Chapter 23
Chapter 23
daidaita miki shi zan d'auki babban mataki akanki, ke kuma Kausar saboda zubda girma har dake ake yiwa yarinyar nan rashin mutunci ko? Ku cigaba," Kausar tayi k'asa da kai Safiyya tace "kiyi hakuri momy," harararta momy tayi tare da yin ciki. Safiyya ta kalli Kausar, Kausar tace "Safiyya dafa matsala kalli yadda momy take mana fad'a kan waccan banzar," Safiyya tace "hmm ai sainayi maganinta," Saudat ce tayi sallama ta k'araso kusa dasu ta xube a kujera tace "wash Allah wallahi na gaji, Safiyya kun jima da dawowa kenan," Ta fad'a tana kallon Safiyya, Safiyya tace "eh tun kafin Aunty su huce muka tawo," Saudat tace "kuna nan a zaune tunda kuka dawo?" D'aga mata kai Safiyya tayi tace "eh mene kike tambaya?" Saudat tad'an kishingid'a tace "kunga shigowar Hibbah? Tun d'azu da aka tashi muketa nemanta amma bamu ganta ba," harararta Kausar tayi tace "Saudat wannan wane irin maganar banzane, kinga munyi miki kama da masu gadi ne daza kizo kina tambayar mu wata banzar 'yar aiki," Saudat taji haushin furucin Kausar dama kuma ba shiri suke ba, Saudat tace "kinga dai aunty Kausar bada ke nake ba kiyi hakuri kiyi min shiru," Safiyya ta kalleta tace "ai gara ita ta tanka miki ni kina tunanin zan tanka miki ne yarinyar da a kanta momy tayi min fad'a, kuma ki fad'a mata tunda tasa momy tayi min fad'a sai tayi data sanin zuwanta gidan nan" Saudat ta buga tsaki tare da mik'ewa ta kalli Safiyya tace "aikin banza don momy tayi miki fad'a saiki huce a kanta? To bismillah," ta kalli Kausar data d'ora k'afa d'aya kan d'aya tana karka d'awa, Saudat tace "a shawarce da zaki daina biyewa wannan daya fiye miki, kinfi kowa sanin halinta matarda ko gidanta bataso aje shine kike mak'ale da ita, duk soyayyar da zata miki a gaban su momy ne kina zuwa gidanta zakiga bambanci ," tana gama fad'in haka ta hau stairs, binta da ido sukayi musamman ma Kausar tayi mamakin Saudat, kuma ta kasa cewa komai, suka kalli juna Safiyya a ranta ta yarda da kalaman Saudat don kafin aunty tayi aure saida tazo tana fad'awa momy. Ita kuwa Saudat d'akin aunty ta nufa donta duba ko Hibbah ta dawo, shiga d'akin tayi da sallama ta k'arasa kusa da Hibbah tana murmushi tace "shine kika gudo koh? Mukaje can muna ta nemanki." Hibbah tayi dariya tace"wallahi gani nayi wannan mutumin yana neman takurani ne shiyasa," Saudat ta d'an matso kusa da ita tace "Hibbah baki fahimci Ya Jabeer bane yana da halaye masu kyau ki tsaya ki fahimce sa," Hibbah ta d'an kalleta tace "kinga Saudat nifa bacci nake ji ki rabu Dani da halin mazan nan duk Wanda yazo wajenki buk'atarsa d'aya ce ya nemi jikin ki," "a'a Hibbah karki yanke hukunci" Saudat tayi saurin katseta, Hibbah tayi murmushi tare da mik'ewa ba tace komai ba ta nufi toilet ta d'an watsa ruwa ta d'auro alwala sukayi sallama da Saudat, tayi addu'o'in ta ta kwanta. Kamar yadda ta saba tashi haka yauma ta tashi, ta d'auro alwala ta zo tana ta nafilfili tana rok'on allah ya k'ara mata juriya da hakurin zama da Kausar, tana nan zaune har akayi assalamu ta tashi ta gabatar da sallah, ta d'auko Qur'anin aunty ta shiga karantawa, bayan ta idar ta d'ora da azkar har gari yayi haske sannan ta ajiye ta sauko k'asa ta nufi kitchen. Hadiza ta gani tana kiciniyar had'a breakfast, ta gaisheta suka shiga had'awa tare. Suna ta hira har suka gama suka kai dinning Hibbah ta jere kayan, Hadiza dama ta ware nasu daban ta koma sukaci sunata hira. Sama Hibbah ta koma tayi wanka ta shirya cikin wani material Orange tayi masifar kyau ta gyara fuskarta, wayarta ta d'auka tanata game har wajen sha d'aya sannan taji motsin 'yan gidan. Tana zaune wajen sha biyu Hisham ya turo k'ofa ya shigo, ya k'araso gaban Hibbah yace ""aunty Hibbah kizo inji daddy'n Nawaz," ji tayi gabanta ya fad'i duk da bata sanshi ba, mayafinta ta d'auka tasan tafiya zasuyi k'irjinta na bugawa ta fita. A parlor'n k'asa taga 'yan gidan a zazzaune harda su momy ita da mamy amma banda aunty Kausar da alama tana tare da mijin nata ko kuma tun jiya ta huce ta gaishe da su, momy tace "yauwa kije yana waje yana jiranki, ki kula da kanki Hibbah ki d'auke kanki akan duk abinda za'a yi miki, can yana da bambanci da nan kinji?" D'aga mata kai Hibbah tayi k'aunar momy na kuma shiga ranta, tace "na gode momy allah ya saka da alkhari," momy tace "ameen Hibbah," mamy ta kalli su Safiyya tace "ku tashi Ku rakata mana," Saudat ce ta fara mik'ewa taja hannun Hibbah suka fita, ita kuwa Safiyya dama danna wayarta take yi data fito ma cigaba tayi da abinta. A mota suka tarar dashi motar a bud'e shi kuma ya zuro kafarsa d'aya waje yanayiwa Nawaz wasa, suka k'araso wajen inda yake suka gaishe shi ya amsa tare da d'agowa ya kalleta, ji tayi gabanta yayi wata muguwar fad'uwa ganinsa tayi kamar Faruq komai nashi irin na Faruq bambancinsa da Faruq kawai girmane amma hatta maganarsu ma iri d'aya ce. Ya kalli Nawaz yace "boy shiga mota mu tafi gida," yaron d'an kyakykyawa yace "to daddy," ya kalli su Saudat yace "Aunty Saudat wace wannan?" Saudat tayi murmushi tace "sunanta aunty Hibbah," ya kalli Hibbah yace "aunty Hibbah," Hibbah ta kalleshi tana murmushi. Ya kuma kallon Saudat yace "aunty Saudat aunty Hibbah tana murmushi don na Kira sunanta," Faheem ne ya katseshi da cewa "Nawaz ka shiga mota mu tafi mana," da sauri yaron ya juya ya bud'e motar tare da shiga yana yiwa su Hibbah murmushi, Saudat ma ta bud'ewa Hibbah gidan baya ta shiga sukayi sallama, Faheem ya tashi motar suka huce. Safiyya na ganin sun tafi ta komawarta gida dama ita Danna wayarta take. A mota Nawaz sai surutu yake tayi shi kad'ai, yace "daddy aunty Hibbah gidan mu zamu da ita?" Faheem dayake tuk'i yace "eh Nawaz ita zata dinga zama tare da kai idan ka dawo daga school, tayi maka wanka ta koya maka homework ta dafa mana abinci," Nawaz jin ya ambaci homework yasaki ihun murna "yeeeh daddy nima na samu aunty," ya juyo yana kallon Hibbah yace "aunty Hibbah har unguwa zaki dinga zuwa dani momy na bata zuwa unguwa dani wai nayi girma, ai banyi girma ba ko aunty?" Hibbah ta d'aga masa kai tana murmushi tace "eh Nawaz zan dinga zuwa dakai," lokaci d'aya taji k'aunar yaron ta shiga ranta, shi kuwa Nawaz cigaba yayi da wasanshi har suka k'araso gidan Mai gadi ya bud'e gate d'in gidan yana yiwa Faheem sannu dazuwa. A parking lot ya ajiye motar suka fito, Faheem yayi gaba shi kuma Nawaz ya zo ya rik'e hannun Hibbah suka parlor yana ta yi mata surutu. Suna shiga suka tararda Faheem a parlor yana k'ok'arin kunna TV, bai kallesu ba ya kunna TV ya dawo ya zauna yana kallon labarai, a k'asa Hibbah ta zauna Nawaz yana kan cinyarta, Faheem yad'an kalleta kad'an ya kawar da kansa yace "Hibbah sunanki ko?" Hibbah ta d'aga kai "eh" yace "Hibbah aikin ki a gidan nan shine girki,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63