Chapter 27
Chapter 27
da lullub'e kanta da mayafin rigar, ta shafa powder da lipstick ta feshe jikinta da daddad'an turarukan da aunty ta bata, ta rik'e hannun Nawaz d'an kad'afi duk inda ta cire k'afa ya maida sawunshi, shiyasa suke kuma shak'uwa. Yana zaune cikin motar ya kasa d'auke idanunsa daga kanta ashe duk ganin da yake mata bai gama ganin baiwar da Allah yayi mata ba, tayi masa kyau shi dai yana k'aunarta a ransa, tak'i goguwa a zuciyarsa wani d'an sataccen murmushi tayi masa, ikon allah sai yaji ta tafi dashi gaba d'aya. Ya fito ya jingina da motar komanta ya burgeshi ya rik'o hannun Nawaz yana kallon kyakykyawan yaron, a kunyace ta gaisheshi don itama d'in yau ta k'are masa kallo. Bak'ine kyakykyawa wato irin black beauty d'in nan hancinsa dogo har baka shi ya dad'a fito da sigar kyansa ga shiga da tsari, yana sanye da wani laushashshan boyel yayi matuk'ar kyau ga nutsuwa da allah ya bashi. Ya kalleta da murmushi a fuskarsa yace "Hibbah naji dad'in ganinki da baki fito ba bazanji dad'i ba sai na tafi zuciya ta tana wasi wasi kina jin sak'ona wajen Aunty Aysha na dameta da batunki, Hibbah ki godewa Allah dan ba k'aramin so nake miki ba," tayi murmushi "uhm to na gode itama tana fad'amin," ya kuma murmushi "Aunty sarkin yak'ina ce koda yake itama tasan irin son da nake miki so ne na tsakani da Allah, gashi kuma rowar magana kike yi min so nake naji muryarki dad'i take yi min," ta d'an kalle shi "to me kake so nace?" "Hibbah kenan nidai fatana ki amince min muyi aure, amma fa ban b'oye miki ni mutum ne magidanci mai iyali da mata na da yara na uku ban miki tsufa ba dai ko?" Ta kuma murmushi "aure nufi ne na Allah," "nasan hakan kina nufin kin amince kina so na kuma zaki aure ni?" Tayi shiru, ya karyar da kai yace "hmm Hibbah kinyi shiru har cikina ya d'uri ruwa fa," tayi dariya "sai kace wani mai lefi?" "Ai gara ace lefi nayi zuciyata ta kasa nutsuwa," tad'an sauke ajiyar zuciya "to ka bari sai naje na fad'awa ummana." Ya dubeta a nutse "shikenan iyaye sune gaba da komi Hibbah na baki dama Amman dai ki tausayawa bawan Allah nan, Zan Kira ki a waya naji yarda kukayi," ya bawa Nawaz kud'i "Nawaz rik'ewa Auntyn ka ko?" A daidai sanda motar Faheem ta sanyo kai ko kallonsu baiyi ba ya shige cikin harabar gidan, 'yar hantar ta saida ta motsa sukayi sallama da Jabeer ya huce sukuma suka tawo gida. B'angaran Faheem kuwa yana shiga ya zauna kan gado gami da jefar da takardun yayi jim zuciyarsa zafi take da tana tafasa sai yaji gumi ta kowanr kofofin gashinsa kamar Mai had'iyar wuta, ya kasa sanin wannan abu ciwo ne ko lalura ne ya rasa meke masa dad'i, ya huro iska mai d'umi a bakinsa zafi dad'a k'aruwa yake a ko ina na jikinsa, mik'ewa yayi ya shoga toilet ya sakarwa kanshi shower snyin ruwan ya ratsa shi had zuciyaarsa, bai san iya lokacin da ya d'auka ba sannan ya fito ya kunna AC ya kwanta ya d'ora kansa bisa pillow ya lumshe idanunsa. Yana tunanin wai shin me yasa ya damu kansa da yarinyar nan? Shi fa ba sabgarta yake shiga ba don me yake jin zafo don ya ganta da wani ina ruwanshi da sabgarsu? Don me zai tunzura haka don ta fit a bada izininshu bane ko kuwa metayi masa ya b'ata ransa har hankalinsa ya tashi haka? Ji yayi anyi masa kiss gami da shafo sajensa, juyowa yayi ya rumgumota yayi ajiyar zuciya, ya lalubo abinshi duk lefinta ne da bata tarairayarsa bare ta kwantar masa da hankali in ya shiga damuwa. Juyowa tayi suna kallon juna abinda ta gano a idanunsa ya tabbatar mata akwai rikici wani abu ya tab'o mata shi. Ta kuma k'ura masa ido "dear me yake damunka ne naka ka sauya ba kamar yadda nake dawowa na sameka ba," bai fad'a Mata abinda me zuciyarsa ba sai dai yace Mata wai baijin dad'i tunaninta da kewarta suke damunsa, nan ta shiga yi masa kisses masu zafi don k'ok'arin mantar dashi dan tasan lefin tane Sam bata bashi kulawa kullum ita tana wajen aiki kamar agogo.. *** Hibbah na zaune a d'aki taga mutum kawai a gabanta a karo na biyu ya kawo mata ziyarar bazata yunk'urun guduwa tayi ya kuwa yi azamar cafkota kamar 'yar tsana ya rik'e ko motsi bata iyawa, tasa kuka mai ban tausayi yau ta gamu da gamonta kashinta ya bushe in dai kisa ne yau Faruq ya karta. Ya tallafo hab'arta ya juyar da kanta gefe, tsananin bugun zuciyarta yasa taji zata fad'i don dai ya rik'eta ne amma da tuni ta fad'i. Shi kuwa Faruq tamkar wata sabuwar halitta yake ganinta d'an hakin da ka rain a shike tsone maka ido, wai Hibbah ce macen da ya kasa jimiri da dakewa akanta so guda ne kamar Hibbah babu abinda yake buri fiye da ita a *RAYUWA RSA*, duk tsarinsa ya wargaje d'aya bayan d'aya abin har mamaki yake bashi ya tashi hankalinsa idan yana zancen zuci sai ya fito fili yaji yana sambato. A yau tausayi take Bashi a yau ji yake ba mace mai k'imarta, a yanayin sonta da yake addabarsa, don't me why not baisan dalili ba? Ya sassauta murya "Hibbah why? Why Hibbah? Me yasa nake son ki wallahi babu dad'i akwai wani abu ne daga Allah, ni fa na haukace akanki Hibbah ke baza ki Sani ba har sumbato nake idan sonki da tunaninki sukayi min zabi, ranar dana ganki da wannan guy d'in kasa barci nayi Hibbah, son nan shu'umi ne ya canzani Hibbah ya canza min manufa a kanki ki manta da baya daya kasance kuskure ne don a da can ban iya tantance sha'awar da nake miki yanxu kyauta kika mallaka min kanki bazan iya yi miki komai ba sai Allah yasa aure a tsakanin mu Hibbah bud'e idanunki ki dubi masoyinki." Hawaye ne yake zuba a idanunta, yasa hannu ya lakuto hawayenta ya shanye kuma sassauta murya yayi "Hibbah kina sona kuwa?" Saura kad'an ta fad'i yayi saurin tarota kanta yayi gingirim. "Hibbah" ya fad'a da rad'a, wani abu ke taruwa cikin idanunsa, tsorone yasa ta gyad'a mishi kai alamar wai tana sonshi don tasan Faruq sarai baida tausayi da imani kwanda ta bishi su rabu lafiya. Ya kafeta da ido can kuma yayi murmushi "matsoraciya ban yarda da wannan amsar ba ki bud'e bakinki naji muryarki kiyi magana da yawunki," "uhmm ina sonka" muryarta a sark'e ta fad'a. Ya shiga tsantsar farin ciki "are you sure? Kin tabbatar alk'awari ne fa," ta rufe bakinta da hannunta yadda zuciyarta take bugawa zai iyasa jininta hawa saboda tsoro. Ya ja da baya "ina k'aunarki Hibbah zan tabbatar miki da hakan idan kin samu nutsuwar zuciyarki, don Allah ki daina jin tsorona ki amince dani," ta gyad'a kanta, Nawaz ya k'ank'ame shi "uncle kullum kazo sai kasa aunty Hibbah tayi kuka saina fad'awa daddy na." Bata san sanda ta zube k'asa ba ta had'a kanta da gwaiwa, ya shafa kan Nawaz ya zare masa ido tare da d'ora
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63