Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 51

Chapter 51

Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ta tambayemu lafiyar Aysha da munyi niyyar b'oye mata saboda yanayin ciwonta amma Faheem yayi caraf ya fad'a mata Amminsa ta rasu don haka suke kiranta. Nan fa jikin hajiya ya kuma tashi Dr da yaga jikinta ya dinga fad'a itama a lokacin tace ga garinku nan. Nan fa muka kuma shiga damuwa Rukayya da momynku suka fad'i a wajen a sume hankalinmu ya kasa kwanciya nida Abban Ku. A tak'aice dai haka ranar muka yini cikin zulumi da rud'ani, washe gari muka tawo da gawawwakinsu hajiya gida abinda muka samu a gida yasa nima saida na ziyarci asibiti don nima ban tab'a tunani zan kuma rayuwa ba don zuwa mukayi kuka tadda Mukhtar ya b'alle k'ofar ya bar gidan. Abbanku shine yayi k'arfin zuciya yasa akayi musu sallah aka kaisu makwancinsu, ni kuma yasa aka kaini asibiti shi kuma ya zauna da sauran dangi suna karb'ar gaisuwa. Bayan na samu sauk'i munyi cigiya a gidan radio dana TV amma bamu samu Mukhtar ba haka muka hakura muka mikawa Allah lamarin, abinda ya bamu mamaki ko da wasa Ibrahim bai zo mana gaisuwa ba balle yayi mana jajan rashin d'an uwanmu. Ni na d'auki Aysha yarinyar Mukhtar na cigaba da rik'onta." Daddy yasa tissue ya goge hawayen daya zubo masa, sauran matan ma duk kuka sukeyi musamman su mamy ji suke mutuwar ta dawo musu. Cikin kuka harda majina Hibbah tace "Daddy wace Aysha da Ammi ta bari?" Daddy ya d'ago ya dubi duk 'yan d'akin "kuyi hakuri yauzan bayyana duk wani sirri da muke b'oyewa, Hibbah Ayshan da aka haifa ba kowa bace illa............. *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:27 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page4⃣7⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* Ba kowa bace illa Auntynku Aysha, itace wadda amminku ta rasu ta barta, ni kuma na d'auketa momynku ita ta shayar da ita kuma babu Wanda zaice ba Zainab bace ta haifi Aysha, gashi ta d'auko kamannin Zainab tunda Aysha da Zainab uwa daya uba daya ne" duka 'yan d'akin sun firgita da jin wai Aunty Aysha ba 'yarsa bace, Aunty ta janyo Hibbah ta rumgume ta suka saki kuka duka su biyun mai ban tausayi sun jima a haka babu Wanda yayi yunk'urin rabasu kowa tausayinsu yake ji a zuciyarsa musamman ma Hibbah da ta taso cikin wahala da uk'ubar *RAYUWA*. Hibbah ta d'ago daga jikin Aunty suna kallon juna "Aunty dama ashe ke 'yar uwata ce shiyasa kike tausaya min kika inganta rayuwa ta ki jiyar dani dad'in rayuwa aunty bani da kamar ki na gode Allah ya saka miki da.........." Aunty tayi saurin toshe mata baki "ko a da Hibbah babu godiya a tsakanin mu balle yanzu da muke *jini d'aya* ni dake, Allah za muyiwa godiya da har ya nufe mu da sanin gaskiya" Hibbah tayi murmushi tare da yiwa Allah godiya, ta dubi su momy sai murmushi suke yi ita da mamy. Mamy tace "zonan Hibbah inji d'umin jikin d'an uwana" a hankali Hibbah ta k'ara kusa da mamy, mamy ta rumgume ta tana jin k'aunarta na ratsa jikinta, ta b'anb'areta daga jikinta tana kallonta "Hibbah yanzu ina d'an uwana yake? A ina yanzu yake *RAYUWA*?" Hibbah hawayen farin ciki nabin fuskarta "mamy yana wani k'auye a cikin k'auyukan Bunkure" mamy ta kalli su Abba da suke ta bin Hibbah da kallo cike da k'auna tace "Yaya yaushe zamuje mu gansa?" Daddy fuskarsa cike da farin ciki "ai yau za'a sallami Faheem tunda k'auyen ba nisa ne dashi ba sai muje yau Donni na k'osa naga d'an uwana" Saudat ta mik'e da sauri "bara naje na kira Dr yazo ya sallami Yaya mu tafi" Aunty tasa dariya "kai Saudat kin fiye zumud'i ki Bari yanzu ma zaki Ganshi ya shigo" "ai Aunty na k'osa ne muje wallahi" Faheem yayi murmushi yana yiwa Hibbah wani kallon "Ashe dai ke k'anwata ce shiyasa na rud'e a kanki na kasa sukuni saboda bana son wani ya b'ata miki *RAYUWA*" "ba wani nan dama can kai kana sonta kana tsoran kar ayi maka k'wace ka rasata yasa har ka kwanta a asibiti wai ciwon zuciya" Abba ya fad'a cikin sigar tsokana duka suka sa dariya banda Kausar da Safiyya da sunma kasa had'a idanu da Hibbah saboda tsantsar kunyarta da suke ji. Safiyya tafi Kausar kusanci da Hibbah don haka ta matso kusa da ita ta rik'e hannayenta "don Allah Hibbah kiyi hakuri ki gafarce ni wulakancin da nayi miki" Hibbah tayi murmushi "habba Safiyya wallahi ni baki yi min komai ba" Safiyya ta rumgume ta tana share hawaye cike da Dana sani tace "na gode sis Hibbah" Hibbah ma ta rumgume ta tana yiwa Allah godiya a zuciyarta ashe itama tana da gata haka, Saudat dake gefe cikin tsokana tace "lallai Safiyya wato yau Hibbah har ta samu matsayin sister" ta fad'a tana dariya Safiyya ta harareta "to ina ruwanki gulgul." Kausar ma ta matso kusa da ita ta zauna a gefenta "Hibbah na sani na wulakantaki nayi miki rashin mutunci iri iri na d'aukeki kamar wata baiwa a gidana, yanzu gani a gabanki ba don ni ba don Allah kiyi hakuri ki yafe min" Hibbah ta shiga girgiza Kai "Aunty Kausar ni ya dace na baki hakuri ba ke ba, don kuwa a matsayina na 'yar aikin gidanki na aure miki miji kiyi hakuri Aunty wallahi babu laifina a ciki ban ma san da auren ba" Kausar tayi murmushi "haka Allah ya k'addara Hibbah hakan shine sanadiyyar kawo zaman lafiya a gidan Allah ya bamu zaman lafiya" Hibbah tayi k'asa da kai cike da kunya, don tunda akace ita matar Faheem ce take tsananin jin kunyar Kausar da kuma Faheem d'in. Momy tace "alhamdulillah naji dad'in wannan al'amari Allah ya had'a kanku" suka ce amin. Dr ya shigo don duba lafiyar Faheem ya tadda Faheem a zaune yana ta murmushi kamar ba shine Mara lafiya ba, dr cikin mamaki yace "a'a Faheem yana ganka haka garau dake kamar ba Kaine Mara lafiyar ba?" Aunty tayi caraf "dr ba dole ka ganshi haka ba tunda ya samu abinda yake so ai dole ya watstsake" Faheem ya harareta "Dr ba wani nan Allah ne ya kawo sauk'i" "to Allah ya k'ara sauk'i" "amin suka amsa. Dr ya mik'a masa takardar sallama da kuma ta wasu magunguna da zai cigaba da amfani dasu, ya amsa sukayi masa godiya ya fita, Daddy yace "kuyi sauri Ku had'a kayan mu tafi, ni so nake kawai naga Mukhtar" Hibbah ta dubi Daddy idanunta taf da hawaye zuciyarta cike take da tsoro tana tuna furucin Inna *_kuma wallahi sauran idan an kaiki kice zaki zo ganin gida wallahi saina kashe ki, kinsan halina zan aikata,_* ta kuma tuno lokacin da gwaggo tace *_yanzu lami baki tsoran yarinyar nan ta fad'a mugun hannu ko kuma su gidan da aka kaita su koreta, ina zata wata sani scan da zskice karta waiwayi mahaifarta? Inna tace oho ni ko Karuwanci zatayi tayi ina ruwana._* Hawayen fuskarta ya tsananta zuba gaskiya bazata iya zuwa k'auyen nan ba don tasan halin Inna lami tsaf zata iya kasheta, ji tayi an dafa kafad'arta da sauri ta waiwaya Kausar ce tace "Hibbah me kike tunani muna ta magana?" Ta share hawayenta ta girgiza kai

Table of Contents

Chapters

63 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});