Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 45

Chapter 45

Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

canza ra'ayi ba don hakan nuna k'aranta ne" ya had'e girar sama da k'asa to zaki gani kuwa ni zan tsone miki ido idan kuma baki yarda ba kije ki binciki labarin don haka bakin alk'alami ya bushe ni dake mutu ka raba," ta matsa gefe ya dings k'yalk'yala mata dariya mai ban haushi, hangar cikinta tana kad'awa "Allah ya tsare ni da aurenka saidai a kai maka gawata Faruq don bana sonka bana k'aunar halayenka" "to ai kuwa za'a Kai gawar taki gidan nawa ko kuma muyi mutuwar kasko ki k'one mu gaba d'aya saboda k'iyayya" Bata san sanda ta sa kuka ba don bak'in ciki, ya rik'o hannunta ta k'wace da k'arfi d'aki ta nufa da gudu ta kulle hankalinta yayi mugun tashi, number Aunty ta shiga kira, tana d'agawa cikin rawar murya "Aunty........" Da sauri Aunty ta katseta kinga ni babu ruwana, bani ba ke Hibbah kuma kanki kika cuta, Faruq ba kanwar lasa bane d'an uwa nane amma bazan b'oye miki ba ina cikin masu da'awar wannan aure, Faruq jikinki kawai yake so daya samu zai yarda k'wallon mangoro ba fata nake miki ba." Ta fashe da kuka "Aunty wallahi tallahi bana sonshi basan ya k'ulla wannan k'aryar ba nima yanzu yazo yana fad'amin" tsawa Aunty tayiwa Hibbah donhaushinta take ji "dalla ni rufe min baki ni kin bani mamaki da kunya, Dana san kina son shi da tun farko ban d'aukoki daga gidan ba na k'yaleki yayi miki abinda zaiyi miki, wallahi Hibbah ina tausaya miki a hannun Faruqna fad'a miki badon Allah yake sonki ba" cikin kuka Hibbah tace "Auntyna kiyi min rai na tuba wallahi gaskiya na fad'a miki, na shiga uku Aunty kiyi hakuri wallahi bazan iya auran Faruq ba," "to ni me zan yi miki ai ta faru ta k'are tunda har iyaye sun shiga maganar saiki d'auki k'addara haka Allah yaso, fatana Allah yasa ki bashi guzurin shiriya ki dunga sashi a hanya ta k'awarai" Aunty tana kaiwa man ta kashe wayar don ba k'aramin haushin Hibbah take ji ba, gani take da Hibbah bata amince da Faruq ba da bazai ce sun daidaita ba, kuma da gani take Hibbah tana son Faruq don da bata sonshi baza ta dinga sauraronshi ba, da wata ce yadda yayi barazanar lalata Mata *RAYUWA* ai da ko kallo bai isheta ba. Hibbah tayi wurgi da wayar ta kifa kai ta saki wani irin kuka, ita dai ta shiga uku haka *RAYUWARTA* zata kasance cikin k'unci, kuka take sosai tana shashsheka kamar zata shid'e numfashinta har wani sama sama yake yi. Ji tayi an bud'e k'ofa ga zatonta Nawaz ne, wani mugun kallo tayi masa don ita tayi zaton ma ya tafi. A hankali ya zauna kusa da ita, ta zubura ta koma gefe don yanzu bata k'aunar ganinshi ko kad'an, ya d'aure fuska gami da d'ora k'afa d'aya kan d'aya yana kad'awa cikin k'asaita yana wurga mata harara, wanj murmushin mugunta dake saman fuskasa yake jifanta dashi. Wata muguwar sha'awarta yake ji kuma yanason aikata k'udirinsa don ya tabbatar mata da ta zama tashi, surarta mai kyau yake gani, kafin ta ankara ya fizgo hannunta "haba baby Hibbah aini mijinki ne na rantse miki bazan wulakantaki ba inason ki ki yarda da ni" Wani bak'in ciki ya tokareta ta yaya zuciyarta ma zata amince da Faruq bayan ba sonta yakeyi tsakini da Allah ba, illa da wata muguwar manufa, burinsa kawai ya lalata Mata rayuwa, ta tuna maganar Aunty Aysha data ce _jikin kawai yake so daya samu shikenan zai yarda k'wallon magoro,_ tabbas haka ne gashi nan yanzu ma bashi da burin daya huce yaga ya tab'ata. Faruq ya tashi daga kusa da ita kamar Wanda zai fita daga d'akin, ita tayi tunanin ko haushi yaji zaiyi tafiyarsa, saidai taga sab'anin haka kulle k'ofar yayi ya zare mukullin ya jefa a aljihunsa yana dariyar mugunta. Kan gadon ya turata da k'arfin tsiya ya mak'ureta, Allah sarki Hibbah sai ta kuma sakin kuka. Cikin kuka take magana kanaji kasan cikin ranta babu dad'i "matuk'ar ka cimma mummunar manufarka akaina wallahi sai kayi nadama a rayuwarka, kuma aurenka ne bazanyi ba, bazan hanaka aikata k'udurinka ba tunda bakaji tsoron Wanda ya halince ka ba kana aikata abinda baya so." Bai ma san tanayi ba don shaid'an ya kad'a masa ganga yau dai yana k'ulaficin yarinyar nan wannan masifa dame tai kama. "Sai na fad'awa iyayenmu abinda kayi min domin su sani aure ya jagule, kuma su sani kai bak'in kumurci ne azzalumi" Ya rufe mata baki da hanci kamar zaiyi mata k'amshin mutuwa. Da k'arfi aka bugi k'ofar zubur ya d'agata yana harar k'ofar a k'ufule yake saboda burinshi bai cika ba, da gudu ta tashi zata fita ya rik'o hannunta ya murd'e ta saki k'ara ya toshe mata baki "ki nutsu ki kama kanki matuk'ar kikayi yunk'urin tona asiri na to kamar kin fasa k'wai ne don Daddy bazai yarda da zancen ki ba, koda zaki rantse da Qur'ani, kuma ina tabbatar miki mutuwa ce kawai zata hana wannan auren Hibbah saidai idan na mutu ko ke kin mutu. Ina tabbatar miki wannan gangar jikin mallakina ne kin zama tawa iyaye sun shaida kuma kafin wannan lokacin saina aiwatar da nufina yanxu an b'ata min shirina amma ki saurari gamonmu a gaba sai nayi kaca kaca dak............." Bugun k'ofar ya katse shi "Aunty Hibbah, Aunty Hibbah" yayi tsaki Nawaz ne amma yaron nan ya kwafsa masa ya doki iska da hannunsa, ya dubeta kuka take sosai kome ya tab'o zuciyarsa ya tallafo hab'arta "Hibbah sone sanadi ni kaina saina miki wani abin zanyi nadama ke kuma kiyi ta yimin gardama, to mene abin damuwa sirrin mu nefa ni dake babu Wanda zaiji. "Ubagiji ya sani wannan gub'atacciyar soyayya ce domin babu Allah cikin lamarinka, kana aikata k'udirinka aure ya lalace sai anyi istibra'i don tsarkake aure, Faruq kaji tsoran Allah ka tuna kana da k'anne idan akan yi musu haka baza ka ji dad'i ba" "ke ki share wannan wa'azin naki, abu ne na da yanzu zamani yazo da irin wayewa to menene ni na k'addara ke matata ce to meya rage, ai Allah mai gafara ne, ni ba ruwana da wannan surutun banzan ni saina yi abinda nake so." "Sai kayi laifi kace Allah mai gafara ne bayan yace kar kayi kai kuma kace sai kayi, a hakan Allah zai yafe maka bayan kak'i bin umarnunsa, Allah ya tsare ni da kai wallahi Kai babban mak'iyi nane" ya fashe da dariya "zan naushi wannan bakin mai tsiwa zaki d'and'ani kud'arki gamona dake ba kyau, gaskiya kinyi sa'a ina sonki Hibbah" ya lakuto hawayenta yana murmushi, ya tusa hannunsa a aljihu ya zaro mukullin ya bud'e k'ofar sannan ya dubeta yana murmushi yasa kai ya fita. Ta zauna dirshen tana kukanta mai zafin zuciya ta kuma yiwa Allah godiya tasan shine yake tserar da ita sharrin Faruq, tsabar rashin mutunci ne da rashin tsoran Allah, Faruq bashi da tausayi da imani dole idan y k'udurce mugun nufinshi sai ya aikata abinda yake so, baya fargaba shakkar uban kiwa Anya kuwa Faruq bashi da matsala a k'wak'walwarsa. Nawaz ya katse mata tunani ya kwanta akan ciyarta "Aunty Hibbah Daddy na bashi da lafiya yana.................

Table of Contents

Chapters

63 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});