Chapter 32
Chapter 32
baya nan ake sanin amfaninsa, shi yafi kowa sanin mahimmancinta a gareshi, gashi nan gidan yau kwana biyar kenan ba'a share ba bare a goge k'ura, to waye ma gwagin yin aikin shi ko Kausar. Matar da take fice warta aiki kuma ko tana nan baza ta iya ba, basu gane rashin Hibbah gib'ine a gidan ba sai a wajen girkinta babu abincin nan Kala Kala na yay daban na gobe daban, yau gashi kwana biyar kenan kullum abinci d'aya sukeci ba canji har ta gundire su. Babban matsalar da ta tashin hankalin Faheem bame kular masa da Nawaz, ya rasa yadda zaiyi da damuwa Nawaz ya daina cin abinci har yayi 'yar rama, ga damunsa da kuka da yake yi shi dai a kaishi wajen Aunty Hibbah zai je wajenta, abubuwan da ta saba mishi sun shiga jikinsa ya shak'u da ita sosai fiye da uwar data haife shi. Da daddare baya barinsa yayi barcin kirki dan rigima yake masa shi wai dole wajen Hibbah za'a kaishi. Ashe ko kare ne da ranarsa ita kanta Kausar duk da ba kulata take yi ba to amma ta Saba da abincinta sannan ga d'awainiyar da take yi Mata da yaro har sun shak'u, bata da wata fargaba da wahala hankalinta kwance yake tasan Hibbah zata kula dashi. Kwana biyu da bata ganta ba sai ta dinga yiwa Faheem k'oeafi tana tambaryarsa ina Hibbah ta tafi bata sanar da ita ba, haushine ya cika shi yace "tayi tafiya," a ganinsa duk lefinta ne, ita ta tab'arb'ara jin dad'in gidan, da tana tarairayar su da menene zai dame su. Shi bama damuwarsa kan Hibbah tayi yawa bawai don tabar kula masa da gida ba, kad'aicinta ya danganta da babban al'amari ahi kad'ai zai iya sanin abinda ke damunsa, baisan abin ya shahara haka ba saida ya daina jin motsinta a kusa dashi, yaje bakin k'ofar d'akinta ya kasa kunne ko zaiji motsinta amma shiru ya bud'e d'akin ya lek'a babu kowa a ciki d'akin har yayi k'ura, Anya kuwa zai iya hakuri? Ya zaro wayarsa har ya dannan layin Aunty Aysha yayi saurin katsewa, karfa Aysha tayi tunanin wani abu don bata San Hibbah bata nan ba, bai jin dad'i Sam a ransa yasani yayi rashin wani abu mai mahimmanci wadda ya rasa yadda ya kasa sarrafashi. Ya sauke ajiyar zuciya, ya kalli Nawaz dake jikinsa, Bashi da lafiya tun jiya da daddare da yaci wani farfesun kifi ya sashi amai da ciwon ciki, shiyasa yau ko shirin makaranta baiyi masa ba. Nawaz ya fara juyi ya rik'e cikinsa yana murk'ususu, hankali tashe Faheem ya d'agoshi ya rumgume shi "Nawaz menene?" Yasa kuka "daddy cikina ciwo," "oh God sannu sannu kaji," ya d'auko maganinsa na jiya ya bashi, sannan ya d'aukeshi ya kaishi toilet yana masa wanka Nawaz ya shiga kwararo amai, habawa duk hankalinsa ya kuma tashi don ko k'uda baya son ya tab'a Nawaz tilon d'ansa d'aya daya mallaka don Kausar ta hana kanta haihuwa sai nan da wasu shekaru. Ya gama yi masa wanka ya saka masa kaya ya Bashi tea nan ma ya amayar ya kasa jurewa ya d'aukeshi suka nufi asibiti. Suna zuwa doctor ya dubashi yayi masa test d'in fitsari da jini yasa aka dauki hoton cikinsa duk babu wata gagarumar matsala, kawai dai cikinsa ne baison abinda yaci shiya b'ata masa ciki. Doctor ya sanya mishi ruwan don jikinsa yayi sanyi sosai, saida Nawaz ya samu barci sannan ya kira Kausar ya fad'a mata komai. Hankalinta a tashe ta shigo ta ganshi yana barci ta zauna tana shafa sumarsa tayi ajiyar zuciya cike da tausayin d'an nata wani mummunan tunani ya fad'o mata _yanzu idan Nawaz ya mutu yaya zanyi?_ ji tayi k'irjinta tayi mugun bugawa. Ta dubi Faheem yana rik'e da hannun Nawaz da aka Sanya mishi k'arin ruwa don kar ya motsa ya goce, kamar yasan abinda take tunani wani abu ta hango a cikin idanunsa tsabar damuwa ce kawai, Faheem yana son yara sai dai babu yarda zaiyi ne yabar abin a zuciyar shi. In banda yahudanci da sab'awa Allah, bawa yace shi zai zab'awa kansa yaran da yake son ya Haifa wannan ai halaka ne, ka manta Allah shi ya halicceka shiyake da hurumin zab'a maka komai na rayuwa, kuma yarda yaso haka za'ayi don haka tun anan imanin mutum yayi rauni kenan. Ta kewaya hannunta a bayanshi ta sunkuyo ta gefen kunnanshi da sigar lallashi "dear menene ka damu da yawa zaiji sauk'i insha Allah, baka walwala cikin kwanakin nan meke saka damuwa ne haka uhmm?" Ta janyo kujera ta zaune suna fuskantar juna, "kinfi kowa sanin damuwata, dole ne na damu don ni bansan dad'in mace ba, saboda bamu da mahimmanci a gurinki aikinki ya fimu a wajenki baki da lokacin iyalinki, duk wani hakuri nayi a kanki gashi nan saboda ciye ciyen restaurant yaro na ya samu matsala cikinsa ya gurb'ace, kullum ni kenan yawo gidajen abinci sunan ni magidanci ne ina da mata, wani abin bana k'ate bane nifa na gaji mafita zan samawa kaina," ta d'ora kanta akan cinyarsa don tasan ta tab'oshi kuma ya fita gaskiya "kayi hakuri naji lefina na d'auka zansa momy ta nemo mai dafa masa abinci," yayi shiru maganar ta kuma Bashi haushi wato ita dai baza ta zauna ta kula da gidanta ba kenan. Nawaz ya farka yace "Daddy" ya rik'oshi yana shafa kansa "Nawaz sannu cikin ne?" Ya girgiza kai, "zaka sha yogurt?" Ya kuma girgiza kai yace "aunty Hibbah" suka kalli juna, tsaki taja "har yanzu bai manta wannan yarinyar ba sai kace mayya ko kurwars ta kama ne, haba abin yayi yawa," bai kulata ba ya zubo mishi yogurt a cup yana bashi amma surutun Hibbah yake tayi musu, Kausar ta kama mita don haushi taji wai duk kwashe kwashen Faheem ne da Aysha sai da ta nuna rashin amincewarta akan zaman Hibbah a gidan k'ila ma mayya ce. Yayi murmushi "hmmm ki Sani ita zuciya nason mai kyautata mata shi yake sanya shak'uwa har mutum ya ji bazai iya rabuwa da mutumin nan ba domin rashinsa wani gib'ine a rayuwarsa, kinga d'anki ma kenan k'aramin yaro yasan mai tarairayarsa mai k'aunarsa har rashinta ya sakashi damuwa, ina tabbatar miki da kece bakyanan bazai damu haka ba don bai saba ganinki a gida ba bare ki rumgume shi ya shak'u dake kamar ko wace uwa da d'anta, 'yan awoyi kad'an kike bamu sauran duk na aiki ne agogo sarkin aiki, to idan mafarki kike ki farka don wallahi kinji na rantse na kusa sama mana mafita," Kausar taji zafin kalaman Faheem ta wurga masa wani kallo tama kasa magana sai huci take ta warto jakarta ta fita fuuuu babu ko sallama. Ya tab'e baki, ya cigaba da kula da Nawaz yana ta biye masa suna surutu har bacci ya d'auke shi ya gyara mishi kwanciya. Washe gari da sanyin safiya ta shigo tana cika tana batsewa, sai da taga jikin Nawaz da sauk'i ta d'anyi saki ranta, doctor ya shigo ya dubashi ya d'an jinkirta Bashi sallama don a cewarsa karsu tafi wani abu ya faru saiya tabbatar da lafiyarsa. Dak'ar Kausar tayi masa magana tana wani kumbure kumbure ta tambayi lafiyar Nawaz, shima a ciki ya amsa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63