu cireba" girgiza kai Momma tayi tace "Aliyu da Abdul ai saidai Allah ya shirya domin kam duk kanwar ja ce" ta gyara zama tana kokarin daukan remote dake kan dayan kujeran tace "jekici abincin ki Ihsan". Sai wuraren shadaya sanan Aneesa tabaro wurin Baffa dasuka wuce dakin zaure dasuke kwana itakuma tadawo daki, kulle kofa tayi dan tasan Ammi ta riga ta kwanta, dakin Ammi ta wuce straight Ammi na zaune kan gado tana linke kayan data cire, kallo daya tama Aneesan ta dauke kai, murmushi Aneesa tayi takarasa kan gadon ta zauna kusada Ammin, kayan ta karba takarasa linkewa ta tashi tai wajen sip din Ammi, sip din tabude tana kokarin maida kayan ciki tace "Ammi kinason Abban? Naga su Baffa sunce jibi ne bikin" tana maganan tana jera kayan a sip, jin Ammi ba tace komiba yasa ta juyo ta kalleta, hada ido sukayi da Ammi dake kallonta, washe baki tayi takaraso ta zauna kusada Ammi tareda daura hanunta kan cinyar Ammi tace "eh Ammi, bakice komiba" dan murmushi Ammi tayi tace "kina sonshi to Aneesa, ba dole na yarda ba" washe baki tasake yi tace "nagode Ammi na, Ammi kinga ko nizan miki lallen biki, in miki kwalliya dakomi ko Ammi" tabe baki Ammi tayi tace "nine zanyi wani lalle saikace bikin yar yarinya" kaman Aneesa zatai kuka tace "wlh nisaina miki, Ammi na mai shegen kyau kinji" tabe baki Ammi tayi tace "naji to, Allah kaimu da rai da lafiya" Ameen Aneesa tace haka tacika Ammi da surutu har Ammi tagaji tace mata tamata shiru kota maketa, gabaki daya tama manta da batun wani Aliyu daya bata mata rai dazu, bamata so ta tuna ko kadan, mamanta is getting married so she's super excited. _masu iya magana sunce rana bata karya, saidai uwar diya taji........_ Yau dubannin jama'a wayanda suka halarci sallan jumma'a a babban central mosque in Suleja, wanda ya kunshi mutane da dama daga ciki harda abokanen Dady na wajen aiki da kasuwance, Aliyu, Abdul, dakuma Baban Abdul (mijin Momma), shi kanshi Dady dayaci wata fitinannan shadda wacce taci sunanta shadda, dakuma su Baffa da fuskokin su ke dauke da annuri, limami ya daura aure tsakanin Alhaji Muhammad Ibrahim da kuma Rukayya Hamisu, inda su Baffa da mutane da dama suka shaida sai murna ake ana hayaniya, sosai Aliyu ke murmushi he's trying his best yaboye damuwan shi dan baiso Dady yagane, today is a happy day for Dady baiso yaga any sign of something a tattare dashi ya shiga damuwa, yanada matsala daya addabi zuciyan shi ainun rabonshi da Aneesa tun ranan nan, yakira layin ta taki dagawa daga bayama kashe wayan tayi gabaki daya, gajiya ma Yayi da amsa gaisuwan mutane ganin kanshi yafara masifan ciwo ya kalli Abdul dake kusada shi shima yana sanye cikin shadda fara kaman tashi yace "am going home" da sauri Abdul yace "me haka? Kasan Dady zai nemeka ko" yatsine fuska yayi yace "stay kai, am having headache, inya tambayeni kacemai naje gida" yana yin maganan yay tafiya yana kallon Dady dake washe baki kaman anmai kyautan makka yana gaisawa da mutane, yawuce ya shiga mota yaja zuwa chan Abuja dan yasan koyaje gidan momma dake nan Suleja dakwai hayaniya kuma baison hayaniya ko kadan, yana danna mota cikin gidan Maman su Rauda na fitowa daga motar ta datai parking, wani natsiyacin kallo tama motarshi ko damuwa baiyi a yabude yafito yay side dinshi batare dayama inda take second look ba ballema yasan wats she's up to, kwafa Maman su Rauda tayi tace "inhar ban koyama Aliyu hankali ba aduniyan nan basunana Kareema ba wanan alkawari ne namaka, wlh kuwa" tai kwafa tawuce dakinta. Bude part dinshi yayi ya shiga yaji ko ina na kamshin turaren wuta lumshe ido yayi yabude dan yana mugun son kamshi kuma yasan aikin Rauda ne hakan yamaida kofar yarufe yya hanyar bedroom dinshi, kaya yarage ya shiga wanka koyaji dadin jikinshi, baiwani jimaba yafito yana yatsine fuska sanye da bathrobe yafada kan gado tareda daukan wayanshi yana kallon number Aneesa yanaso yakira but yasan koya kira bazata dauka ba, ahankali bacci yay awon gaba dashi. _Bangaren su Ammi, Suleja_ Yau jumma'a tun kafin a daura auren wuraren karfe takwas nasafe Momma da kawayenta suka kawo akwati guda goma inda saiti bakwai na Ammi ne dake cike da hadaddun kaya da an dinka wasu wasu kuma ba'a dinka ba saiti uku kuma na Aneesa ne da aka cikamata da kaya na yamma ta harda dogunayen riga Aneesa harda kuka, few kawayen Ammi na anguwan ne suka tarbesu itakuma Ammi taki fitowa har suka tafi anata guda daga baya aka daura hadadden abinci dan tun jiya Dady ya turo da motan kawo abinci Aneesa tama Ammi hadadden lalle bana wasaba ta shirya Ammi cikin wani lace mai kyau sky blue da fari ta rungume Ammi yafi sau dari sabida yanda Ammi tai kyau sanan takawo wani farin babban mayafi ta yafama Ammi, Ammi sai amsan gaisuwa take tana murmushi ka ganta itada Aneesa zaka zaci y'a da kanwa ne, Aneesa itama wani farin lace tasaka mai ratsin pink shima dadin ne yaaaimata takai aka dinka mata tai kyau telan dudda bai aunata ba amma chip chip yamata yafito da shape dinta sosai bana wasaba sai murna take ko ita ke aure albarka. Wajajen karfe uku anguwan ya cika da maza da mawaka ana wake Dady, Baffa ne ya shigo ya leko ya kira Aneesa dake tsakar gida tana nan tai chan tama kasa zama waje daya da gudu tai wajen Baffa a zaure, baki Baffa yarike yace "wai wai wai, masha Allahu, ashe haka yar tawa keda kyau aida kyar naganeki wanan kyau haka" wani irin cute smile tayi cike da zumudi tace "Baffa an daura? Yanzu Abba yadawo mijin Ammi na?" tafada cikeda wani irin murna gyadamata kai Baffa yayi yace "kinsan mezakimin yanzu anjima zamuyi hira, yanzu jeki kawomin maman ki nan dakin mu ta zauna kifito, sabon baban ki keson yimata magana" da sauri Aneesa tace to Baffa tajuya da sauri takoma cikin gida Baffa yakoma waje ko minti daya ba'a yiba shida Dady suka shigo zauren tareda Baffa dakin su Baffa yabude ma Dady yace "shiga ka zauna na aika Aneesa takirata, cikin gidan mata sun cika abinka da gidan sha'ani" shiga ciki Dady yayi ya zauna yana murmushi yanadan girgiza kafa yawani irin kosa yaga Ammi ta shigo. Har gaban kofar dakin Aneesa takawo Ammi dake wani irin jin kunya sosai sanan tawuce takoma cikin gida da gudu, bin bayanta da kallo Ammi tayi tana sauke ajiyan zuciya kafin ahankali tasa hannu tabude kofar dakin ta shiga ciki ahankali da sallama, mikewa tsaye Dady yayi yana yana gyara babban riganshi dayasha lafiyayyen aiki yana kallon Ammi, kasa jure kallon daya ke mata Ammi tayi hakan yasa ta saukar da nata kan kasa, ahankali tashigo tana taku daidai anatse har gabanshi kafin ta tsugunna ahankali zata gaidashi da sauri yawani irin riketa batare daya bari ta tsugunna ba yadago ta tashi tsaye tayi tana kallon
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78