Chapter 48
Chapter 48
su momy da mamy basu saka baki ba. Aunty Wanda tunda suka shigo data zauna kanta yake a k'asa tana zubda k'walla tana tausayawa halin da Faheem zai shiga na rashin Hibbah a hankali ta d'auko wayarta a jaka ta shiga kiran Hibbah ta saka a speaker kowa yanaji tana fara ringing Hibbah ta d'aga cikin tashin hankali da tsoro ta Fara magana "Aunty ki taimake ni kasheni zaiyi ya kuma lalata min *RAYUWA* Faruq ya sato ni ya kawo ni wani waje zaiyi lalata dani Aunty don Allah ki taimaka......" D'if wayar ta d'auke. Aunty gaba d'aya ta tsorata da fargabar abinda Faruq zai yiwa Hibbah ta kalli kowa na parlor'n duk sun firgita suke ta kalli Daddy jikinsa yayi sanyi don tagumi ma yayi, ta maida dubanta ga Faheem gani tayi ya mik'e ya dafe kansa yana tangad'i zai fad'i kafin tayi wani yunk'uri har yazube a wajen. Da gudu ta k'arasa kusa dashi ta shiga tana kiran sunanshi saidai ina baya ma hayyacinsa, su Abba suka k'araso kusa dashi suna tattab'ashi sam baya motsawa daddy duk hankalinsa ya tashi ya zaro wayarsa daga aljihu ya shiga kiran layin Dr Umar. Ba jimawa ya d'auka Daddy baima jira sun gaisa ba yace "Umar kana asibiti ga munan zuwa Faheem ya fad'i" shima Dr Umar ya d'an ji tsoro saboda yanayin ciwon nasu ba'ason mutum ya dinga damuwa balle har takai ga ya fad'i "ina nan daddy garin yaya" Daddy bai tsaya bashi amsa ba ya kashe wayar. Abba da Daddy ne suka kamashi suka shiga dashi mota, Aunty da Abba suka shiga motar, Daddy momy da mamy kuma suka shiga wata motar. Suna zuwa nurses har sun fito masa da gado aka d'orasa a kai suka shiga dashi Dr Umar yabi bayansu wani d'aki suka shiga. Dr Umar ya kai kusan 1hour a ciki sannan ya fito daga d'akin, su Daddy da sauri suka nufoshi suna tambayar jikin nasa ya kasa magana yace "daddy kuyi hakuri muje office" yayi gaba suna binsa a baya har suka isa office d'in nashi, suka zazzauna akan kujerun office d'in. Dr Umar ya dubi su Abba, dasu momy da hankalinsu ya gama tashi don a rikice suke, balle kuma Aysha da taketa kuka mai ban tausayi, yace "munyi k'ok'arin ceto rayuwarsa cikin ikon Allah Daddy gaskiya rayuwar Faheem tana cikin had'ari sosai zuciyarsa tana gab da bugawa, matuk'ar ba'a daina b'ata masa rai ba akwai abinda yake matuk'ar so a zuciyarsa amma kuma ana yunk'urin hanasa wannan abun, matuk'ar ana buk'atar rayuwarsa to Dan Allah Abba ayi yunk'urin yi masa wannan abun. Nan 4hours zai iya farkawa yana buk'atar hutu baza ku iya ganinsa ba" gaba d'ayansu sun kasa magana Abba ne kawai yayiwa Dr godiya suka nufi d'akin da Faheem ke ciki suna lek'ensa ta window har ya d'an fad'a duk tausayinsa ya cika musu zuciya. Sagir mijin Aunty Aysha ne ya shigo cikin wajen ya k'araso kusa dasu ya gaishe dasu Abba da tambayar mai jiki, shima ya lek'a ta window yaga yanayin jikin Faheem d'in ya tsorata ya kalli Aysha "Aysha wai mene sanadin wannan ciwon" Aunty Aysha tasa kuka tama rasa me zata ce masa, hankalinta ya kasu biyo tana tunanin rayuwar d'an uwanta tana kuma tunanin rayuwar Hibbah a wajen Faruq, Daddy ne yayi k'arfin halin ya bashi labarin duk abinda ya faru ya d'ora da cewa "nayi nadama sagir nayi Dana sanin sangarta Faruq da nayi na lalata masa tarbiyya, na b'ata masa rayuwa sam bana ganin laifinsa idan yayi gashi yanzu yaya neman lalata Matar Yayansa Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un nayi nadama" ga mamakin kowa hawayene yake zuba a idanun Daddy. Sagir yace "kayi hakuri daddy kabar min komai a hannuna ni da kaina yau zan fara binciken inda ya kaita yanzu zanyiwa yarana waya daga asibitin nan bazan je ko ina ba zan fara bincike akan Faru................. *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:26 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page4⃣5⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* *a gurguje pls* Sagir mijin Aunty Aysha inspector ne shiyasa yayi ruwa yayi tsaki a kwana uku suka damk'e Faruq ta hanyar amfani da company'n Layin da yake amfani dashi don gano inda yake, sun sameshi ne agidan gonar Daddy dake wajen gari inda yake yunk'urin raba Hibbah da mutuncinta. Bangaren Faheem Allah ya taimaka ya farka sannan su Abba suna bashi kulawa daidai misali, anyiwa Kausar waya ita hankali a tashe ta nufo asibitin, kwana ukun da yayi alhamdulillah ya samu lafiya musamman ma Daddy ya tabbatar masa da aurensa da Hibbah babu fashi tana nan a matsayin matarsa, tuni Faheem ya watstsake ya samu sauki don shi a yanzu ji yake babu wani abu da yake damunsa duk wata matsala yashi ta kau. Su momy ne suka zaunar da Kausar suka yi mata nasiha mai sanyaya jiki kafin su fad'a mata abinda yake faruwa, ta girgiza sosai dajin a dalilin aikin da take yi mijinta zai k'aro aure sannan kuma 'yar aikinta zai aura gaskiya wannan aikin bata ga amfaninsa ba tunda bata da lokacin Bawa mijinta kulawa. Da bata d'auki hakan wani abu ba sai yanzu, sai yanzu take ganin illar wannan aikin nata na bank ga 'ya mace tunda ta gani a kanta wace irin kulawa ce Faheem baya bata duk da ta fifita aikinta akan zaman aurenta hakan baisashi ya daina bata kulawa ba, babu abinda ta rasa a wajensa ga d'anta Nawaz data k'wallafa rai akansa shima sam bai Saba da ita ba yafi sabawa da Daddy'nshi da kuma Hibbah, ita kama shikenan bakin alk'alami ya bushe, me yasa bazata bashi kulawa kamar yarda yake bata ba? Me yasa ta zab'i ta k'untatawa iyalanta ta fifita aikinta akan mijinta da d'an? Lallai ta tafka babban kuskure wanda baza ta tab'a iya gyarashi duka ba tunda gashi a sanadin haka mijinta zai auri 'yar aikinta wadda tafi tsana. Ranar da aka damk'e Faruq suna kamashi suka yiwa su Aysha waya suka fad'a mata ita kuma ta fad'awa su Abba, Daddy have su huce dashi yanzu zasu zo su amshesa, don sunyi shawara da su mamy sun yanke hukuncin kaisa gidan mari su kuma cigaba da yi masa addu'ar Allah ya shiryesa. Faheem ba k'aramin farin ciki yayi ba da aka samo masa Hibbarsa, ya kuma hi dad'i da hukuncin dasu Daddy suka yanke don hakan shine daidai. A lokacin Daddy da Abba suka je suka amshi Faruq suka wuce dashi gidan mari, yayin da inspector Sagir ya kawo ta asibitin wajen su Aysha bama su had'u da su Daddy ba, dama kuma bata tab'a ganin ko d'aya daga cikin daddy ko Abba ba. Inspector Sagir yasha godiya da addu'a wajen su Aysha da su momy har ma da Hibbah d'in, yayin da Faheem yayi masa kyauta mai tsoka tare da yi masa godiya. Tunda Hibbah tazo bayan Sagir ya koma bakin aikinsa su Aunty suke ta tambayarta abinda ya faru, Hibbah ta numfasa tace "Aunty Allah abin tsoro ne, sai ka jima kana shirya abu amma matuk'ar bai nufin hakan da faruwa ba babu Wanda ya isa yasaka hakan ya faru, Aunty ashe Faruq ya jima yana shirya hakan yayi amafani da Kalmar so wajen ganin ya aikata nufinsa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63