Chapter 28
Chapter 28
hannunsa a kan leb'ensa yace "shiiit! Keep quiet surutunka yayi yawa parrot, tafiya zanyi gobe zan kawo maka ice cream da ball," Nawaz yayi dariya ya kad'a kansa. Ya kashe bakin surutu tunda zai kawo toshin baki ya d'aga mishi hannu "uncle bye sai gobe," yayi murmushi tare tare da fita daga parlor. Nawaz dafa bayanta "Aunty Hibbah uncle dukanki ko? Saina fad'awa daddy shima ya dukeshi," bata kulashi ba yace "kinji," Sallamarshi ta katse Nawaz ta kasa d'ago kanta bare yayi masa sannu da zuwa, ta runtse idanunta bugun zuciyarta ya tsananta, sai kuma taji wani sanyi yana kad'ata wani abune ta kasa fahimtarsa a duk sanda taji Faheem, bata san ya dinga ganinta da wani lefi, mutum ne mai k'ima a idonta. Ya rumgume me Nawaz suka zauna hankalinsa yana kan Hibbah kome yake sata yawan damuwa? Nawaz ya kalli daddy'n nasa "Daddy, uncle ne ya so shine............." Nan take fuskarshi ta canza kamar an fad'a mishi sak'on mutuwa, d'if komai ya tsagaita a kwanyarsa, wani abu ke faruwa dashi fiye da wanda yaji ranar dayaga Hibbah da Jabeer, dole Faruq yafi tada masa hankali idanunsa sun sauya. Bai sake kallon ta ba, ta mik'e ta shige d'aki ta fad'a kan gado, wani bak'in ciki ya addabeta ya zatayi da *RAYUWARTA*, shiru ma magana ce a wajen Faheem tun a karo na farko yaja kunnanta da gargad'inta akan Faruq gashi ya kuma jin Faruq yazo wajenta dole ya zargi da yawunta da sanint Faruq ke zarya a gidan, haka tayi ta jin haushin Faruq zuciyarta sam bata jin dad'i. Tun daga ranar basu k'ara had'uwa da Faheem ba, sun shiga wasan b'uya naushi ya kuma k'aruwa. Shi kuwa Jabeer ko yaushe yakan tuntubeta a waya yaji wai yaushe zai zo ya ganta, ita kuma ganin Faheem baice da ita komai ba sanda ya gansu da Jabeer yasa bata damu ba ko kad'an tunaninta Aunty Aysha ta fad'a masa komai game da Jabeer, don haka ta bashi damar cigaba da mu'amalarsu. Kamar kullum da yamma rana tayi sanyi ya shigo saidai bai samu damar shigowa harabar gidan ba saboda tsaro daya samu an canza wani mai gadi, kuma ya sanar dashi cewa Mai gidan ya kafa dokar shiga gidansa. Waya ya zaro ya kira Hibbah ringing biyu ta d'auka yace "na k'araso ina bakin gate d'in," "to" ta fad'a tare da kashe wayar ta fito. Tana sanye take da da atampa green light da ratsin baby pink ta lullub'o baby pink mayafi a waje ta iskeshi ta k'arasa suka yiwa juna murmushi, ya rik'o hannun Nawaz yana da san yara sosai yace "Hibbah kina jin dad'inki kullum kike min, ya batun mu kinsan rana bata k'arya saidai uwar d'iya taji kunya," ta sunkui da kanta "ai nace na amince, munyi waya da Umma tayi farinciki," yayi dariyar jin dad'i "to Hibbah na gode da karb'ata da kikayi, ni kuma sainaga abinda ya turewa buzu nad'i dan Zan turo manyana su gana," "kamar ya ban fahimta ba," wani kallo yayi mata harsaida taji kunyarshi "to ina neman izini zan turo manyana wajen iyayen mu, za'a ga Alhaji ko? Hibbah aurene ya kama ceki zaki fi samun nutsuwa hankalinki ya kwanta ki samu wadataccen 'yan ci" Shiru tayi cikin nazarin jawabinsa babu shakka gaskiya ya fad'a domin har yau a rakub'e take gidan mutane matsayin mai aiki, amma in d'akin aurenta ne fa alfarmace da darajarta, ta kalleshi "bazan b'oye maka komai ba kamar yarda kaji a bakin Faruq ya fad'i matsayina a gidansu ni 'yar aikinsu ce, Aunty Aysha ita ce ta taimakawa *RAYUWATA* ta bani kulawa da ilimin da nake yi, dan haka kai tsaye bazan amsa maka ba har sai nayi shawara da Aunty dan bani da wadda ta fita a duniyarnan sai Umma," yayi d'an murmushi "naji bayananki kuma na gamsu, nidai na ganki nace ina son ki, ra'ayi nane na gamsu dake Hibbah don allah nake sonki," "na fahimce ka, kuma ka kuma bani dama dai na sanar da aunty," yayi dariya "kina son Auntyn nan da yawa," "ba doleba masoyinka ai masoyinka ne," ya kuma yin dariya "to na gode sai kuma yaushe?" D'as d'as k'irjinta ya data gano motar Faheem, a d'an sace ta kallo shi ko inda suke bai kalla ba, mai gadi ya bud'e k'ofar tare da d'aga masa hannu "barka da dawowa," hon yayi masa ya shiga ciki............. *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:23 PM] Maman Najma Author P1: Yana mamkin meya kawo ta gidan ya Faheem. Hibbah kuwa tana shiga gida d'akinta ta nufa ta zube a kan gado ta shiga rera kuka, tana mai jin zafin abinda Faruq yayi mata ace a gaban saurayinka yayi maka wannan rashin mutuncin wannan wace irin *RAYUWA*ce? Ta kuma rushewa da kuka tana kuma tunano *RAYUWARTA* ta baya. Nawaz ne ya shigo rik'e da chocolate a hannunsa yana sha ya mik'o mata "Aunty kinga uncle ya bani chocolate," da sauri ta goge hawayen ta tana murmushi tace "to jeka sha Nawaz nima bara na shiga kitchen," ta mik'e ta nufi kitchen ta had'a musu dinner ta gyara kitchen d'in, tana gamawa taji ana kiraye kirayen sallah tayo alwala tazo ta gabatar da sallar, ta d'ebo abinci ta zauna suna ci ita da Nawaz sai shirme yake mata ita kuwa duk abin da Faruq yayi mata ne yake damunta har ta kwanta tana tunanin abin. Washe gari Monday ta tashi da ciwon kai sakamakon kukan da taci jiya da dadaddare, ta tashi tayiwa Nawaz wanka ta shirya shi school bus na zuwa ya tafi, ita kuwa bata da niyyar zuwa saboda ciwon kan dake damunta don tana gama shiryashi ta koma ta kwanta sai wajen sha d'aya ta tashi tayi duk ayyukanta tana cikin yin mopping taji motsin mutum a bayanta tana waigawa taga Ashe Faheem ne tace "barka da safiya daddy" bai ma jita ba dun ya sha'afa wajen kallonta tunda suke zaune da ita sai yaune ya tab'a k'are mata kallo lokaci d'aya yaji wani abu a zuciyarshi, hazak'ar Hibbah da ayyukanta suna burgeshi sam bata nuna gajiyawarta akan duk abinda Kausar zata sata ga d'awainiyar da take yi masa da yaro. Ta kuma cewa "daddy barka da safiya," ya d'anyi firgit ya kalleta "lafiya" ya huce d'akinsa ya shiga ya d'auko takardun daya manta ya huceta, ita kuwa ko a jikinta ta k'arasa aikinta tayi wanka ta shirya tsam kamar mai fita wajen party ta shiga kitchen ta d'ora musu abinci yana yi ta juye ta jere a dinning ta koma d'aki ta d'an kwanta a hankali bacci yayi awon gaba da ita. Cikin barci kamar a mafarki taji ana shafata taji kamar an danneta a hankali ta bud'e idanunta wa zata gani Faruq ne a kanta wani wawan ihu ta saki tare da tattaro k'arfinta ta tunkud'eshi ya fad'i k'asa da gudu ta ta fito parlor kicib'is sukayi da Faheem daya dawo hannunsa rik'e dana Nawaz da gudu ya rjn [10/26, 9:24 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page3⃣1⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION* D.B.W.A *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* Jabeer yad'an fahimci wani abu akan fuskarta amma bai son yi mata bin k'wak'k'wafi ya d'auko wata leda a cikin mota ya bata don Nawaz tuni ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63