Chapter 40
Chapter 40
kingani, gwara kiyi aure duk randa zatai nata auren kina gidan mijinki karkashin mijinki akwai wanda zai dinga debe miki kewa kinajina" gyadamai kai Ammi tayi ahankali, murmushi yasake yi ganin batamai gardama ba, ahankali yakira sunanta "Maman Fateema" ahankali tace "na'am Alhaji" anatse Baffa yace "Alhaji Muhammad Ibrahim wanan mutumin daya taimaka miki yakawo Aneesa asibiti dazu yasame mu da wata magana da tamin dadi ainun, ya nunamin shi daga ranan daya fara ganinki yaji yana matukar sonki ainun" wani irin murmushi Aneesa da tun dazu dasuka fara magana yatashi tayi cikeda jin dadi, da sauri Ammi ta kalli Baffa, gyada mata kai Baffa yayi yace "inaso kiyi tunani sosai bazan takura miki ba, gobe nakeso kibani amsa kuma ko kadan banso adau lokacin dazaran an sallami Aneesa za'a daura auren dan zanzo mu daura auren kafin mubar garin nan, Inaso ki natsu kiduba lamarin da kyau, kuma namiki alkwari gobe ni nan da Na Sani zamu fantsama garin nan muje muyi binciken halinshi inmun dawo zamu fadamiki maimuka gano sanan saimuji amsan ki saimu kirashi, inamiki kwadayin aure sosai, so kiyi tunani kinji karki takura ma kanki, Allah ya sadamu da alkhairan shi" gyadamai kai Ammi tayi ahankali tace "Ameen" murmushi yayi yace "to bamu abincin muci mutafi" plate tadauka ta zuba musu tavasu sunaci ana hira sama sama saida suka gama sanan suka mata sallama suka tafi. Tagumi Ammi tabuga tana tunani sosai sai hango fuskan Dady take, dan motsin da Aneesa tayi yasa tadago kanta ta kalleta ganin idanunta abude yasa ta tashi da sauri tareda daura hanunta kan goshin Aneesan tana murmushi tace "Aneesa na kin tashi zakiyi fitsari nakaiki bayi?" girgixa ma Ammi kai tayi tana murmushi, murya chan kasa tana lum lumshe ido tace "Ammi ki yarda ki aureshi ni inason shi wlh, inason Abba Ammi, please ki yarda kinji" Aneesa tai maganan tana murmushi sosai baki Ammi tabude cikeda mamaki tana kallonta tace "ke, so dama idanunki biyu kinajin duk abinda muke cewa ko" gyadama Ammi kai tayi tana murmushi sosai tarike hanun Ammi tace "Ammi please kinji ki yarda, dan Allah" hararanta Ammi tayi tace "Common kimin shiru anan, zakiyi fitsarin ko bazakiyi ba" turo baki tayi tace "ni banaji, kuma inyazo gobe sainace mai Ammi na ta yarda su Baffa su daura auren" haba Ammi tarike tana kallon Aneesan cikeda mamaki tace "kaman rashin lafiyan nan yasamiki rashin jine ko Aneesa wanan magana haka" dan murmushi Aneesa tayi tace "inda ni namiji ne dani zan badake Ammi" daka mata duka kadan Ammi tayi acinya hakan yasa tafashe da dariya sosai Aneesan tana safe kanta dake mata ciwo Ammi tace "ahh lallai lafiya tasamu, zanci gadanku ne" rungume cikin Ammi tayi tace "please Ammi na ki yarda kinji for me Ammi na, ni inason shi" shiru Ammi tayi tana sauraron ta kafin tadan sauke ajiyan zuciya tace "to shikenan, zanyi tunani in sha Allah" matseta Aneesa tayi tace "yauwa Ammi na, my Ammi najin magana ta, my Ammi is a good girl" dariya sosai Ammi tayi tana shafa kanta tace "Allah shirya" haka suka dinga hira kasa kasa harta sake komawa bacci. [4/5, 8:09 AM] Hijabi_muslimah🙌: _*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_ _IN BETWEEN THE LOVE_ ❤ _Lies another love_❤ _✍🏿M Shakur_ 2️⃣8️⃣ Tunda asuba ta tashi ganin tanada dan karfi yasa Ammi ta kaita bayi tamata brush tareda dauraye mata jiki da towel da ruwan zafi ta taimaka mata ta chanza kaya hakan yasa taji dadin jikinta sosai suka fito, a zaune tai salla sanan takoma kan gado Ammi tahada mata hot tea mai kauri tabata tasha dan yamata dadi sosai nan da nan tafara zufa dan sauki yasoma samuwa kafin daga bisanni tai bacci. Wuraren biyun rana su Baffa suka iso kowannen su dauke da murmushi akan fuskar shi suka zazzauna nan suka shiga bama Ammi labarin binciken dasuka yo, Dady nada kirki ainun ga taimakon musulmai, sanan baida zalunci, matayen shi duka suna tare bai taba sakin mata kodaya ba, gidan shi ba'ajin kansu awaje atakaice dai basuji any bad halin Dady ba daidai da kwara daya, hakan yasa Baffa ya gyara zama yace "todai kinji komi, me kikace dan kiranmu yake jira, eh maman Fateema me kikace?" dan ajiyan zuciya Ammi tasauke kafin ahankali tajuyar da kanta ta kalli Aneesa dake bacci tai shiru kafin tafara zancen zuci. "hukuncin dazan yanke yanzu sabida kene Fateema na, I know, ni karan kaina nasan yanda zuciyar ki ta kwadaitu, tana neman wanda kowani safiyar Allah zaki kalla ki kirashi da Baba ko Abba ina kwana, kema ki sami wanda zaki kalla ki kira da mahaifi, bakomi zaisa na yarda da auren nan ba saidan inga farin ciki akan fuskarki, farin ciki wanda ni mahaifiyarki ce tasanyaki ciki, nothing beat seeing your child happy and as a mother I have to make you happy, zan yarda da auren nan for you Aneesa na dan naga yanda kikeson Alhajin nan banda hakaba ma ta sanadinki muka hadu" ajiyan zuciya ta sauke ta juyo da kanta ahankali ta kalli su Baffa dasuke jiran me zatace gyadamusu kai tayi ahankali tace "na yarda Baffa" wani iri washe baki da sukayi zaka dauka an musu bushara da aljanna ne Baffa yace "masha Allah Masha Allah, naji dadi, ina kuma rokon Allah daya sanya albarka awanan lamarin, ya kade fitina, yanzu Na sani tashi muje musanar dashi me akeciki kaga nasan zaiyi farin ciki sosai" cikin jin Dady suka tashi suka fita, dan murmushi Ammi tayi harga Allah tunda Aneesa ta nuna tanason Alhajin sai itama taji tana sonshi sosai bana wasaba kuma zata so ta kasance tareda shi har abada, dan dugo dakai tayi ta sumbaci goshin Aneesan dake bacci tana murmushi tanata kallonta ahankali tace "Allah yabaki miji nagari wanda zai soki sanan ya kulanmin dake aduniyan nan" karan dataji na shigowan message a wayanta ne yasa ta mike tsaye ta dau Jakarta dake kan saman drawer, wata savuwar number ce tatura mata sako, zama tayi abakin gadon tabude. _Assalamu Alaykum, Rukayyah_ _Hakika yau kin sani cikin tsananin farin cikin dana dade ban shiga irinshi ba, naji amsan ki daga bakin Alhaji, Masha Allah, Alhamdulillahi Rabbil Alameen, alkawari daya zan miki shine bazaki taba samuna dacin amana ba, zan rikeki amana, Aneesa tadawo y'ata zan riketa amana sanan zan bata tarbiya amatsayina na mahaifi agareta, karkiji komi zan kasance miji nagari da zaki dinga alfahari dani akodayaushe. Ina kaunar ki sosai Rukkayah Sainazo_ _Alhaji Muhammad_ Dan murmushi Ammi tayi ta ijiye wayan tareda sauke ajiyan zuciya tana tunani wai yanzu itane zatai aure? Abinda bata taba kawowa zai faruba, Allah kenan dazaran yace lokaci yayi to yayin nefa, Allah sa mudace! Ameen. Da sallama Dady ya shiga part din Aliyu, jin shiru bai amsaba TV ne kawai ke aiki a falon yasa yay bedroom dinshi, ahankali yabude kofan babu kowa a bedroom din sai kamshin da dakin yakeyi, fitowa yayi yana kwalamai kira. "Aliyu, Son, Gadanga na" fita yayi daga part din yana mamaki to ina yaje yaga motarshi ai, har zai wuce idanunshi suka sauka kan wani fine paint brush dake kasa, tsugunnawa yayi ya dauka yana murmushi yace "yau yan zanen sun tashi kenan jibi ya yarda wanan baima saniba" garden din dake side
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78