Chapter 52
Chapter 52
"ba komai Aunty" Nawaz ya kwanto a jikinta "Aunty me yasa ki kuka?" Aunty tace "haba Hibbah ya kina kuka kuma kice babu komai don Allah ki fad'a mana me ya saki kuka me kike tunani?" Hibbah ta k'ara goge hawayen dake zuba a idanunta,"Aunty kuyi hakuri wallahi ina tsoran komawa k'auye ina tsoron Inna lami nasan halinta zata iya kashe ni, tunda tayi min gargad'in karna kuma waiwayar garin" Hibbah ta fad'a hawaye na bin fuskarta. Faheem yana daga can gefe "karki damu Hibbah babu abinda ta isa ta yi miki Wanda Allah bai nufa zai same ki ba ki tuna baya taso ta lalata miki *RAYUWA* ta tozar taki amma da yake Allah ba azzalumin sarki bane sai ya hana faruwar hakan sannan ta turoki birni don ki zama k'ask'antacciya shima hakan sai ya zame miki alkhari don haka ki cire wannan tunanin daga ranki, mu duka nan muna tare dake Allah na tare dake babu abinda ta zai sameki da yardar Allah" Hibbah ta gyad'a kanta cike da gamsuwa ta kuma ji dad'in kalaman Faheem, "Kai Aunty Hibbah kin fiye tsoro da yawa" Saudat ta fad'a tana dariya, Hibbah tayi mata hararar wasa Safiyya tace "ai tsoro halal ne kuma kema kina yi Aunty Hibbah nima ina bayanki ki cigaba da jin tsoro wallahi mutumin da yace zai kasheka kuma kasan halinsa zai aikata ai dole kaji tsoransa" Abba yace "haka ne amma Hibbah ina son nasan wani abu game dake, don ni har yanzu zuciya ta tana raya min wani abu game dake kuma inajin wani abu a tattare dake" dukkan ninsu suka maida hankalinsu kan Abba, ya cigaba "Hibbah tun d'azu dana ji muryarki nake jin zuciyata na harbawa danaga fuskarki kuma k'irjina ya tsananta bugawa idan kika yi magana kina tunamin wani mummunan abu daya faru a baya, kina tuna min k'anwata Aysha da nake matuk'arso" Hibbah ta kasa fahimtar inda kalamansa suka dosa "Abba ni wallahi ban fahimce abinda kake fad'a ba" Abba yayi d'an shiru yana tunani, su Daddy dasu momy kuwa duk so suke suji abinda ya faru da Abba mene shi kuma had'insa da Hibbah? Abba cikin murya mai nuna tausayawa yace "Hibbah Aysha da kike kama da ita k'anwata ce iyayenmu d'aya mu biyu ne a wajen iyayenmu, mahaifimu d'an kasuwane tare suke kasuwanci da mahaifin Daddy'n ku. Ranar juma'a da rana bayan sallar juma'a su Alhaji da hajiyarmu zasu yi tafiya zuwa k'auyukan dake zagaye da garin kano, Alhaji ya saba duk juma'a yakan je k'auyuka ya kai musu tallafi, sun saba da Aysha suke tafiya ni kuma a barni a gidansu Daddy lokacin Aysha tana da shekara biyar a duniya. A hanyar su ta dawowa ne daga k'auyen suka had'u da 'yan fashi........... Inna lillahi wa inna ilai hirra ji'un" Abba ya fad'a hawaye yana bin fuskar sa yasa tissue ya goge hawayen sanna ya cigaba "suka buk'aci kud'i daga wajen su Alhaji lokacin Alhaji babu kud'i a wajensa don haka ya fad'a musu cewa babu kud'i a wajensa, babu ko imani suka harbeshi a k'irjinsa suka hajiya ma tare da driver'nsu amma basu harbi Aysha ba ogansu yace su k'yaleta. Haka suka barsu a k'asa a kan titi suka tafi da motar, Aysha ta zauna a wajen tana ta kuka daga baya kuma ta tashi ta shiga cikin garin don shaida musu abinda yake faruwa tun daga nan ba'a kuma ganinta ba. Bayan an kawo gawawakinsu na irin Neman da ba'a yiwa Aysha ba amma ba'a ganta ba. Naji mutuwar iyayena nayi kukan rashin Aysha, daga lokacin ne Alhajin su daddy ya d'auke ni ya cigaba da rik'eni." Abba ya kuma share hawayensa yana kallon Hibbah yace "shiyasa zuciyata take raya min ko Aysha tana raye ke 'yarta ce" Hibbah da itama hawayen take yi na tausayawa Abba tace "Abba saidai muje wajen Umma a tambaye ta amma ni nasan a k'auyen mu Ummana ta taso don iyayenta ma suna raye har na baro k'auyen" Daddy shima cike da tausayi yace "babu matsala sai muje muji ta bakinta, ku tashi mu tafi" Nan suka shiga had'a kayayyakin suka zuba a mota suka huce gidan daddy............... *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:27 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page4⃣8⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* Suna zuwan wanka sukayi kawai suka shirya Faheem da Kausar kuwa saida zukaje gida suka kintsa a can Kausar ta tawowa da Hibbah kayanta, Aunty ma saida taje gidanta anan ta kira Sagir mijinta take fad'a masa abinda yake faruwa yayi mata izinin zuwa kuma yayi mamaki ashe su *dangin juna* ne shiyasa Allah ya dasa musu k'aunar junansu. Su Aunty suna dawowa Daddy yasa Adamu ya fito da mota Daddy da Abba suka shiga baya, yayin da motar Faheem kuma Kausar ta karb'i tuk'in shi kuma yana gefenta mamy momy da Hisham suna baya. Motar Aunty kuma Hibbah tana kusa da ita Nawaz yana kan cinyarta sai Safiyya da Saudat a baya, sai hira suke cike da k'auna a haka suka k'ara gidan Alhaji Sani. Sunyi sa'a yana gida don shigowarsa kenan daga masallaci motocinsu sukayi parking a gidan, yayi mamakin ganin zugarsu haka da yawa amma duk da hakan bai hanasa tarbarsu cikin karamci ba yayi musu iso cikin gidan direct ya shiga dasu har parlor. A parlor suka tadda Umma ita kad'ai kana zaune tana sauraron karatu Wanda kana shigowa parlor'n zakaji yana tashi. Tana ganin su Aunty sun shigo ita dasu Hibbah, Saudat, Safiyya da Kausar ga kuma mamy da momy ta tsayar da karatun ta taresu da murna suka zazzauna akan kujerun parlor'n tana ta yi musu sannu da zuwa. Ta cika musu gaba da abinci kala kala ga lemuka sannan suka shiga gaisawa, anan su momy suke fad'a mata basu kad'ai bane tare suke da mazajensu amma su suna tare da Alhaji zasu shigo daga baya Umma tace to shikenan dama da hijab d'inta a jikinta ita a lokacin ta idar da sallah. Sun d'an tab'a abinci suka shiga hira kamar sunsan juna, karb'ar da umma tayi musu ta burge su sosai sunji dad'i, suna cikin hira su Abba suka shigo da sallama suka amsa musu, kallonta Abba ya tsaya yi zuciyarsa na harbawa da k'arfi tabbas babu tantama wannan itace Aysha k'anwarsa don ga muryarta nan ga kuma kamanninta nan sak dana hajiyarsu. Ya ilahi! Ikon Allah kenan dama ashe zai kuma sanya Aysha a idanunsa, suka zauna ta kawo musu abubuwan tab'a baki, sai binta da kallo yake tabbas itace ga tafiyarta nan ma. Kallon da Abba yake mata ya fara b'ata mata rai don duk inda tayi saiya bita da kallo don haka lokaci d'aya umma ta had'e rai. Bayan sun d'an huta Alhaji Sani ya fad'a mata wajenta suka zo ba wajensa ba umma ta mayar da hankalinta kansu tana son jin meke tafe dasu don ita tayi tunanin ma akan maganar auren Faheem da Hibbah ne. Daddy ne yayi gyaran murya ya gyara zama ya shiga bata labarin abinda ya faru ya kuma tabbatar mata da cewa Hibbah 'yarsu ce basu sani ba. Umma hawayen farin ciki ya sauko mata "alhamdulillah naji dad'in wannan al'amari ikon Allah kenan ashe 'yar kuce shiyasa Allah ya sanya k'auna a tsakaninku
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63