Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 31

Chapter 31

Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ba wai don ka nuna min kuskure na ba, bani da Kalmar yabo da godiya a wajenka na gode da kyautatawar da kayi min allah ya saka da mafificin alkhari. Ka bawa Nawaz hakuri ka rarrasar min shi Nina zanji ciwon rashin Nawaz!" "Bissalam, daga Hibbah._ Ta goge hawayenta ta ninke takardar ta ta shiga d'akinsa don baya kullewa saboda kullum sai ta gyara mishi d'akin, ta d'ora akan pillow, ta fito tare da kulle gidan. Ta doso gate d'in ta hango Isah yana washe baki ya k'araso yana cewa "yau tafiya zakiyi kenan wato kinyiwa wazirin naki wayo, amma fa yau mai gida zaisha fama," tayi murmushi "ai bazan dad'e ba kwana biyu zanyi kawai," "to Allah ya kaiki lafiya bari na d'aukar miki jakar," ya d'auki jakar suna tafe suna hira har suka yi nisa ta juyo ta sake kallon gidan, ko zata kuma zama a gidan ko kuma kallon k'arshe take yi masa, kai bata jin zata kuma sake dawowa gidan ko da wata rana ne, ta goge k'walla don kar Isah ya gani, ya tsaida mata adaidaita sukayi sallama ta d'auko dari biyu ta bashi yayi ta godiya, yana d'aga mata hannu "a sauka lafiya," Da rana tunda Nawaz ya dawo Isah ya tareshi suna zaune a benci yana ta janshi da wasa shi kuwa duk ya shiga damuwa yana ta damun Isah wai har yanzu aunty Hibbah bata dawo ba, haka Isah yayi ta biye masa har Faheem ya dawo da yammaci lik'is yayi mamakin ganin Nawaz a bakin get da uniform a jikinsa. Da gudu yaje ya rumgume shi tare da zubar da jakarsa, yana ajiyar zuciya cikin murya mai sanyi yace "daddy aunty Hibbah bata dawo ba har yanzu," ya dube shi a nutse kamar ya sokeshi da mashi "bata dawo ba?" Ya nanata a cikin ransa, tuni ya soma wani zargin ya d'auki jakarsa yana lallamin Nawaz "karka damu my son yanzu zanje na d'aukota a wajen aiki," ya gyad'a masa Kai. Isah ya rugo da gudu ya kawo masa mukulli, ya karb'a ba tare da yayi magana ba. Ya bud'e gidan suka shiga m, tsit parlor'n babu motsin Hibbah daya saba ji da k'amshin girke girkenta, lallai mutum ma a guri rahama ne, tun anan yaji wata kewarta da kad'aicin Hibbah, Wanda ko Kausar matarsa bai tab'a jin hakan ba akanta ba, ko dan ta horesu ne da rashinta oho. Ya dafe goshinsa ga mamakinsa sai ya rasa meke masa dad'i babu shakka Hibbah tafiyarta tayi tunda har ta bada ajiyar mukulli, don bata tab'a tafiya wani wajen ba tare da izininsa ba, sai dai ko idan Jabeer ne yazo kuma idan ya dawo yakan iskesu a waje, to amma me yasa bai tab'a d'aga hankalinsa ba kamar na jiya kodan ya ganta da wannan d'an iskan Sadeeq ne. Ya shiga d'akin yana bin ko ina da kallo babu wata alama da zai nuna tana nan ba tafiya tayi ba, yayi ajiyar zuciya, ashe Hibbah bata da hankali tana nufin ta bar gidan kenan ita mai zuciya saboda 'yan iskan samarinta, sai taje a sauka lafiya shi dai ba zai iya d'auka ba. Ya shiga toilet ya watsa ruwa sanyin ya ratsa shi, ya fito ya shirya ya d'an kwanta yana d'ora kansa a pillow yaji wani abu a Kai, ya lalubo takarda ce ya k'ura mata idanu shi dai yasan bai ajiye takarda ba, ya bud'e yana nazari. Lumshe idanu yayi daya kai k'arshe, Hibbah, zuciyarshi tana bugawa komai ya rikice masa, Hibbah abin har yana Bashi mamaki da al'ajabi, ya fito waje ya yafito Isah, da sauri ya taso. "Ranka ya dad'e," "am yaushe yarinyar nan ta tafi ne?" "Bayan kun fita ne tace min kwana biyu zatayi harma ta bani d'ari biyu ranka ya dad'e," ya kad'a kai "shikenan kawai dama bansan da tafiyar bane." Ya shiga motarsa tare da barin gidan, wai meke damunsa ne? Duk ya rasa nutsuwarsa, yanzu ina tafi neman Hibbah bayan ta yankewa kanta hukunci, kawai kalamanta ne suka karya masa zuciya, haka kawai zai dami kansa sai kace Wanda yasha k'awa? Yayi tsaki tare da juya kan motar ya koma gida. Ita kuwa Hibbah tunda taje gidan Umma bayan sun gaisa ta kasa komai bata da wata nutsuwa, Umma ta fahimci hakan a tattare da d'iyar tata, "Hibbatullah ganinki nayi tafe da kayanki, ko dai wani abune ya faru hankali na ya tashi," ta maida k'wllar da ta tawo mata don kar Umma ta gani tace "ba komai Umma sunyi tafiya ne su duka shiyasa nima na tawo nan, Umma Jabeer da gaske yake fa," ta fad'a mata yadda suka yi dashi. "Wannan aniyace mai kyau Allah ya tabbatar mana da alkhari zan fad'awa Alhaji, kuma kije ki shawarci Auntyn ki don mai k'aunarka har a bada ya gama yi maka komai kuma ta b'angarenta yaron nan yazo ta san komai game dashi," wayarta ce tayi ringing Jabeer ne sai taji zuciyarta tad'anyi sanyi ta mik'e tana satar kallon Umma, Umma tayi dariya "wayar sirikin nawane dai na sani" ta fita tana murmushi ta kara wayar a kunne "tunaninki nake yi na k'osa muyi aure wallahi, yaya alkawarinmu kun tattauna da Umma?" "Uhm yanzu maganar da muke yi kenan da ita ta sanya albarka amma tace zata fad'awa Alhaji," ya d'anyi murmushi "naji dad'i kuma nasan insha Allah akwai nasara zasu bani goyon baya, Hibbah in dai na sameki burina ya cika ki saurare no da yamma zanzo," "to amma ina gidanmu bara zanyo maka text message na kwatancen unguwar," "ok na gode ki gaishe da Umma," da haka sukayi sallama. Tana ajiye wayar kiran fauzy ya shigo tana d'agawa ta fara yi mata masifa "haba Hibbah dama kinsan bazaki je school ba yau kuma jiya kika k'i bari mu k'arasa wannan physics d'in," "no fauzy ba haka bane ina cikin matsala ne ni kaina bansan bazan zo ba, yanzu haka ma ina gidan Umma," ta maimaita "kina gidan Umma? Mai ya faru?" Nan Hibbah ta kwashe komai ta fad'a mata, fauzy tace "amma wannan mutumin anyi d'an iska, kinsan Allah ya taimake mu ba jiya bane don yau aka kamasa da wannan d'alibar tasa Dana ke fad'a miki yanzu maganar da nake miki ma an mik'ashi kotu gobe za'a fara Shari'a," Hibbah cikin razana tace "garin yaya fauzy?" "Hmmm ai in fad'a miki zuwa yayi school d'insu d'aukota, ashe vice principal yaga lokacin da suka fito da ita a mota, suna fita yaje ya fad'awa principal shine fa suka d'auko masa police suka biyoshi ana zuwa office d'inshi aka gansu suna aika aika," "tab to allah ya shirya" fauzy tace "ameen ya goben amma zaki shigo ko?" "In allah ya yarda" "To shikenan nan ki gaida su Umma," da haka sukayi sallam.................. *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:24 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page3⃣3⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION* D.B.W.A *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* *Wannan page d'in naki ne Surbajo tawa ban manta dake ba kina raina Allah raba ki da mak'iya, kinfi k'arfin duk wani mai hassada💪* Yayi d'an tsaki ya ture plate d'in gefe, cikin kwanki biyar kacal da yajin aikin Hibbah ya ritsa da kowa na gidan komai ya tsaya cak, sai mutum

Table of Contents

Chapters

63 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});