Chapter 63
Chapter 63
zame bakinta daga nasa "kayi hakuri Dan......" Bata k'arasa ba ya d'auketa ya nufi d'aki da ita don ya kasa jurewa. *6 years later* "Asra baza kizo mu tafi ba zamu tafi mu barki fa" Nawaz dake tsaye a bakin k'ofar d'akinsu Asra d'in, yanzu yana da shekara 12 kenan sanye yake da wata shadda anyi masa d'inki irin na samari sai zuba k'amshi yake. Wadda ya Kira da Asra d'in ta fito yarinyace da bazata wuce shekaru biyar ba daka ganta kaga Hibbah don tsananin kamannin da suke da juna sanye take cikin wata riga mai hannun vest da wando jeans kanta anyi mata wata kalba mai shegen kyau an zubo mata dashi ta k'araso kusa da Nawaz d'in, cikin 'yar muryarta irinta Hibbah tace "kayi hakuri Ya Nawaz naje d'aukowa Uncle sweet din da Daddy ya siyo min jiya ne saboda bani da abinda zan bashi idan ya dawo" ta k'arashe maganar tana marairaicewa kamar zatayi kuka. Nawaz ya janyo hannunta "to sarkin 'yan kuka tawo mu tafi su momy suna jiranmu a mota" suka k'araso Asra ta nufi gaban mota don ita take zama anan don ko wani ya shiga sai ya fito bazai zauna ba. Faheem ya dube su "Nawaz me kuka zauna yi ne a ciki?" "Daddy Asra ce ta tsayar damu" Faheem ya kalli Asra "me kika zauna yi a ciki ne Mamana? (Sunan momy ne da ita Zainab)" ta d'an had'a rai "Daddy ni ka daina cemin Mamana kace min Asra yafi dad'i" yayi murmushi don yasan bata son sunan yace "to Asra baby" tayi dariya "yeeh daddy sunan yayi dad'i" ta dubi Hibbah "Aunty mama bani Asrar na rik'e shi dan Allah" Nawaz yace "a'a salon kawai ki muntsine shi anki a baki d'in" Asra ta juyo ta harareshi "to ina ruwanka Daddy ka Ganshi ko?" Faheem ya kalli Nawaz "a'a Nawaz babu ruwanka, ke kuma Asra bana hanaki yi masa rashin kunya ba oya tell him sorry" ya fad'a yana kallon Asra data turo baki tace "sorry" faheem ya kalleta haka ake bada hakuri?" Ta juyo ta kalli Nawaz tare da had'e hannayenta waje guda "am so sorry I won't repeat it" Faheem ya kunna motar suka nufi gidan Daddy, yana gama parking Asra ta bud'e k'ofar ta fito da gudu ta nufi cikin gidan tana kiran uncle Faheem ya girgiza kai su Hibbah suka fito Kausar tana rik'e da Asrar suka shiga cikin gidan. Tana shiga ta d'ane jikin Faruq, ya d'agata sama yana "oyoyo my Asra ina Nawaz?" Tace "yana mota yanzu zasu shigo dasu Daddy" ya sauke ta ta mik'a masa sweet d'in dake hannunta "happy birthday uncle" "Tnx my Asra wannan ne gift d'in nawa kenan to na gode" tayi murmushi "mention not uncle you deserve more" ta fad'a tana hawa saman momy tana kiran k'walawa Saida 'yar wajen Aunty don sa'anni ne. Su faheem suka shigo suka gaisa Faruq ya karb'i Asrar yana masa wasa sai k'yak'yata dariya yake Faruq ya kasa duban Hibbah don har yanzu kunyarta yake ji duk da tun wancan satin daya dawo ya nemi yafiyarsa kuma ta yafe masa amma har yanzu yana daya sanin abinda ya aikata a baya. Bayan azahar duk ilahirin family suna zaune a parlor Ana ta hira cikin rah da k'aunar juna, Daddy yayi gyaran murya "to abinda yasa na tara mu anan don na sanar muku da abin farin cikin daya samemu bayan godiya ga Allah daya shirya mana Faruq har yanzu yake Neman aure kuma insha Allah ranar juma'a za'a d'aura auren" gaba d'ayansu duk mamaki da farin ciki ya cika su har suna had'a baki wajen fad'in "wacece amaryar daddy?" Daddy yayi murmushi "ai tun zuwansa suka daidaita da Rahma" Hibbah dake kusa da Rahmatu tace "amaryarmu shine baki fada min ba" Haka dai sukayi ta hirar yadda bikin zai kasance. Ranar juma'a da yamma aka d'aura auren Faruq da Rahma Wanda dubun nan mutane suka halarci d'aurin auren musamman Faruq dayake da masoya kasancewarsa d'an k'wallo ada. To Rahmatu dai ta tare a gidan mijinta Faruq bayan gyara da tasha a wajen su gwaggo, sunci amarcinsu sun more. Shekararsu d'aya da aure Rahma ta sambad'o yaranta 'yan biyu duk maza masu Kama da Faruq sak ansha shagalin suna aka sawa yara sunan baba da Abba wato Mukhtar da Umar, ana kiran Mukhtar da Hammad shi kuma Umar Hammam. Sati d'aya da suna Kausar ta haifo itama 'yarta aka sa Mata sunan mamy wato Rukayya suke ce mata Hooriya. Haka *RAYUWA* ta cigaba da tafiyarwa wannan family cikin farin ciki da kaunar juna. *Fahibbateam💘* *SUBHANAKALLAHUMMA WABI HAMDIK ASHHADU ALLA ILAHA ILLALLAH ASTAGFIRUKA WA A TUBU ILAIH, ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH* *NA GODEWA ALLAH DA YA BANI IKON KALLAMA WANNAN LITTAFIN* *GODIYA TA MUSAMMAN GAREKI AUNTYNA AYSHA ALIYU GARKUWA* ```YABON GWANI YA ZAMA DOLE AUNTY AYSHA ALI GARKUA ALLAH YA KARO BASIRA DA HAZAKA YA KAREKI DAGA MAK'IYANKI.``` *GODIYA GAREKU K'AWAYEN ARZIK'I BAZAN* _EYSHART NA GODE DA K'AUNARKI_ _Sweetie Safiyya Dandada_ _uktee Lessy_ _Teemah nuhu_ _bestie Muneerah_ _Merry jay_ *BAN MANTA DA KUBA* Kuna bani k'warin gwaiwa _Hassana danlaravawa_ _kadeey pinky_ _ummu Fatima_ _Muneera_ _feenerh baby_ *Jinjina gareku* *Masoya novel group* *Mamyn Najmah fans* *Aysha Ali Garkuwa fans* *Tabital pulaaku* *groups din Facebook, da duk wani group da nake ciki ina mik'a godiyata a gareku na gode sosai Allah ya bar k'auna ana mugun tare🤝😍* ```Ina yiwa masoyana albishir da littafaina masu zuwa, amma saidai ku zab'i guda d'aya da zan fara yi muku a cikin guda biyu da zan bada zab'i kuma dukkanninsu true life story ne``` *WATAN UWAR MIJI* *DA* *WANI GIDA* _sai Ku zab'i guda d'aya a ciki_ *labarin WATA UWAR MIJI labari ne daya kunshi yadda wata uwar miji take gallazawa surikarta har take kishi da ita, Ku dak biyoni kuji abinda ke cikin wannan labari* *labarin WAMI GIDA labari ne daya kunshi wasu 'Ya'ya da suke yiwa mahaifinsu rashin mutunci da rashin kunya saboda bashi da kudi kuma sun samu koyarwarne daga wajen mahaifiyarsu, gefe guda kuma ga wata d'iyace da ta lalace a sanadiyyar rashin aurar da ita da kakarta ta Hana ayi* _Ku dai Ku biyoni a cikin wad'annan littattafai, kafin nan kuma sainaga zab'in Ku Wanda zab'insa yafi yawa shi za'ayi._ *sai na ji Ku BISSALAM* *by* *Mamyn Najmah* Copied By YAYA HAYAT (admin Hayat hausa novels Hausa novels and fashion Cool novel, makeup and kitchen1⃣ Cool novel, makeup and kitchen2⃣ AND Cool novel, makeup and kitchen3⃣) WHATSAPP NO:+2349030159301
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63