Chapter 9
Chapter 9
korar yarinyar nan daga gidan" cikin alamar tambaya lami tace "kamar ya kuskure bayan itama zata kawo min matsala idan na barta a gidan, saboda idan na barta kinga itama fa tana da gado banda gidan ma ga kuma gonakinsa fa," murmushi delu tayi tace "ai ke baza ki gane ba ai cikin salama zakiyi komi batare da kowa ya zargeki ba". Inna lami tace "kamar ya?" Kuma murmushin mugunta delu tayi tace "ai kawai aikatau zaki turata birni, kinga kin samu riba biyu kenan ga kudin aikinta gashi kuma ta bar miki gida cikin salama," cikin happy inna tace "Kai delu shiyasa fa nake sonki amma kuma yanxu lokaci ya kure ya kenan?" Delu tace "a'a aminiya lokaci bai kureba, yanxu ita Hibbah tana ina?" Cikin nuna rashin damuwa lami tace "ya huce gidan kakarta tana da inda yafi nan ne?" Delu tace "yauwa kinga ya kwana gidan sauki, kawai turawa zakiyi kice tazo nasan tunda yarinyar nan na sonki babu abinda zai hana ta zuwa." Inna lami tace "Kai delu kin yi dabara to yaushe zaki kaita kenan?" "Ai dama in anjima zan shiga garin kano, Zan anso kudin wata yarinya kinsan wata ya kare," delu ta bata amsa. Lami tace "to kuma kudin nasu yana kaiwa nawa?" Delu tace "eh to ya danganta da yanayin gidan da aka kaita da kuma yanayin aikin da take musu," lami tace "Kai amma fa zan cafki kud'i" delu tace "kodai zamu cafka?" Lami bata amsa ta ba tace "yafa kamata mukoma wajen boka don kar fa malam ya kawo min cikas a lamurana, kamar yarda na fada miki jiya ma fa yaso ya kwafsa," delu tace "bakya sanya lami baki da sauk'i da kinga ya fara warewa saiki kuma d'aureshi" dariya inna lami tayi tace "ina fa zanyi sanya, yanzu dai yaushe zamu je?" Delu tace "eh to muje yanxu, bara na k'arasawa Musa d'umamencan sai mu je?." Lami ta d'an yatsina fuska tace"nikam musan nan idan wani yaji yarda kike masa saiya zata shine mijin naki ai," dariya delu tayi tare da cewa "kamar yarda kike yiwa Rahmatu ba," "ai gara ni macece kuma idan nayi mata ma ai koya mata nake," lami ta maidawa delu. Delu tace "oho dai nima koya masa nake yi" ta fada tana mikewa. Bakin murhu ta nufa taje ta sauke tukunyar takai d'akin Musa, sannan ta zaro mayafinta suka nufi gidan boka. Wani daji suka nausa canciki sunma fita daga kauyen *katsalle* sun shiga dajin k'auyen *Gomma* wani dogon dutse naga suna hawa saida suka hayeshi tas, sai kuma suka cire mayafansu da d'an kwalayensu da takalma suka fara tafiya da baya da baya baya har suka k'arasa bakin wata bukka. Zagi suka shiga yi sai ga wani mummunana gardin mutum ya bayyana a zaune a wajen yana dariya yace "halakarku kun zo ku kuma halaka?" Ya k'alk'ale da dariya, lami ce tace "yauwa boka dama........" Katseta yayi da cewa "na sani! kamar yarda aka Saba ga wannan," ya mika lami wani kullika yace "kici gaba da tsarki dashi, wannan a abincinsa wannan kuma turare," ya kwashe da dariya. Karba tayi tana godiya, yace "wannan yarinyar daza ku turata aikatau karku bari ta kuma waiwayar k'auyen nan don idan kika bari ta dawo gida da akwai matsala gagarima. Ku tashi ku tafi na sallame ku." Yana gama fadin haka ya b'ace, kallon kallo suka shigayi kafin su tashi subar wajen, kayansu suka d'auka suka sa sannan suka sauka daga dutsen kowacce da abinda take sakawa musamman ma lami. Bayan sun shiga cikin k'auyensu lami ta kalli delu tace "me kike ganin zamuyi akan abinda boka yace?" Delu tayi shiru kafin tace "mafita d'aya ce kawai idan na kaita gidan nace basai ta rink'a zuwa ganin gida ba zan dinga zuwa ganinta." Lami tace "kina ganin hakan ba matsala" delu tace "babu wata matsala ai nace zan dinga zuwa dubata kuma su gidan gaba ta kaisu." Lami tace "Hmm to shikenan bara na huce gida saikin zo." Delu tace "ai kawai mu shiga ki aika a kirata mu huce don ba lallai na dawo ba," murna fal cikin lami suka shiga cikin gidan. Suna shiga gidan sukaci sa'a Rahmatu na nan, delu tace "shikenan nan ma Rahmatu nanan kinga saita shiga ta kirata koh," kallonta lami tayi tace "toh allah yasa taje kema kinsan halinta." Delu dai batace komi ba suka k'ara cikin gidan. Kujera delu taja ta zauna hakama lami amma ita tata kujerar kusa da Rahmatu ta kaita tare da kwantar da murya tace "yauwa Rahmatu Dan allah shiga gidansu Abu ki kira min Hibbah kice tazo yanxu." Kallon ta Rahmatu tayi a wulak'ance tace "tab ni wallahi na gaji babu ida zani" matsowa lami ta kumayi kusa da ita tace "haba autar inna kije mana don Allah" Rahmatu ta zumburo baki "wai me zakiyi mata ne bakince ta bar gidan ba, kuma kince ta tsaneni to me kikeso kuma tayi mana a gida?" Lami tace "aike baxaki gane ba aikatau za'a kaita birni kinga kenan duk kudin da aka bada na aikinta namu ne daga nan ma saina saimiki wayar da kikace kina so koh?" Daga Kai Rahmatu tayi cikin happy tace "eh wallahi inna ammafa kinyi dabara bara naje" ta fada tana mikewa da gudu tabar gidan. Lami tace "oh ni lami naga Randa Rahmatu zatayi hankali" delu tace "gaskiya kam." *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:22 PM] Maman Najma Author P1: πππππππππ *RAYUWA* page1β£5β£to1β£6β£ *NA* *MAMYN NAJMAH* πππππππππ *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION* D.Z.W.A Su Hibbah suna zaune a tsakar gida suna gyara waken alala ita da Abu da gwaggo, sai gay Rahmatu ta shigo gidan kamar an wurgota ko sallama babu ta kallesu d'aya bayan d'aya, sannan ta maida kallonta ga Hibbah tace "ke zo inna na kiranki," tana gama fadin haka ta juya ta fita abinta. Tsorone ya bayyana k'arara a fuskar Hibbah ta kalli Abu tace "Abu kinji wai Inna naje ni wallahi tsoro nake ji." Abu tace "kuma ke zuwa zakiyi? Kika sani ma ko wani muguntar ta kuma had'a miki kawai zaki kwashi jiki kice zaki," gwaggo tace "ke inna ruwanki kika sani KO uban ne yace ta dawo?" Abu tace "tab, gwaggo kin dai fimu sanin halin matar nan wallahi ko yace ta koma sai tayi yarda tayi tace karya maida ta." Murmushi gwaggo tayi tace "hmmm Ku yara ne bazaku gane ba, ai zata maida tane don ta ci mata gaba da tallanta, ko kuna tunanin wannan mara kunyar 'yar tata Rahmatu zata daukar mata talla?" Hibbah wadda tayi shiru tana sauraronsu tace "wallahi gwaggo nima abinda nayi tunani kenan," ta mike tsaye tare da cewa "bara naje naji gwaggo," "waike yanxu xuwa zaki yi?" Abu tayi saurin katseta, Hibbah cikin damuwa tace "to ina da wani mafita ne banda naje d'in?" Abu ta tab'e baki tace "tab wallahi da nice baza ni ba," gwaggo tace "kinga karki biye mata yi maza kije kiran innarki kinji." Daga kai Hibbah tayi tace "to." Ta fice a gidan. Gidansu ta nufa tana shiga taga inna lami tare da aminiyarta inna delu suna hira harda shewa, wani yawu ta had'i kut, zuciyarta ta fara bugawa tasan tunda taga inna delu a gidan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63