Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 3

Chapter 3

Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Kuma tasan tunda Rahmatu ta ganta tasan saita fadawa Inna. Hibbah tace "to idan na karba yazo da daddaren kuma ba canji fa?" Abu tace "karki damu saina anso mana wajen gwaggo nasan tana da canji" Hibbah tace "to shikenan idan zamu tafi na amsa" mikewa Abu tayi tare da cewa "tashi mu tafi alalan ya kare ai" mikewa Hibbah itama tayi ta dora farantinta aka sannan ta karasa kusa da inda sale yake tace "Zan tafi gida ka samo canjin?", "ban samu ba gashi na amsa ko gobe ne idan yau banzo dandalin ba" sale ya fada yana kuma kallon girjinta tare da miko mata kudin. "Ni dai wallahi babu ruwana idan na kaiwa Inna kudin tace baza ta bada canji ba" ta karba kudin, shi kuwa sale ya sha'afa da kallon lips dinta, jin bai amsa ba ta kalleshi tace "kadai ji Na fada" sale yace "ai ba komai saina fanshe" kallon mamaki Hibbah tayi masa tace "ka fanshe da me" cikin sauri yace "a'a ina nufin bakomai idan ma ta hana canjin." Juyawa tayi taja hannun Abu suka tafi, muryar sale sukaji yana cewa "saina zo" basu waiga ba suka yi............. *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:21 PM] Maman Najma Author P1: ๐Ÿ“๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡ *RAYUWA* page6โƒฃto7โƒฃ *NA* *MAMYN NAJMAH* ๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡ *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* *ุงู„ู„ู‡ ุงูƒุจุฑ ุงู„ู„ู‡ ุงูƒุจุฑ ุงู„ู„ู‡ ุงูƒุจุฑ* *ู„ุงุงู„ู‡ ุงู„ุง ุงู„ู„ู‡ุŒ ุงู„ู„ู‡ ุงูƒุจุฑ ุงู„ู„ู‡ ุงูƒุจุฑ ูˆู„ู„ู‡ ุงู„ุญู…ุฏ* *ุงู„ู„ู‡ ุงูƒุจุฑ ูƒุจูŠุฑุง* *ูˆุงู„ุญู…ุฏ ู„ู„ู‡ ูƒุซูŠุฑุง* *ูˆ ุตุจุญุงู† ุงู„ู„ู‡ ุจูƒุฑุฉ ูˆ ุงุณูŠู„ุง* _*Ina bawa mabiya littafin RAYUWA hakuri kasancewar yau zan dakata da yin typing sai bayan sallah idan Allah ya kaimu zan dora, allah yasa muyi sallah lafiya mugama lafiya.*_ _*Au na manta da sakon Aunty na ban fada muku ba, Aunty AYSHA ALIYU GARKUWA tace bayan sallaha karku manta ku tawo mata da nata naman๐Ÿ˜œ.*_ Haka Hibbah ta yini tana kuka da tunanin yarda zata cigaba da *RAYUWA* a gidannan cikin wahala da ukuba. Sallah ce kawai ta tasheta daga inda take, alwala tayi tai sallar azahar sannan tayi la'asar kasancewar taji anata kiraye kirayen sallah bayan ta idar ta zauna ta rika kwararo addu'a tana kaiwa mai sama kukanta, addu'a take yi amma hawaye na zuba a idanunta. KO abinci ranar bata iya ci ba saboda tsantsar damuwar dake damunta na rabata da mahaifiyarta gatanta da akayi. Umma kuwa suna zuwa gida Yaya Habu ya fadawa su gwaggo komi, sun firgita kwarai dajin kazafin da akayiwa 'yar tasu, ko kadan saki bai daga musu hankali ba saboda sunsan yanayin halin da 'yar tasu take ciki a gidan mijin nata. Kuma sun goyi bayan Yaya Habu daya tafi da ita cen Bunkure din zatafi samun nutsuwa sannan data gama iddarta idan Allah ya kawo miji tayi aurenta. Nan sukayi musu sallama suka huce. Da daddare bayan sallar isha'i Hibbah na kwance a dakin ummanta zazzabi ya rufeta sai rawar dari take yi. Rahmatu ce tashigo dakin tana cewa "ke Hibbah kije sale driver na kiranki, cikin rawar baki Hibbah tace "Dan allah Rahmatu anso masa canjinsa wajen Inna, zazzabi ya rufeni bazan iya tashi ba." Harararta Rahmatu tayi "lallai ma ni zaki aika? Shima din abinda yasa kika nazo kudi ya bani amma badan haka ba babu inda zani, mtwss" ta karasa maganar dayin tsaki tayi ficewarta. Tana fita dakin Inna ta shiga tana shan rake bako sallama ta haye kan gadon innar ta cigaba da shan rakenta, inna ta kalleta tace "me sunan baba me kike shane haka?" Shiru Rahmatu tayi bata amsa ba ta cigaba da shan raken. Inna ta kalleta tace "au saboda kar nace ki sammin shiyasa kikayi min shiru koh Rahmatu?" Cikin gajiyawa da maganar Rahmatu tace "ai dama nasan sai kince na sammiki bayan kuma kena fara cewa ki bani kudi na siya kika hanani" ta fada tana kuma gyara zamanta akan gadon innar. Cikin yanayin lallashi Inna tace "haba me sunan baba ai ina baki kina siya, ki sammin kadan zansha." Turo baki Rahmatu tayi tare da mika mata tace "to gashi nan karki sha min dayawa, inkika sha da yawa allah saikin sai min wani," inna ta amsa tana cewa "bazan ma sha da yawa ba." Bantara tayi tasha zata kara, Rahmatu tayi saurin cewa "wallahi inna kika Kara saikin sai min sabo" mika mata inna tayi tana cewa "ai raken nakine akwai zaki, wa ya baki kudi kika siya?" Bata kalli inna ba tace "Sale direba ne yazo wajen Hibbah, shine zan shigo ya ganni yace na kira masa ita nace bazani ba shine ya dauko hamsin ya bani." Inna ta gyara zama tace "wai mene a tsakanin su ne dazuma kince ya bata Dari biyar a kasuwa, don ya barar mata da abinci kuma nidai nasan abincin dana dora mata na dari uku ne. Kinga kudin ma data zo tana ta uwarta bata ma yimin bayani ba ta bani kudin duka." Rahmatu tace "toni ina Zan Sani ni dai nasan kawai yana yawan kulata ko kuma yace zai tabata ita kuma ta haushi da masifa." Tana gama fadin haka ta mike tare da cewa "ni na tafi dandali" inna tace "sai kin dawo amma kafin ki tafi ki shiga ki kira min wannan shegiyar yarinyar tana nufin dan uwarta tabar gidan shine yau bazata fitar min da gyadata ba." "Inna tana can bata da lafiya" Rahmatu ta bawa inna amsa tana fita daga dakin. Murmushin mugunta inna tayi tare da bin bayan Rahmatu. Shi kuwa sale ganin Hibbah bata fito ba yasa ya zauna zaman jira don yasan dole zata fito da gyada. Yana nan zaune yaga Rahmatu ta fito ya kalleta yace "Rahmatu ina Hibbah din?" Kallon shi tayi adan wulakance tace "tana ciki wai bata da lafiya" tana fadin haka tayi gaba. Shiru yayi yana nazarin koya shiga cikin gidan, yana kuma tsoran kar a kamashi don yasha alwashin yau dinnan saiya dan dani zumar Hibbah. Inna ce ta katseshi da cewa "sale Kaine a kofar gidan namu?" Dan sosa keya yayi ya shiga gaishe da inna tare da cewa "nazo karbar canjina ne a wajen Hibbah na dazu dana bar mata". Inna jin anyi batun canji yasata murtuke fuska ta fara masifa "wane irin canji kuma?" Dan sunkuyar dakai sale yayi tunda yasan shi yake nema yace "eh dama dazune na zubar mata da abinci a kasuwa kuma na bata Dari biyar babu canji shine nace zanzo Na amsa." Dariya inna tasa harda tafa hannu tace "hmm yaro man kaza sale mene na boye min ni mai taimaka maka ne ka samu abinda kake so a wajen Hibbah, nasan komai kuma Zan taimaka maka ka samu Hibbah a Daren nan ma idan kana so amma da sharadi." Wani irin happy ne ya rufe sale cikin sauri yace "wane sharadi ne xan bishi matukar zan sami Hibbah" dariya inna ta kumayi tace "sai naji dumus a hannu" ba musu sale ya dauko 'yan dari bibbiyu ya irga guda shida ya bawa inna, inna ta amsa ta irga wani kallo ta bugamai tace "dubu daya da dari biyu ne fa kana tunanin wannan yakai darajar abinda zaka samu?" Cikin sauri ya kuma irgo guda hudu ya mika mata. Karba tayi tana ganin hudune cikin zafin nama ta warce sauran na hannunshi ta hada. Tace "kazauna anan

Table of Contents

Chapters

63 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});