Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 54

Chapter 54

Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

da kanta Inna ta mik'e "bara a kawo muku ruwa ko?" "A'a ki barshi mun gode" Faheem yayi saurin dakatar da ita donshi ko me za'a yi masa bazai iya cin wani abun daya fito daga hannun lami ba. Abba yace "wajen mai gidan muka zo gashi ance baya nan zai iya kaiwa zuwa yaushe kafin ya dawo?" Inna ta kuma washe baki "ayya ai yanzu zaku ganshi ya dawo ba jimawa zaiyi ba" Abba ya jinjina kai "to shikenan bara mu jira sa" Hibbah sai b'oye kai take kamar munafuka, su kuwa su momy dasu Saudat su Aunty duk mamakin inna sukeyi yadda take ta wani washe baki kamar gonar auduga. Suna nan zaune har wajen k'arfe hud'u saura malam bai dawo ba duk sun k'osa ya dawo musamman Daddy, Faheem ya kalli inna dake ta son jansu da hira "anya kuwa zai dawo yanzu ga la'asae har ta gabato ko dai muje mu dawo ne?" "Eh to ko zakuje ku dawo d'in amma idan sak'one Ku bayar a ajiye masa" duk suka kalleta da mamaki, ita kuwa ko a jikinta ta mik'e ta d'auko wata bak'ar buta wadda rabon da a wanketa har anmanta ta d'ebo ruwa a ciki ta kawo musu "ga ruwan alwala naga lokacin sallah yayi" Faheem ya mik'e "a'a mun gode muna da ruwa a mota" ta dube shi ta d'an b'ata rai ya fara bata haushi "au k'yamarmu kake yi 'yan k'auye ba mutane bane?" Daddy shima ya tashi yana bawa inna hakuri "kiyi hakuri baiwar Allah ba k'yamarki yake yiba, bara muje zuwa anjima zamu dawo" ta kalli su momy da suka kasa ma magana don matar mamaki take basu "ku tashi mu k'arasa can in anjima ma dawo." Suka mik'e zasu tafi Hibbah sai b'oyewa take a bayan su Saudat ita kuma Umma mamaki ne tab ya cikata ya akai Inna bata ganeta ba meta canza. Har k'ofar zaure inna tayo musu rakiya sai surutu take yi musu sudai basu kulata ba sukayi gaba. Ta koma cikin gidan tana ta d'auki ta dubi Rahmatu "ke yanzu haka ake tarbar bak'i musamman ma wad'annan 'yan birni dasu kina ganinsu kinsan kud'i ya zauna musu ai ko baza su shaba sai ki kawo musu ruwan, ni wannan d'an gayun ne yafi bani haushi sai wani iyayi yake yimi" sai kuma ta washe baki "Kai Allah mun gode maka may be sunzo tafita ne da malam can birnin shikenan zamu bar zaman k'auye" ta saki gud'a. Su Daddy kuwa suna fita suka ce su sallah zasu fara yi su matan su shiga gidan su Umma idan yaso su daga baya zasu shigo. Haka kuwa akayi Umma tayi musu jagorancin shiga cikin gidan suka shiga da sallama lokacin gwaggo tana sallah bata amsa musu ba. Umma ta shigar dasu d'akin gwaggo ta shimfid'a musu tabarma suka zauna ta dubesu da murmushi a saman fuskarta "Hibbah tashi kije ki amso musu ruwan alwala mun mance ba'a amso ba" momy tayi saurin tare ta "a'a idan akwai a nan zuba mana muyi dashi" "zaku iya kuwa amfani dashi karya ja muku matsala tunda ba sabawa kukayi ba?" Mamy ta mik'e "nuna min inda ruwan yake ni na d'iba don naga kamar kina tsoro ne" "a'a bara na d'ebo muku" Umma ta tashi ta d'auko butocin gwaggo sababbi guda uku ta zuba musu ruwan a ciki, momy da mamy da kuma Aunty suka d'auka. Suna fita gwaggo ta idar da sallar ta dubesu "sannunku da zuwa kunsha tafiya ya hanya?" "Yauwa alhamdulillah" "kunzo lafiya?" "lafiya lau mun same Ku lafiya?" Nan suka shiga gaggai sawa, Nawaz da Hisham suka gaishe ta. Hibbah ta kalli gwaggo cikin shagwaba "wai gwaggo yanzu don Allah wai baki gane ni ba?" Gwaggo ta tsaya kallonta tana mamaki fara tattafa hannu tana salati "Hibbah Kece? Alhamdulillah Allah kaine abin godiya Hibbah dama ashe zan kuma ganinki?" "To ba gashii kin ganni ba, ni fa ba mun b'ata da wannan tsohuwar tunda bata ganeni ba" Hibbah ta fad'a cike da shagwaba "ayya Hibbah ba haka bane ni ban tab'a tunanin zan kuma ganinki ba, na d'auka tunda lami tace karki kuma dawowa bazaki dawo d'in ba." "To ba gashi yanzu na dawo ba ina Abu?" "Gaskiya naji dad'i da zuwan nan naki, Abu tuni tayi aure Hibbah har da 'ya'yan biyu ma" Hibbah ta zaro ido "gwaggo Abu ce ta haihu har yara biyu?" "Eh mana Hibbah kema da kina nan da yanzu da naki, wad'annan su waye? Ko a wajensu kike aikin?" Gwaggo ta tambaye ta. Gyad'a Kai tayi "eh gwaggo a gidansu nake aiki sune suka inganta min rayuwa suka tallafa min suka ni a makaranta sun d'auke ni tamkar 'yarsu" "Allah mai iko mun gode da wannan kulawar da kuka yi mata Allah ya saka da alkhari ya k'ara bud'i mun gode" Kausar tayi murmushi "babu komai gwaggo" su mamy suka shigo suka gaggaisa da gwaggo suma gwaggo tayi musu godiya. Su Hibbah suka tashi don zuwa suyi alwala Saudat ta kalli Hibbah tana murmushi tace "Hibbah banji kincewa gwaggo kinyi aure ba" Hibbah ta harareta gwaggo ta rik'e baki "au Hibbah kema kinyi aure shine ba'a fad'a mana ba" "gwaggo k'arya take fa" Saudat tasa dariya "wallahi gwaggo tayi aure amma bata tare ba, munzo wajen baba ne" Hibbah ta kai mata duka tare da fita ta d'auki buta Nawaz ya biyota wai shima alwalar zaiyi. Su Safiyya ma suka fito Saudat tana ta yiwa Hibbah dariya, suka yi alwala suka koma d'akin. Bayan sun idar da sallah su momy suka shiga hira da gwaggo kamar sunsan juna anan suke fad'a mata tsakanin su da Hibbah kuma sun tabbatar mata da cewa Hibbah da gaske tana da aure d'an uwanta ma take aure amma bata tare ba, gwaggo ta bayyana murnarta sosai suna cikin hira Daddy ya kira layin momy ya fad'a musu sun dawo. Momy ta fad'awa su Umma taje ta shigo dasu, gwaggo ta fito da manyan tabarmi aka shimfid'a a k'ofar d'akin su Daddy suka shigo a tare da malam (mijin gwaggo) suka gaggaisa dasu gwaggo, sukayi musu godiya da kuma yi musu murnar ganin d'an uwansu da sukayi. Bayan sun gama gaggaisawa gyara zama ya fad'a musu abinda ya kawo su ya d'ora da cewa "to shine muka zo don mu tabbatar amma ita Umman Hibbah tace wai ba ita bace ita a nan aka haifeta kuma wai iyayenta basu mutu ba suna raye" malam da gwaggo suka yi shiru kamar ruwa ya cinyesu babu wanda ya iya magana, malam yayi k'asa da kai yana tunanin dole yau ya bayyanawa Aysha cewa ba sune mahaifanta na asaliba don ranar wanka ba'a b'uyan cibi. A hankali ya d'ago kai ya kalli duk su Abba da suka maida hankulansu a kansa ya dubi Umma yace "tabbas Aysha ba mune asalin mahaifanki ba" a razane Umma take kallon sa da alamomin tabbaya k'unshe a fuskarta. Malam ya cigaba "bamu muka haife ki ba kuma da dukkan alamu wad'annan mutanen sune 'yan uwanki da mukayi ta nema bamu samu ba, yau zan baki labarin yadda akayi muka same ki" "Ranar wata juma'a da yamma na dawo daga gona na hango ki kinata............... *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:27 PM] Maman Najma

Table of Contents

Chapters

63 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});