Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 22

Chapter 22

Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ina?" Fauzy ta tambaya, muna sitting room d'inta" fauzy tace "ok to bara na fad'a mata" fauzy ta kalli Hibbah tace "y'ar gidan aunty kije aunty na kiranki wai suna sitting room," Hibbah tai murmushi tace "au kema haka zaki ce?" Saudat da suke ta aikin make up ita da fauzy dayake su duk sun iya har kit ne dasu tayi karaf tace "to ba 'yartan bace," ta kalli fauzy "ai fauzy jelar aunty ma zakice mata ai, ga wanan na Aunty ne kayanta ne ta bari a d'akinta shine momy tace na tawo mata dashi," suka sa dariya Hibbah ta mik'e tare da d'aukar kayan ta nufi sitting room d'in, a lokacin su Hibbah har sunsa ankonsu na sisters baby pink yayi mata kyau sosai. 'Yan matane a zaune a parlor kowacce na kintsa kanta sunsha wani material sky blue sunyi kyau, ta k'arasa ciki inda yayar fauzy surry take tace "Yaya surayya gani" surry tace "zauna Hibbah Aysha tace a Fara yi miki," tace "to" ta zauna aka fara yi mata a zuciyarta tana jin k'aunar Auntyn ta na ratsata. Aunty ma alwala ta d'auro tazo ta tada sallah saida ta fara gabatar da maghrib sannan tayi isha'i, ta kalli inda Hibbah take tayi murmushi ganin yarda Hibbah tayi kyau bata ce komai ba, saida aka gama yiwa Hibbah aka d'aura Mata d'ankwali tayi kyau kamar itace Amaryar sannan aka Fara yiwa Aunty, Hibbah ta sunkuyo da kanta daidai kunnan aunty tace "aunty ga kayanki nan inji momy, kuma aunty na gode Allah ya saka da alkhari ya barki da uncle sagir." Aunty taji dad'in add'arta a zuciyarta tace ameen a fili kuwa hararar Hibbah tayi, Hibbah cikin sauri tabar d'akin ta koma wajen su fauzy ba jimawa ma akace su fito ga motoci nan. Motar wani abokin Sagir d'in suka shigaa akwai shi da surutu, ita kuwa Hibbah tunda ta shiga motar batai magana ba tana dai ta Danna wayarta ta bud'e pulse d'in da aunty ta bata kud'ine sababbi 'yan hamsin bandir d'aya tayi murmushi a ranta tana yiwa aunty godiya, ta cigaba da sauraron duk hirar dasuke yi shida su Saudat da haka suka k'arasa wajen dinner d'in,waje yayi kyau an k'awatashi. Su Hibbah akace karsu shiga har sai Amarya tazo, suna nan a jikin wata mota saiga Amarya da angonta cikin shiga ta alfarma suka shiga da su, kowane sit na mutum hud'u ne dan haka su Hibbah suka samu d'aya daga ciki suka zauna. Suna zaune wannan Wanda ya kawosu d'in yazo ya zauna yana cewa "na zamo cikon na hud'un kenan," ya kalli Hibbah yace "y'ar beauty waike bakya magana ne?" Ta kalleshi tace "sannu ka," ta d'auke kai, ya kalli Saudat yace "Saudat 'yar beauty nan bata magana ne?" "Tana yi mana, ai indai kaga tana magana to tana tare da aunty shiyasa ma nake ce mata jelar aunty," suka sa dariya ita da fauzy. Hibbah ta harareta, shi kuwa murmushi yayi yace "mene sunan beautyn tawa ne," Hibbah ta maimaita a ranta beautyn tawa? A ina na zama tashi? Fauzy ce ta katse mata tunani, ji tayi tace "sunanta Hibbah," da murmushi a saman fuskarsa yace "Hibbaaaaahhh!" Ya wani ja sunan tare da sakin ajiyar zuciya ya kalli Hibbah yace "Hibbah sunanki yana da dad'i kamar yadda kema kike da kyau sunan ya dace dake," Hibbah tace "na gode," yace "da farko dai sunana Jabeer ni abokin sagir ne, kuma ba maganar b'oye b'oye tunda na ganki naji kin shiga zuciya ta Hibbah," Hibbah ta mik'e tace "to na gode da sonda kake min" ya kalleta yace "ina zaki kuma Hibbah? Ina son muyi magana ne," Hibbah ta Fara tafiya tace "inason zanje nayiwa Auntyna lik'i ne," ta fad'a tare dayin gaba. Jabeer ya kalli su fauzy yace "wallahi da gaske nake Saudat ina son Hibbah tun dana ganta kuma aurenta zanyi" Saudat ta mik'e tace "Ya Jabeer indai kana son ka samu Hibbah cikin sauk'i to ka kama k'afa da aunty" yace "allah ko Saudat" fauzy tace "wallahi ya Jabeer don aunty ce kad'ai zata iya fad'awa Hibbah taji," suka kalli wajen rawa, Hibbah suka hango tana ta zubawa Auntyn ta kud'i, Jabeer yayi murmushi tare da yin wajen rawar su fauzy ma suka mara masa baya. Yana zuwa ya shiga zubawa Hibbah kud'i yana mata lik'i, ta d'ago Kai ta kalleshi yayi mata murmushi ya cigaba da yi mata lik'in, kallo sai ya koma Kan Hibbah, su Saudat mazari tuni aka fara rawa ta rik'e hannun Hibbah wai sai tayi rawa, ita kuwa Hibbah ba gwanar rawaba ta dai tsaya tana kallon yadda suke ta rawar su. Haka yayi ta mata lik'i daga baya aka tashi daga wajen dinner ango ya d'auki amaryarsa suka huce, abokan ango suka kwashe 'yammatan suka huce dasu. Ita kuwa Hibbah tana ganin zaa tashi taje ta cewa Adamu driver ya kaita gida tayiwa Aunty sallama, aunty ta jata gefe tace "Hibbah dan allah kiyi hakuri da duk abinda Kausar zata yi miki nasan kina da hakuri ki k'ara akan na da, kuma nasa Adamu d'azu yakai miki kayanki duka gidan saina gobe dazaki sa kawai ya bar miki suna d'akina," Hibbah ta share hawayen daya zubo mata "insha allah aunty na gode," da haka sukayi bankwana, aunty ta kawar da kanta don bata son Hibbah taga hawayenta, Hibbah itama ta huce tana share hawaye don ta shaku da aunty fiye da kowa, Adamu ya tafi kaita. Shi kuwa Jabeer shida su Saudat sai nemanta suke yi daga baya suka gaji ya d'auki Saudat ya kaita gida ita kuma fauzy driver'n su ne ya kaita. Hibbah tana zuwa taga gidan babu kowa duk 'yan bikin sun watse sai su aunty Kausar da safiyya a zaune a parlor suna maida gajiya, Hibbah ta shigo da sallama babu Wanda ya amsa Kausar ta bita da wani mugun kallo tace "'yar aiki kawai.............. *kuyi hakuri da wannan, muna asibiti ne 'yar hatsaniyar da taa faru a fagge ne ta ritsa da nephew na yanzu haka ma muna asibiti bashi da lpy, ina bukatar addu'ar ku plsπŸ™.* *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:22 PM] Maman Najma Author P1: πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“ *RAYUWA* page2⃣7⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“ *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION* D.B.W.A *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* *Wannan page d'in nakune MASOYA RAYUWA GROUP na gode da k'aunar da kuke nuna min Ana mugun tare🀝😍.* *Fans na gode da addu'o'in ku Allah ya saka da alkhari.* Hibbah ba tace komai ba ta nufi stairs da niyyar hawa, fincikota Safiyya tayi tana mata wani mugun kallo tace "haba madam da kenan kafin aunty tabar gidan nan, yanzu baki da 'yancin hawar mana stairs ba tare da izinin mu ba don haka kisan nayi," Hibbah ta d'ago ta kalli Safiyya sannan ta kalli Kausar ta juya da nufin ta fiya taji muryar momy, "Hibbah hayowarki ki rabu dasu don Aysha ta bar gidan nan hakan ba yana nufin na daina kula dake ba kenan," Hibbah ta juyo ta kalli momy tana daga sama take magana momy tayi mata murmushi, hawa Hibbah ta shigayi direct ta huce d'akin Auntyn ta. Momy ta wurga musu wani kallo tace "ke Safiyya ki kiyayeni wallahi ki fita a ido na, naga kanki yana rawa ko zan

Table of Contents

Chapters

63 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});