Chapter 4
Chapter 4
idan kaga malam ya shigo sai kabi bayansa zakaga wani karamin daki dayake kallon dakin dazai shiga amma yayi nisa sosai da wanda zai shiga to tana ciki saika shiga." Sale cikin happy yace "to amma ummanta fa?" "Ummanta bata gidan" tana kaiwa nan tayi shigewarta cikin gidan cike da murna. Ya kalli Hibbah yana dariyar keta, ita kuwa mugun tsoro ya bata cikin Sauri ta tashi zaune tana ja da baya. Binta ya shigayi shima, mikewa tayi dakyar ta shiga yin baya batason tazo bakin gadon ba sai ji kawai tayi ta fada kan gadon. Murmushin mugunta sale yayi yace "kin rage min aiki." Hawaye ne ya fara sintiri a fuskarta tana yin baya har taje karshen gadon. Hayowa gadon yayi yana murmushi, cikin kuka tace "don allah sale kayi hakuri karka rabani da muyuncina darajata don allah ka kyale...." Dariya yasa yace "wallahi Hibbah yau ba mai hanani kusantarki garama ki nutsu mubi komi a hankali idan ba haka ba kuma zanyi ta karfi Wanda ni zanfi son hakan." Kifa kanta tayi a tsakanin cinyoyinta tana karanto kowacce addua tazo bakinta. Kayan jikinsa ya cire ya wurgar daga shi sai trouser ya tunka rota............ *by* *MAMYN NAJMAH* [10/26, 9:21 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *RAYUWA* page 4⃣to5⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* *الله اكبر الله اكبر الله اكبر* *لا اله الله، الله اكبر الله اكبر و لله الحمد* *الله اكبر كبيرا* *والحمد لله كثيرا* *و صبحان الله بكرة و اسيلا* Sukayi tafiyarsu suna hira Hibbah tace "Abu wallahi akwai wani abu da yake bani mamaki da tsoro" kallon mamaki Abu tayi mata tace "wane abune wannan Hibbah?." Numfashi Hibbah ta danja tace "Abu kusan kullum sai nayi wani mummunan mafarki, wai Inna tasa baba ya kori umma daga gidan ni kuma ta biyoni da gudu da wuka a hannunta zata kasheni, sai wani balarabe Wanda ban taba ganinsa ba ya kwaceni a wajenta. Ita kuma ya jefata cikin wani katon rami me dubu idan ya jefata sai naga baba yaxo ya rumgume ni yana cewa na yafe masa" ta karasa maganar cikin tsananin damuwa. Abu tadanyi shiru tana nazarin kalaman Hibbah kafin tace "idan har hakan zai kasance gaske toda munfi kowa murna, mafarkin ki yana nuna nan gaba wani zai taimakeki ya ceto baba daga sharrin Inna. Amma abinda bangane ba shine korar umma da kikace Inna tayi daga gidanku." Cikin damuwa Hibbah tace "Abu nima abinda nake ta tsoro da wannan mafarkin da nakeyi kenan kar fa ya kasance gaskiya." "In allah ya yarda bazai kasance gaskiya ba, Umma tasan kina wannan mafarkin?" Abu ta tambaye ta, girgiza kai tayi tare da cewa "a'a bata sani ba" Abu tace "yakamata ki fada mata wata kila ita ta fimu fahimtar mafarkin naki" "hakane idan na koma zan fada mata" Hibbah ta fada. Suka cigaba da tafiya suna dan hira jefi jefi. Farantin kantane ya subuce ya fadi kasa robobin suka tarwatse, bata damu da faduwar da sukayi ba sai kirjinta data dafe da hannu saboda bugun da yake yi mata. Kallon mamaki Abu tayi mata tace "lafiya Hibbah?" Cikin tsantsar tashin hankali Hibbah tace "wallahi Abu ji nayi gabana yayi wata mummunar faduwa kirjina na bugawa da Sauri sauri," Abu tace "to allah yasa lafiya," Hibbah tace "ameen" tare da sigunnawa tana tattara robobin Abu na tayata. A can gida kuwa bayan umma ta sauke tukunyar daga kan murhu ta dauki tukunyar takai kofar inna tare da cewa "Inna gashinan na gama." Inna Na cikin daki bata ce mata komi ba tayi banza da ita. Umma ta saba da hakan don haka bata damu ba taje daki ta dauko roba ta ajiye a kusa da tukunyar. Buta ta dauka ta shiga bayan gida ta fito ta daura alwala ta shiga daki, sallah tayi bayan ta idar ta zauna tana kaiwa ubangiji kukanta, bayan ta shafa ta zauna ta cigaba jan carbi. Muryar malam taji yana kwalla mata kira cikin fada "ke Aysha, Aysha ina kike fito munafika maci amana." Cikin sauri Umma ta fito tana cewa "malam lafiya.........?" Bata Ankara ba taji saukar yatsun malam a fuskarta. Rike kuncinta tayi tace "malam me nayi don Allah ka fada.........." Kuma katseta yayi da wani gigitaccen mari Wanda yayi sanadiyyar faduwarta kasa, binta yayi ya cigaba da dukanta baji ba gani yana binta da muggan kalamai "Allah ya isa tsakanina dake Aysha bazan taba yafe miki ba, kin cuceni kuma sai kinga sakayya, ki rasa dame zaki saka min saida bin maza" yaci gaba da dukanta. Lami wadda taji duk abinda ya faru tana daki tanata dariya domin kuwa tarkonta ya kama malam, da gudu ta fito daga dakin ta karaso kusa da malam tana cewa "haba malam dukan mace kamar wani mara hankali me tayine malam?" Bai saurareta ba ya cigaba da bugunta. Itako Aysha ganin babu mai cetonta yasa dakyar ta mike ta koma dakinta da gudu. Yana kokarin binta malam Habu wan Aysha daya shigo ya tareshi da sauri "haba malam Mukhtar me yayi zafi haka dukan matarka da hannunka? Da hankalinka kake dukan mace ai fada ya dace kayi mata ba duka ba." Mugun kallo malam Mukhtar yayi masa yana cewa "eh ai dama dole kace nayi mata fada tunda kanwarka ce koh? Kuma na tabbata kasan irin tarbiyyar da kuka bawa 'yarku don haka kadau keta ku tafi na saketa." Ba malam Habu kadai ba har umma dake daki saida ta tsorata, ta fito a rikece tana kallon su malam Habu yace "saki fa kace malam Mukhtar me yayi zafi haka? Ai idan tayi maka wani laifi ni ya kamata kasamu sai mu magance matsalar a sasanta komai, bawai kadinga dukanta ba daga karshe kuma kace ka saketa ba" malam Mukhtar ya kalleshi cikin bacin rai yace "a sasanta me? Ai babu a abinda za'a sasanta kawai ka dauki fasikar kanwarka ku barmin gida" cikin mamaki Umma ta dafe kirji tace "fasika fa kace malam, Inna lillahi wa Inna ilaihirra ji'un allahumma ajirni fi musibati wa akhlifnii khairan minha." Umma ta fada cike da damuwa, malam Habu ya kalleta ya kalli malam Mukhtar yace "Mukhtar fasika fa zina fa kenan, ka nufin matarka na aikata zina? Ka ganta da idanunka ko kuwa zargi kakeyi Mukhtar?" Cikin hayayyakowa malam Mukhtar yace "eh ai dama baza kaga laifinta ba tunda kanwarkace jininka ce, ni dai na gama magana ka dauki kanwarka Ku barmin gida". Lami data nuna damuwa a fuskarta a badini kuwa ta shiga tsananin farin ciki tace "fasika malam gaskiya bazan boye maka ba don ko jiya naga inuwar wani katon mutum da daddare ni wallahi dana ganshima ba karamin tsoro naji ba ashe gurinta yake zuwa" malam Habu kallonta yake cikin mamaki yake kallonta, ita kuwa umma rushewa tayi dawani kuka mai ban tausayi tana cewa "wallahi malam sharri akayi min tunda nake ban taba aikata zina ba kayi bincike kafin ka yanke hukunci......." Katseta yayi da cewa "wane bincike zanyi bayan gashi nasan gaskiya babu wani bincike da zanyi kawai ki fitar min a gida na sakeki......." Furucin malam yayi daidai da shigowar Hibbah, sallama tayi amma babu wanda ya amsa ta kallesu dukansu basa cikin nutsuwa. Lami tadanyi murmushi tace "malam Saki nawa kayi mata?" Malam
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63