Chapter 2
Chapter 2
dauke a fuskar Umma tace "ya akai kika san abinda zan fada miki kenan Hibbah?", murmushi Hibbah tayi tace "Umma ai kullum idan zam fita sai kin yimin wannan fadan shiyasa na rike". Cikin jin dadin kalamanta umma tace " to shikenan dan allah kiyi amfani da fadan danayi miki kinji Hibbah, kije Allah yayi miki albarka, ya kare minke daga dukkan sharri ya kuma bada sa'a kinji Hibbah". Take taji wani happy ya lullubeta cikin jin dadi da manta duk wata damuwarta tace "ameen ummana saina dawo" ta fada tana fita daga gidan. Umma tace "allah ya dawo min dake lafiya". Tsakar gida umma ta koma ta nufi bakin murhu tana iza wutar da take girki da ita. Muryar lami taji dab da ita tana cewa "munafuka annamimiya ai dama nasan duk abinda Hibbah takeyi a gidannan kece kike kitsa mata komai, to wallahi gara ma tun da wuri ki daina kitsa mata bakin hali irin naki idan ba haka ba......." Tayi kwafa "kema kinsan sauran, haba shiyasa naga kullum idan zata fita saikin kirata kin kitsa mata muggan kalamai to ni naci dubu sai ceto wallahi." Lami ta fada tana nuna umma cikin tsantsar masifa har wani girgiza jiki take yi. Ita dai umma bata tanka mata kasancewarta mace mai hakuri da juriya saima ce mata tayi "allah ya baki hakuri Yaya" Cikin masifa lami ta hayayyako mata "ai dama ke kullum haka kike sai kin kulla munafincinki kizo kina bawa mutane hakuri, wallahi bara malam yazo ni gaskiya na gaji da ganinki a gidan nan yazo ya sauwake miki kawai." Umma ta tsorata kwarai dajin furucinta don tasan tsaf zatasa ya saketa din murya na rawa tace "Yaya kiyi hakuri wallahi addu'a kawai nayi mata banda wannan bance Mata komai ba." Tabe baki lami tayi ta juya tana tafiya tare da cewa "kyaji dashi don zamanki a gidan ya kusa karewa eyeeh! Gara ki tattara ki tafi" Tsugunnawa umma tayi a gaban murhun tana mamakin wannan *RAYUWA* da sukeyi a cikin gidan tamkar wasu 'yan aiki ko kuma bare. Hannu ta daga sama tana addu'ar Allah ya kawo musu dauki. Ita ko lami kofar dakinta taje ta zauna tana girgiza kafa cike da masifa, Rahmatu ce ta fito daga daki duk tayi wani dige dige a fukarta tazo ta kwanta akan cinyar lami cike da shagwaba tace "inna nifa yunwa nake ji" ta fada tana zunburo baki. Lami tace "a'a Rahmatu ai na ajiye miki abinci gashi can a roba kije kici" kuma zumburo baki tayi "ni wallahi bana cin wancan abincin" Rahmatu ta fada tana kuma narkewa a jikin lami. Lami cikin bala'i tace "to karki ci din cikin waye?", Burgima Rahmatu ta shiga yi tana cewa "ni wallahi bazan ci wannan abincin ba". Lami nasan Rahmatu fiye da kowa cikin sauri ta dagata tana cewa "haba Rahmatu ya zaki dinga burgima akan wani abinci, uhumm?" Cikin shagwaba da sangarta tace "to ni ki bani kudi na siyo alala a wajen Abu don bazanci wannan abincin ba". Cikin lallashi lami tace "don wannan ai mai sauki ne " ta kunto kudi a jikin zaninta ta bata "ungu jeki ki siyo kinji" karba tayi ta ruga da gudu tabar gidan. Bangaran Hibbah kuwa tana fita ta nufi kasuwa dake can take kaiwa, bayan taje ta zauna a mazauninta mutane suka fara zuwa siye. Sale driver ne yazo yana........... *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:21 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *RAYUWA* page 3⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* *Na sami dukkan sakonku masoyan A.A Garkuwa, kuma in allah yarda zan cigaba da rubuta wannan littafin.* Yana wangale baki ya karaso kusa da Hibbah zai zauna da sauri Hibbah ta mike tsaye tana binshi da wani mugun kallo tare da nunashi tace "Kai sale mene haka baka da hankaline zakake kokari goga jikin ka da nawa?", Kallon ta yayi yana kuma wangale baki yace "haba Hibbah mene waike yaushe ne zaki gane nufina to mene don na hada jikina danaki." Mugun kallo ta buga mai tare da daukar farantin ta zata bar wajen. Hijjab dinta ya janyo da karfi, baya tayo sosai tare da farantin hannunta hakan yayi sanadiyyar subucewar faranti daga hannunta. Ya kife sauran abincin rabi ya zube a kasa rabi kuma a jikinta, Rahmatu da a gabanta akayi komi ta tsaya tana dariya don tasan koba komai yau Hibbah saita nadu a wajen inna . Ita kuwa Hibbah iya kuluwa ta kulu zuciyarta tana mata wani irin radadi cikin zafin nama ta juyo tana binsa da mugun kallo tare da cewa "wallahi kaji Na rantse sale sai ka biya kudin abincin nan daka zubar don bazan dauki asara ba, don nima idan na koma ba afuwa Inna zata min ba bazaka jamin duka a banzaba wallahi" cikin zafin rai take magana. Dariya sale yasa yace "ai nasan da haka kudin abincinki zan biyaki na nawa ne?" Kallon shi tayi a kaiksice tace "Na murtala shida da rabi ne", Hannu ya zura a aljihunshi ya ciro Dari biyar ya mika mata, kallon shi tayi cikin tsiwa tace "mene na wani bani dari biyar bayan kasan bani da canji." Juyawa yayi yaga hankalin mutane baya kansu ya kalli Abu kawar Hibbah yaga bata kallonsu. Hibbah ta kalleshi duk yayi yanayin mara gaskiya sai wani waige yake tace "malam ni ka samu canji ka bani kudi na ka wani tsaya kana waige waige." Murmushin mugunta sale yakeyi yana kallonta yace "karbi kudin da daddare zanzo dandali cin gyda kafin nan kin samu canji saiki bani." "Ni ban yarda ba kuma bazan karba ba kawai kaje ka samo ka bani ina zaune anan" Hibbah ta maida mai da amsa cikin sauri. "To yanxu ya kike so nayi kinsai dai babu wanda zai bamu canji a kasuwar nan koh?" Sale ya fada yana kallon kirjin Hibbah yana lasar lebe. Tsaki Hibbah taja "kaje ka samo ina jiranka a wajen Abu " tana gama fada masa ta tsugunna ta kwashe robobin da murafi tare dayin gaba, wajen da Abu ke zaune ta karasa ta zauna. Da gudu Rahmatu ta kwasa tayi hanyar cikin gari. Da ido Hibbah ta bita cike da tsoro don tasan tana zuwa gida zata fadawa inna. Abu ta kalleta tace "Hibbah ni a ganina dama ki karbi kudin kamar yadda yace da daddare idan mukaje dandali saiki bashi". Hibbah tayi shiru kafin tace "wallahi Abu ina tsoran sale ne kwata kwata na tsameshi na tsani halinshi bana son yana kulani KO kadan, shiyasa fa bana son ya dauki abincina, kina gani kullum don kar magana ta hada mu yasa bana karbar kudin abincinsa amma shi ki duba yarda kullum yake wani shige min." Ta fada cike da damuwa, "Don kin tsane shi bazai hanaki karbar hakkinki ba a wajensa, sannan ki duba fa kigani kullum sai Inna lami ta dakeki akan bakya cika mata kudinta, gashi yanxu Rahmatu taga lokacin da ya zubar da sauran abincin na tabbata saita fadawa Inna kuma idan baki karbi kudinnan ba baki da wata sheda ta kare kanki a wajenta gwara kawai ki amsa." Shiru Hibbah tayi tana nazarin kalaman Abu tabbas gaskiya ta fada mata gwanda ta karbi kudin nan data komawa Inna gida ba sauran kudi.
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63