Chapter 33
Chapter 33
mata don ganin wajen aiki zata tafi, azaton shi yau dai zata zauna ta kula da d'anta domin lafiya tafi kud'i, mai makon ma ta dafo wani abu da tasan mara lafiya zai buk'ata ta kawo musu sai tazo musu k'iyau miyau. Sai takardu a hannu sai kace wadda zata kadance kundin ilimin duniya, shi yasan duk wannan aikin da take yi d'anta ya fishing daraja a matsayinta na 'ya mace bata da abinda yafi d'anta mahimmanci a wajenta. Ta dubi agogo "Zan wuce wajen aiki su momy suna zuwa da abinci munyi waya da Safiyya," ko kallon ta bai yi ba "basu da hakkin bani abinci wannan aikinki ne ba nasu ba kuma baki damu ba zaki tafi uzurinki, akwai ranar k'in dillanci, shiyasa wasu 'ya'yan sam basa tausayin iyayensu kuma ba komai ke janyowa ba sai irin wad'annan abubuwan, baka san wahalar d'an daka haifa ba, shi zaiji k'anka bayan ke ba haka iyayenmu suka yi miki ba," ta d'aga mishi hannu cikin hayayyak'owa "bafa tsoranka nake ji ba da zaka dinga fad'amin abinda kaga dama, ka fad'amin ayar da tace don ka aure ni na ciyar dakai cewa akayi a ciyar dani, kuma ni haka tsarina yake bazan canza ba," "ke kuma akace kimin biyayya don ki samu aljanna to idan na nemo abinda Zan ciyar dake yana cikin biyayyar aure ki dafa min, to don haka ki kiyaye yimin ihu aka kinsan ni ba sa'anki bane sannan a k'ark'ashi na kike kin gane koh?" A fusace ta fita, ya cije leb'e wato yayi shi kad'ai ita bazata saurareshi ba. Duk iyalan gidan sunzo momy, daddy yake yana gari da Faruq su Saudat suna makaranta shiyasa basu zo ba, suna zuwa Faheem yace zaije ya d'an kintsa a gida, momy tayi mamaki da Faheem yace mata wai Kausar ta tafi aiki. Da yamma ya kasa jurewa ya nemo number Aysha, ringing biyu ta d'auka bayan sun gaisa tace "Dan Allah yaya kayi hakuri ina tafe an jima zan shigo ya jikin boy d'in nawa?" "Karki samu damuwa da sauk'i sosai," "to harna ji dad'i Allah ya k'ara sauki, yauwa yaya don Allah ina son ganin Hibbah zamu d'an tattauna akan maganar Jabeer wallahi ya dameni yana so a yi auren nan kasan wajen aikin mu d'aya," Gaba d'aya ji yayi wani abu mai Kama da bugun guduma a tsakar kansa, ransa babu dad'i yayi ajiyar zuciya wani abu na nuk'urk'usar zuciyar sa, "yaya kana jina dai ko?" "Hmmm ina sauraronki, bata nan taje gida ne kwana biyu bata dawo ba bansani ba ko lafiya, bani address d'in gidan nasu," "Oh to Allah yasa lafiya don nima ban nemeta ba kwana biyu, ai gidan Alhaji sani ne gidan nasu fa," "Alhaji sani dai wanda na sani?" Faheem ya tambaya "eh shine yaya," sukayi sallam. Sai ya samu kansa da............ *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:24 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page3⃣4⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION* D.B.W.A *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* ```Tabital pulaaku group ina kuke? Wannan wannan page d'in d'ungurungun nakune, Allah ya barmu tare cikin so da k'aunar junanmu.``` Sai ya samu kansa da kasa samun nutsuwa sai yaje gidansu Hibbah don gaskiya yana so yaga Hibbah, dayake har lokacin momy na nan sai yace mata yana zuwa ya zari key ya fita, direct gidan Alhaji Sani ya nufa, Alhaji Sani ya tare shi suka shiga cikin parlor babu kowa cikin mutumci suka gaisa sosai Alhaji yana tambayarsa ya iyali, suka d'anyi shiru na wasu 'yan dak'ik'u Alhaji yana mamakin zuwan Faheem gidan sa ko Alhaji ne ya turosa ya kasa jurewa yace "Faheem Alhajin ne ya turo ka?" "A'a dama ina sone mu gaisa da Umma tana nan ne?" Alhaji yayi murmushi "to to naji dad'i bara nayi mata magana tana d'aki," Alhaji ya mik'e ya shiga d'aya daga cikin d'akunan cikin parlor'n, jim kad'an sai ga su sun fito shi da umman, Alhaji sukayi sallama da Faheem don shi fita zaiyi. Faheem ya zamo daga kujerar da yake zaune ya durk'usa har k'asa ya gaishe da Umma ta tambaye shi Kausar da Nawaz (ta tab'a ganinsa ne a hoto da Aysha ta nuna mata shi). Yace "wallahi kinga ma shiya taso ni nazo don baijin dad'i ne, kuma ya damu da Hibbah don ciwon da sauk'i akan damuwar," Umma tayi murmushi "Allah sarki bamu sani ba ai da anje an dubo shi Allah ya Bashi lafiya, bawan Allah haka so yake gamuwar jini, badai abinda zamuce muku sai fatan alkhari, Allah ya biya da aljannah," yayi Jim wani abu ya tab'o zuciyarsa yaji dad'in kalaman Umma, yana son ta tashiga ransa sai yaji don me bazai fad'a mata damuwarsa ba damin a maganarta ya fahimci bata da masaniya akan abinda ya faru har Hibbah tayo musu yaji. A nutse ya fad'awa Umma komai abinda ya kasance har yajin da Hibbah tayi musu na tawowa ba tare da saninsa ba, Umma ta kad'a kai "ikon Allah wallahi bansani ba ni nan b'oye min tayi bata fad'a min ba cemin tayi kunyi tafiya ne ni kuma nasan bata iya k'arya ba kuma Allah bai nufa munyi maganar da Alhaji ba, kai amma banji dad'i ba kuma bata kyauta ba. Ita d'in me tafi k'arfin ayi mata fad'a ne idan tayi badai dai ba ka tsawatar mata wannan shine tarbiya, wato tasan idan ta fad'a zanyi mata fad'a shiyasa b'oye tak'i fad'a min, don Allah kayi hakuri," Faheem sai yaji wani iri kamar Umma da girmanta da k'amarta ta dinga Bashi hakuri "a'a Umma babu komai wallahi," wadda take yiwa Umma share share ce tazo d'aukar abu Umma tace ta turo mata Hibbah, sai gata kuwa tana ganinshi tayi turus, zuciyarta tana bugawa kamar zata tarwatse ko a mafarki bata tab'a tsammanin shi ba, ta zube "ina yini Daddy," ya dubeta ya had'e fuska "bazan amsa ba Hibbah tunda nayi fad'a kikayi fushi har kika tawowarki gida bako sallama, kin bani girma kenan? Gashinan kinsa yaronki rashin lafiya yana asiiti kin kyauta kenan?" Ta dubeshi a razane hantarta har ta kad'a ta had'iyi miyau dak'ar idanunta sun cicciko hawaye, Nawaz Allah sarki dama tasan za'a rina bata yi masa adalci ba, ita ma tana nan har d'an zazzab'i tayi shak'uwarsu tayi yawa ita da Nawaz, Allah sarki sak taji tausayin yaron da k'aunarsa na kuma shiga ranta. To yaya zatayi idan ba ta barwa Faheem gidansa ba don yayi mata hannunka mail sanda. Umma kuwa ta rufe ta da fad'a "ni ban san sanda kika koyi k'arya ba halin hofi Hibbah don me baza'a fad'a miki kinyi ba dai dai ba kinfi k'arfi a tank'wara kine, to ki shiga hankalinki idan ka rasa mafad'i a duniya ka shiga uku, wad'annan mutanen sunan k'aunarki mutunan da suka d'aukekan tamkar d'an uwa na jini suke d'awainiya dakai, tun wuri ki sauya tunani ni ban goyi da bayan ki raina na gana da ke ba d'an halak baya manta alkhari, wallahi kar na kumaji kinyi irin wannan shirmen kuma ki d'auki kayanki ki koma, ki bashi hakuri yanzu," Zuciyarta tayi rauni jinkinta yayi sanyi ganin ran Umma ya b'aci sosai gashi tana ta yi mata fad'a abinda bata tab'a yi mata ba, da k'yar muryarta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63