Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 20

Chapter 20

A Tsakanin Soyayya Book 1 Complete Hausa Novel – Aliyu’s Romantic Journey Begins 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Aliyu yatashi da sauri yanadan dariyan shakiyanci yace "leave me alone jor, karka karyani, shine kazo koka kirani" wayarshi dake kan gadon yadauka yace "I know kana mosque saisa I didn't call, wait before anything am hungry" hararan shi Aliyu yayi yatashi daga kan gadon yace "chop chop, Dady zai aiko mana da abinci, let's go, muje falo" tashi Abdul yayi yabi bayanshi suka fita falon daidai lokacin akai knocking kofa, Abdul ne ya amsa shikuma Aliyu yafada kan kujera. "yes come in" bude kofa akayi bodyguard su biyu na Aliyu suka shigo dakin daya dauke da manyan warmers guda biyu sai dayan kuma dauke da tray da slice fruits a bowls kekai, dining Aliyu ya nuna musu suka kai abincin wajen sanan suka juya suka fita, hanyar dining din Abdul yayi yazauna yana bubbude warmers din yana kallon abincin dake ciki kafin yadau plate da spoon ya debi ofada rice da smoke fish stew ya ijiye a gabanshi, wani bowl yasake dauka yadau spoon yacika bowl din da fried pepper chicken sanan yadaga kai ya kalli Aliyu dahar ya kwanta akan kujera yana daddana remote yana lumlumshe ido yace "let's eat Leo" yatsine fuska yayi yace "me aka dafa? Me acikin warmers din?" hararan shi Abdul yayi yafara cin abincin shi batare daya kulashi ba dan yaga iskanci Aliyu keji shikuma right now he's starving bari yabama cikinshi hakkinshi tukunna yanda Abdul kecin abincin was tempting his taste bud ahankali yatashi daga kan kujeran ya mike tsaye, dariya Abdul yafashe dashi ganin yatashi, karasowa dining din yayi yaja daya daga cikin kujerun dining din na kusada Abdul din dakemai dariya ya zauna fizge spoon din hanun Abdul din yayi yaja plate din rice din ya shiga ci, dariya Abdul ya shiga yi yace "nadaiji shege waya gayama anama abinci yanga" yay maganan yana daukan wani spoon suka shiga ci tare, he hardly eat much but because yanaci tareda wani sosai yaci abincin har Abdul na karamusu sukaci, baiwani ci pepper chicken din sosai ba yazuba juice ya kwankwada shikuma Abdul yaci tass, saida suka gama yace "this fruit kasasu a fridge Leo ni banda inda zasu shiga acikina while I clear the dining" gyadamai kai yayi yatashi ya dai bowls din yakai fridge shikuma Abdul ya kwashi plate yakai kitchen. Gamawa sukayi sukai falo Abdul yadau jakunkunan kayan su yace "kaga kayanmu gobe zamu fita dawuri fa, mune abokan ango" tabe baki yayi yadan shafa kai yace "am sleepy sosai bangane mekake cewa, let's go to bed" waya Abdul yadauka yana gyara kwanciya kan kujera yace "kai kaje ni waya zanyi da" ya kashemai ido, tsaki Aliyu yayi yay hanyar bedroom yace "dan iska aikin kenan soyayya" daga murya Abdul yayi yace "bari kafara naka bazaka bari muhuta ba, kardai kazo kana mana kuka idan tace bata sonka" daga murya yayi daga bedroom yace "never" shima daga murya Abdul yayi daga falo yace "is a bet" tsaki Aliyu yaja yana cire rigan jikinshi yace "rubbish, why will I ever cry over soyayya? Allah kyauta" yatabe baki ya shiga bathroom yana tafiya da kyar so yake yay wanka yazo yay bacci. Asuba tagari!!!! _Suleja_ Shigowa dakin tayi tana gyara tsintsiyan laushin dake hanunta tana satan kallon Ammi, harara Ammi ta watsa mata tace "wai lafiya kike kallona haka?" dakin Ammi ta shiga da sauri ta ijiye tsintsiyan tafara gyara gadon saida tagama tsaf sanan ta sharo dakin tafito da sharan ta shiga dakinta ta sharoshi shima sanan tafara sharan falon Ammi sai hararanta take dan tai mata laifi tunda tai sabon wayan nan da Baffa yakawo mata take uban danne danne awayan data rasa nameme, tarasa uban me take dannawa awayan dababu komi aciki, dasafen nan ma daga ta dumama abincin kari saida taji kauri koda tafito taje kitchen abincin ya kone ga Aneesa agefe agaban murhun kan kujera tana daddanna waya bamata saniba tsabagen nisan datayi shine ta zuba mata dunddu ta karbe wayan har yanzu bata bataba saisa taketa satan kallonta tanaso ta roketa tabata amma bataga fuskar hakanba, karasa share falon tayi ta fitar da sharan tsakar gida sanan tawuce kitchen ta debo rushi ta dawo falon ta zuba turaren wuta ta shigar dasu dakunan kafin tafito da turaren wutan ta ijiye a tsakar falon tawuce tafita tsakar gidan, tsintsiyan kwakwa tadauka tana gyarawa ta shiga share tsakar gidan tana tafiya zaure dasu bude kofar gidansu da akayi yasa ta dago daga sharan da sauri wata farar yarinya ce doguwa tadan yafa dan ficicin gyale ta shigo tsayawa Aneesa tayi turus tana kallonta murmushi yarinyar tayi tace "yakuri hala na tsorataki dan Allah tambaya nake wlh tun safe muke garari a Suleja nan mun kasa gane gidan dan Allah nanne gidansu Aneesa mai lalle?" jin gidansu ake nema yasa ta gyadamata kai tana murmushi tace "nanne" wani irin ajiyan zuciya yarinyar ta sauke tana shafa kirjinta tace "Wai Alhamdulillah laaaa koma kece Aneesa mai lallen?" dan murmushi tamata tace "eh, nice" da sauri yarinyar tabude kofar gidan wani babban motane pake a kofar gidan nasu ihu tayi dagangan zauren tace "Anty nanne gidan, gama Aneesa mai lallen nan" bude kofar bayan motan akayi wata budurwa fara itama wacce tafi ta zauren tsawo da dan kiba tafito kana ganinsu kasan Ya da kanwa ne tana rike da wani hadadden designers bag na Charles and Keith da sallama ta shigo zaure. "Assalamu Alaykum" daga kai Aneesa tayi tace "wa alaykumus salam, ina kwana" tagaidata ganin babba ce, murmushi budurwan tayi tace "lafiya lau Aneesa, ashe kece mai lallen kinga wuyan damukasha kafin mugano gidanku kuwa" dan murmushi Aneesa tayi dake karama fuskanta wani irin siriintaccen kyau tace "lalle kukazo ne?" atare ya da kanwar sukace "eh lalle mukazo" "to kushigo, bari na shimfida muku tabarma ku zauna saina hada lallen mufara" da sauri yayar tace "a'a munzo daukan kine home service mukeso bamu kadai zamuyiba duk yan uwanmu na gida, tundaga Abuja aka mana kwatancen gidanku akace mana u are one of the best masuyin lalle in the whole Abuja, please home service mukeso yau za'a fara events din bikina wushe wushe za'ayi da daddare shine zakimana lalle" dan zaro ido tayi ganin yanda macen ke magana ayangance zaka gane irin yaran manyan nanne yan gayu, wasa da yatsan ta tashiga yi tace "banayin home service kuyakuri duk maison lalle a gida nakemai" daga yar har kanwar yisukayi kaman zasuyi mata kuka ahankali yayar tace "dan Allah Aneesa karkimin haka kekadai ne hope dina yau dinan am so stress out, bansan kan Abuja sosai ba hutu school kawai kedawo dani daga abroad saikuma wanan bikin nawa da za'ayi, ta ina zan nemo wata me lalle dazata bini gida tamana, dan Allah Aneesa mai lalli help me kinji sister" sosai tabama Aneesa tausayi kana ganinta kasan tagaji kam ahankali tace "to shikenan amma kuzo kufadama Ammi na, inta yarda saina biku" da sauri amaryan tace "to muje" ajiye tsintsiyan Aneesa tayi tana gyara hulan kanta dafa yau taso tai tsifa taje kitso dan gashin kanta ya tsufa amma kuma gamasu lalle sunzo, bude labulen falonsu tayi ta shiga falon da sallama suna biye da ita har gaban Ammi taje tace "Ammi gabaki nan sunce nabisu wai namusu lalle home service

Table of Contents

Chapters

78 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});