Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 36

Chapter 36

Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ba, ba'a shiga tsakanin Bawa da ubangijinsa ni bana aikata manyan aiyuka bana shan giya bana sata, kisa bare fashi da makami, to menene a ciki kawai don mutum yayi rayuwar da yake ra'ayi tajin dad'i sai ace ya sab'i Allah? Ina sallah, azumi da bin iyayena to menene saura kuma?" "Haka ne to amma ina batun b'angaren Mata naji ka keb'ance shi ko shi baya cikin manyan lefuka? Ba wani inkari da zakayi don kai Gwani ne ta wannan fannin" ya sosa k'eta "kin gane Allah gafurur rahim ne, wannan va wani abu bane kawai lokaci ne daga na aure ki zan daina, don nasan zaki gamsar dani bani da lokacin bin wasu matan" ta dubeshi "hali zanen dutse, a duniya babu abinda nake k'yamata kamar miji mai neman mata, kai kuwa ya zame maka jiki duniya ma ta shaida haka, to saboda me ni kuma zankai kaina ga halaka?" Wani abu ta gani a idanunsa da alama maganarta ta tab'ashi sosai, bai ce komai ba ya fita, tayi d'an murmushi ta k'arasa aikinta. Yana parlor bai tafi ba ta ajiye musu abinci ta koma d'akinta ta gyara don da bata nan yayi k'ura, saboda tunda ta tafi Nawaz ya koma wajen daddy'nsa da kwana. Tayi sallah a gajiye take ta kwanta cikin tunani daban daban, tun daga sanda Faheem yaje gidan Umma, tana jiyo kalaman Umma ko ya ta d'auki Faheem? Lallai yana da k'ima da girma a gunta bata tab'a yi mata maganganu masu zafi haka ba................ *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:25 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page3⃣6⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION* D.B.W.A *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* Washe gari da safe ta shirya zata tafi school taga Nawaz bai tafi ba yama cire uniform tace "Nawaz ina shirin makarantar?" "Aunty Hibbah daddy ne yace yau bazan je ba uncle d'in mu ya bani hutu sai gobe," tayi murmushi "to haka ake so Nawaz Allah ya k'aro sauk'i, ni kuma zan tafi school saina dawo" "aunty Hibbah ki tawo min da chocolate" ta shafa kansa "a'a Nawaz doctor ya hana shan zak'i saboda ciwon ciki" tana rik'e da hannunsa suka fito har bakin gate suka gaisa da Isah, yana tsaye a wajen Isah ya d'aga mata hannu "Aunty Hibbah bye bye sai kin dawo," ita ma ta d'aga masa hannu gami da fita daga gidan, ta soma tafiya har ta k'arasa bakin titi. Ta jima a tsaye bata samu mota ba, duba agogo tayi taga ta kusa latti ta soma tafiya ko zata samu a gaba. Hon don haka ta kauce ta basu hanya, "Aunty Hibbah" juyowa tayu don jin muryar Nawaz, shine da Daddy a motar, sanye yake da T shirt ta d'an d'ame shi, sai ya koma mata kamar Faruq don shi bai saba d irin wannan shigar ba yafi sabawa da shigar manyan kaya. Nawaz ya fito ya bud'e mata baya, dak'yar ta shiga tace "daddy barka da safiya" "lafiya lau Hibbah, wane school kike ne? Ko kema kina inda su Saudat suka gama?" Tace "eh" Shiru ya ratsa sai Nawaz dake ta suruntunsa, Hibbah kuwa zancen zuci take tana mamakin Faheem wane irin mutum ne shi Wanda ta kasa saboda dashi har yau. Sun iso makarantar ya ajiyeta a bakin gate, tana k'ok'arin fita taji yace "k'arfe nawa zaki tashi?" "K'arfe biyu ne" "ok ki jirani" a sanyaye ta fita daga motar, ta kasa shiga school d'in tabi motar da kallo. Ji tayi an dafata ta d'an tsorata ta waiwayo Fauzy ce tana mata dariya "Hibbah me kike jira ko har kin fara duty ne yau?" Hibbah tayi dariya "a'a Fauzy ai kema kinsan bana fara duty da wuri, yanxu fa nazo" fauzy taja hannunta "zo muje class da labari fa su momy sun amince da Ya Nazeef" Hibbah tana murmushi tace "da gaske?" "Wallahi kedai muje na baki labari," suka k'arasa class. Ranar wani yanayi ne mai dad'i a ranta kawai tunanin Faheem ya tsaya mata a rai haka komai nashi take gani harta yarda yake yin tuk'i a nutse da kalamansa masu saka nutsuwa, Allah mai iko wai har takai matsayin da zai kaita school bayan ba komai bace ita sai 'yar aikinsa, Anya kuwa zak'ewar batayi yawa ba, ko da yake Faheem da Aunty halinsu iri d'aya ne sun d'auke ta ne a matsayin 'yar uwa ne ba 'yar aiki ba, kuma yana girmamata gashi akwai kunya da nauyinsa da take ji don bata iya hawa motarsa don dai bata iya yi masa musu. Wani tunani tayi, yanzu idan Kausar ta gano tana shigar mata motar miji ai ta shiga uku, Anya kuwa bazata gudu ba idan yazo yaga bata nan ai zaiyi tafiyyarsa, kuma tunda ba wata magana suke yi ba bazai tambaye ta ba. Ana tashi kuwa tayi sauri ta had'a komai nata suka yi sallama da Fauzy, tana fitowa gabanta ya fad'i ras, mamaki take yi kamar a mafarki anya Faheem ne kuwa? Ikon Allah, tasan ya ganta babu maganar tserewa. Yana kallon ta ta cikin glass ya Gaza d'auke idanunsa, magana yake a waya amma duk hankalinsa yana kanta sai yaji maganar ma tana neman gagararsa, ya had'iyi wani abu sai kace sihiri ya manne mishi kamar mayan k'arfe. Kamar ta nutse Sam ta kasa dubanshi tunda ta shiga motar ai gara d'azu da Nawaz shi yana gaba ita tana baya, wai wannan wane irin nauyi ne da kunyar Faheem Allah ya d'ora mata. Haka sukayi shiru a motar tamkar kurame, Faheem akwai shi da nutsuwa da lafazi a tausashe "Hibbah" ikon Allah saura kad'an numfashinta ta d'auke, shima sautin muryarsa ya sauya. "Ina son muyi wata magana kin shirya saurare na?" Muryarshi tayi sanyi duk sai yasa ta wani yanayi da bazata manta shi ba a ranar, "nafi son ki bud'ame baki kiyi min magana tunda nima mutum ne kamar ke ki daina wani d'ari d'ari Dani, ni na d'auke kine tamkar 'yar uwata" yayi murmushi dayaga ta d'an Saki ranta "mene a tsakaninku da Faruq? Ki fad'amin gaskiya kinsan dai Faruq k'anina ne ke kuma amana ce a hannuna Hibbah" shiru tayi, "Hibbah bakice komai ba" "daddy shine yake zuwa........." "Nasan shine yake zuwa ma'ana maganar daya shafi soyayya" ta d'anyi shiru "gaskiya batun wannan bansan a muhallin da zan iya ajiye Faruq ba, shidai a cewarsa wai zai aure ni...." " kin tabbatar kina sonshi?" Zuciyarta ta shiga harbawa a ganinta cin fuska ne tace bata son d'an uwansa ciki guda. Ya sauke ajiyar zuciya "baki ce komai ba hakan na nufin kinason shi kenan?" Ji tayi gabanta yayi mugun fad'uwa tace "Daddy magana ce mai nauyi zan fad'a amma ba'a wannan lokacin ba" yay d'an murmushi yaji dad'in wannan furucin nata. Yayi parking a wani babban shop ya shiga ya d'an jima a ciki kafin ya fito, tunda ya fito ta k'ura masa ido ta glass d'in tana kallon sa da yake glass d'in a rufe yake kuma mai duhu ne, tabbas wani abu take ji yana ratsa zuciyarta ko mene wannan d'in? Yabshigo motar k'amshinsa kawai yana mata dad'i mutum ne gentle, ya ajiye ledojin a kujerar baya suka tafi. Nawaz yana ya biyo su, yana gama parking ta shige gida ta barsu anan. Tana

Table of Contents

Chapters

63 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});