Chapter 56
Chapter 56
fad'i jin muryar Hibbah cikin rud'ewa ta mik'e tsaye tayo kan Hibbah Wanda itama tuni tayi kan baba da masifa take magana "muryar wa nake ji kamar ta Hibbah me ya dawo dake garin nan baki ji gargad'in da nayi miki ba ko?" Kausar dake gefenta tace "itace Hibbah ce kuma ta dawo ne don ceto rayuwar mahaifinta daga hannun azzalumar mace irinki" cikin d'aga murya Inna tace "ke Kama kanki ki nutsu ban kasa dake ba da zaki d'auka" ta kalli Hibbah da tayi tsuru tsuru ta fizgota ta d'aga hannu zata mareta Faheem ya rik'e hannun "karki sake ki tab'a min mata, kina tab'ata sai dai a kwashi gawarki" "idan ba'a kwashi gawata ba za'a kwashi gawarta yanzu ba sai gobe ba, wallahi alkawarin da na d'auka saina cika shi na indai Hibbah ta dawo garin nan sai na kasheta" Faheem ya tura Hibbah kusa da Inna "gata nan don Allah ki kashe ta ki kasheta nace" Inna ta buga mai wani mugun kallo "ku jirani nan da mintuna kad'an" ta zari mayafinta ta fita tana masifa. Hibbah ta kuma saka kuka Kausar ta janyota jikinta "kiyi shiru Hibbah babu abinda Bawa ya isa yayiwa d'an uwansa Bawa wanda Allah bai nufa zai same shi ba ki kwantar da hankalinki babu abinda ta isa ta yi miki" Rahmatu dake d'aki jin fitar Inna ta fito don Inna hanata fitowa tayi ta d'auko kwano cike da ruwa ta mik'awa su Abba, Abba ya amsa ya d'iba a hannunsa ya safa a fuskar baba, baba baiyi motsi ba ya kumayi nan ma shiru har sai da yayi sau uku baba bai motsa ba nan hankali su ya mugun tashi har sun yanke shawara d'aukar shi zuwa asibiti sai kuma.............. *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:27 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page5⃣1⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* *Kulawarku da damuwa da littafina ya sani cikin farin ciki na gode sosai, masu kirana a waya basu samu ba da masu min magana ta what's up kuyi hakuri ina busy ne.* Sai kuma baba ya ya sauke wata sassanyar ajiyar zuciya a hankali ya fara bud'e idanunsa ya sauke su akan na Daddy shima da Daddy kallon sa yake zuciyarsa duk ta karaya hawaye na zuba a idanunsa. A hankali baba ya d'ago hannunsa ya d'ora a saman fuskar daddy ya shiga goge masa hawayen yana masa murmushi "ka daina kuka d'an uwana ban Sonka da zubar hawaye" Daddy ma murmushi yayi "ai dole ne Mukhtar munyi kewar rashinka munyi kuka har mun gaji munsa a ranmu ka rasu sai yanzu muka sami Labarin kana raye kaga kuwa dole mu zubda hawaye farin ciki" baba yayi murmushi yana kallon duk mutanan wajen babu Wanda ya Sani a cikinsu banda momy da mamy sai kuma Faheem da yake ta kallo yana son gano waye? Ya dubi momy da mamy da suke ta matsar k'walla "autar hajiya da matar Yaya ku daina kuka Dan Allah ku matso gare ni" a hankali suka matsa kusa da baba ya rumgume su tamkar yara suka fara kuka yana d'an bubbuga bayansu. Baba ya d'ago kansa yana kallon Abba suna yiwa juna murmushi da kuma hawaye a fuskokinsu, baba ya d'an saki su momy ya kuma duban Abba "babban Yaya wai wad'annan duk 'ya'yana ne?" Abba ya d'aga masa Kai "naka ne duka Abban Aysha" mamaki ne ya bayyana a fuskar baba yace "Abban Aysha wace Aysha? Ni banga Aysha ba da hajiya suna ina?" Da sauri daddy ya d'ago kansa jin mutanen da k'anin nasa yake tambaya hawayensa suka tsananta zuba, Abba shima hawayen yake yi yace "kayi hakuri Abban Aysha sanadin cutar da ta sameka a wannan daren Allah yayiwa hajiya rasuwa sanadiyyar hawan jininta daya tashi, Aysha kuma tashin hankali ne yasa ta nak'uda a lokacin ta haifo 'yarta mace shine aka saka mata sunan Aysha saboda ita ma Aysha bata rayu ba." Inna lillahi kawai baba yake furtawa zuciyarsa na masa zafi a sannu rayuwar da sukayi da mahaifiyarsa da matarsa ya Fara tunowa sai kuma hawaye suka fara sauka a saman fuskarsa yasa hannu yana gogewa yana mai yi musu addu'ar samun rahamar ubangiji. Su Kansu su daddy hawayen suke yi saboda tuno mutuwar da sukayi sai filin tsakar gidan yayi shiru sun d'auki wasu lokuta a haka kafin baba ya katse shirun da cewa yana murmushi "wace Ayshan a cikinsu? Duk sun d'auko kama iri d'aya" daddy ya dubi Aunty "Aysha matso Gare shi zo ga mahaifinki" Aunty ta taso ta zo wajen baba, shi kuwa baba cikin happy ya rumgume ta k'aunarta na ratsa duk ilahirin jikinsa ita kuwa Aunty kuka take ga k'aunar mahaifinta na shigarta sun d'auki lokaci k'amk'ame da juna baba ya d'ago yana kallon su Kausar "yarana ku matso gare ni kuzo naji d'umin jikin yarana" ya fad'a yana bud'e hannayensa, matsowa su duka suka yi banda Hibbah dake gefe kusa da Umma tana ta kuka zuciyarta cike take da tsoron abinda inna ta fita yi shima Nawaz bai tashi ba yana jikin Hibbah yana goge Mata hawaye wai tayi shiru . Su Saudat kuwa baba had'asu yayi ya rumgume su yana mai jin k'aunar 'ya'yan 'yan uwan nasa na ratsa shi, sun dauki lokaci kafin ya sakesu ya kalli Faheem "babban Yaya kar dai kuce wannan ne Faheem nawa" da murmushi Abba t?yace "shine Abban Aysha" baba ya dubi Faheem yana dariya "lallai na dad'e rabona da ku dubi fa yadda ka zama babban mutum, ina Haisam kuma?" "Haisam yana Abuja acan yake aiki" "to Allah ya bada sa'a ina dai fatan yanzu kun ajiye iyali ko?" Faheem ya d'an Sosa k'eya yana duban Abba. Cikin dariya Abba yace "ka fad'a masa mana" Faheem ya kuma sunkui da kai daddy yayi dariya "duk sunyi aure dashi da Haisam d'in shi ya auri k'anwarsa Kausar da ka tafi Rukayya na da cikinta har ma da d'ansu Nawaz yanzu kuma ya kuma k'aro wata a sanadiyyarta ne muka gano inda kake." Baba ya dubeshi da mamaki "wace ita?" "Hibbah ce 'yar wajenka" mamaki ne ya kuma bayyana a fuskar baba gumi ya fara keto masa "Hibbah ina kike matso gare ni kiyi min afuwa ki yafe min muzgunawar dana miki ke da mahaifiyarki, kinga Rahmatu yadda mahaifiyarta ta cutar mata da *RAYUWA* ko?" Hibbah ta matso kusa da baba Nawaz ya biyota tace "baba baka yi min komai ba na yafe maka" "ina Ummanki Hibbah?" Ta nuna masa Umma. Ya yunk'ura zai tashi daddy ya ruk'oshi, baba yayi murmushi don ya gane dalilin rik'eshin da daddy yayi "nafa samu sauki babu inda ke min ciwo" daddy ya sake shi ya k'arasa gaban Umma "kiyi hakuri Aysha ki yafe Min lefin da nayi miki don Allah" "nasan ba lefinka bane na yafe maka Allah ya yafe mana" baba yaji dad'i tace "na gode Aysha" ya dubi Nawaz "wannan ne abokin nawa?" Ya fad'a yana janyo Nawaz jikinsa ya kalli Faheem dake ta sunna Kai "Faheem wai kunyata kake ji ne? Ni ba surukinka bane fa" Faheem yayi murmushi yana kuma k'asa da kansa. Baba yayi murmushi yana mamakin yadda Faheem shi bai yadda ba kunyar shi yake ji. Abba ya d'anyi gyaran murya "k'aramin k'anina
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63