Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 47

Chapter 47

Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

take..........." Wayarta ce ta katseta ta lalubo wayar a cikin jakarta sunan da ta gani ne a kan screen d'in wayar yasa zuciyarta bugawa ta kalli Faheem, yace "waye yake kiranki?" Tayi ajiyar zuciya bata amsa sa ba ta d'aga wayar don taga ta kusa katsewa. Bai ma Bari tayi magana ba ya hauta da fad'a "kun kyauta Aysha wato saboda bakwason Faruq ya auri yarinyar da yake so shine kuka had'a baki keda Faheem kuka k'ulla tuggunku yaje ya aureta kafin naje nema masa ko, to kuzo yanzu Ku sameni a gida ina jiranku," "kayi hakuri Daddy Allah ya huci zuciyarka, amma Daddy wallahi bawai don bama son Faruq ya aureta bane dama tuntuni Faheem yake sonta kuma yaje ya sami mahaifiyar yarinyar ta bashi ita.........." Cikin fad'a Daddy ya katseta "rufe min baki munafukan banza kiyiwa shi Faheem d'in waya kuzo tare tunda ni na kirashi yak'i d'auka" Aunty ta kwantar da murya "kayi hakuri Daddy ba k'in d'auka yayi ba muna asibiti ne bashi da lafiya kuma na kira Abba da su mamy na fad'a musu" "ba wata rashin lafiya da yake yi duk k'arya ne kuzo yanzu ina jiranku idan ba haka ba ranku zaiyi mummunan b'aci" yana gama fad'in haka ya kashe wayar. A sanyaye ta sauke wayar daga kunnenta, Faheem ya kalleta "me Daddy yace miki?" Ta sauke ajiyar zuciya "Yaya Daddy yak'i saurarata yace muje yanzu yana nemanmu, na fad'a masa muna asibiti baka da lafiya yace k'arya ne idan bamu zo ba ranmu saiya b'aci" Faheem ya yunk'ura ya tashi zaune "kije ki Kira min Dr Umar yazo ya sallame mu muyi sauri muje," "a'a Yaya baka jin dad'i fa har yanzu ka bari ni naje ni kad'ai" ya kalleta "haba Aysha so kike na sab'awa su Daddy ne? Ai rashin lafiyata ba komai bace akan sab'a musun da zanyi don haka kiyi abinda nace ki Kira min Dr" ta kalleshi tana tausayawa Yayanta, lallai ba k'aramun so yake yiwa Hibbah ba a dalilinta ya samu ciwon zuciya, gashi kuma ya d'aukarwa kansa hukuncin barinta. Ta mik'e da niyyar zuwa kiran Dr sai gashi ya shigo, suka gaisa ya shiga duba Faheem d'in bayan ya gama yayi 'yan rubuce rubucensa ya juya zai fita, Faheem yace "Dr inason ka sallameni yanzu pls" da mamaki sosai akan fuskar Dr Umar yace "saboda me? Kasan illar ciwon da kake tattare dashi kuwa? Kayi hakuri ka zauna a nan zaka fi samun kulawa" Faheem yad'an dubeshi "kayi hakuri Dr Daddy ne yanzu yayi min waya yana son ganina da gaggawa, pls ka taimaka ka sallameni yanzu karna sab'a umarninsa" Dr yayi shiru yana yaba biyayyar Faheem ga jyayensa "to shikenan Aysha biyoni office" Ya fita Aunty tabi bayansa suka je office ya bata takardar sallama da ta wasu magunguna da ake buk'ata tayi masa godiya ta dawo d'akin ta had'a kayansu suka fito daga asibitin. Wata bak'ar mota ce mai bak'in glass tayi parking a gabanta aka bud'e gidan baya tare da fizgota cikin motar aka rufe motar ta fita a 360. Cikin tsoro Aunty ta kalli Faheem tace "Yaya wannan ba Hibbah bace?" "Itace yi sauri mubi bayan motar" da sauri suka shiga motar Aunty ta figi motar a 360 suka bi bayan motar sai dai ina motar................... *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:26 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page4⃣4⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION* D.B.W.A *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* Motar tuni ta b'ace suka kalli juna ita da Faheem wanda hankalinsa ya mugun tashi, ta karyar da kai "Yaya pls ka kwantar da hankalinka kaga baka da lafiya, insha Allah ba abinda muke zargi bane zai faru da Hibbah" ya gyad'a kai "muyi sauri Daddy yana jiran mu" Aunty ta juyar da kan motar suka nufi gidansu. Babu kowa a babban parlor direct parlor'n Daddy suka nufa Faheem ne a gaba Aysha tana biye dashi suka shiga cikin parlor'n, dukkanin ilahirin gidan ciki manyan gidan iyayen nasu kenan. Faheem ya shigo da sallama Abba da su momy da mamy ne suka amsa Daddy ko kallonsa baiyi ba yana zagaye parlor'n, Faheem ya gaishesu Aunty ma haka nan ma Daddy bai kallesu ba. Faheem ya matso kusa da inda Daddy yake "don Allah Daddy kayi hakuri wallahi bani da niyyar.............." Katse shi yayi ta hanyar yarfa masa wani mugun mari cikin fad'a ya fara magana "Faheem ni zaka wulakanta ka nuna ban isa da kai ba, saboda kuna yiwa d'an uwanku bak'in cikin karya auri yarinyar da yake so shine kuka zage kai da Aysha kuka k'ulla makircinku har ka aureta ko? To baka isa ba tunda shima ya rasata dole kaima ka rasa, aikin banza da wofi yara sai bak'in cikin tsiya ni banma yarda da wannan auren ba tunda shi Abban Janan shine walilinku kuma ba zama yake yi ba za'ayi aure ne babu waliyyi?" Faheem ya sunkui da kansa yanaji rad'ad'i mai zafi a zuciyarsa baya so yaga ran iyayensa ya b'aci sam. Abba dake zaune ya kalli Daddy cikin kwantar da murya yace "Daddy'n Faruq ka tsaya kayi bincike akan abinda ya faru kafin ka yanke hukunci, ni d'innan nine nayiwa Faheem waliyyi aka d'aura auren nan, ya kirani a waya yake fad'amin damuwarsa nasan Faheem akwai shi da zurfin ciki tunda har ya fad'amin damuwarsa to abin ya dameshi, ni na bashi shawarar yaje wa mahaifiyar yarinyar da maganar Allah bashi nasara daya fad'awa mahaifiyarta ta bashi aurenta a lokacin tace a d'aura, ya kuma kirana a waya ya fad'amin cewa ta amince kuma tace ya turo yanzu a d'aura auren Allah yasa ranar na shigo kano naje aka d'aura auren, don nima ina sauri ban ma shiga mun gaisa nayi mata godiya ba saidai na barwa mijinta sak'on gaisuwar. Bayan an d'aura auren mai makon naga Faheem yana farin ciki sai naga ya shiga damuwa na tambaye shi menene kuma yake damunsa, yace min yana tunanin yadda zaka d'auki zancen k'aro auransa bada saninka ba ga kuma Kausar da yayowa itama abokiyar zama ba shiri, na nuna masa karya damu indai Kausar ce, kai kuma zanyi maka bayanin komai Allah bai bani ikon kuma dawowa kano ba sai jiya da kayi min waya mukazo yau. To kaji abinda ya faru Daddy'n Faruq tun kafin ka fad'a min Faruq nason yarinyar nan Faheem yake dakon son ta a dalilin maganar da kayi musu jiya shi kuma ya yankewa kansa hukuncin sadaukarwa da Faruq ita bayan irin son da yake yi mata, sonta ne da fargabar rabuwa da ita ga kuma dakon sonta da yayi yasashi kamuwa da ciwon zuciya" daddy yayi shiru yana sauraronsa yace "naji kuma na fahimta amma yarinyar nan Faruq ya shaida min shi take so kuma ita ta amince da aurensa, don haka ke Aysha kece mai number ta ki kirata yanzu tazo ta shaida mana wa take so a tsakaninku, oya Aysha kirta kisa muna ji" Abba ya kuma kallonsa "haba Daddy wai sai yaushe ne zaka daina nunawa yaranka bambanci? Ka dinga yi musu adalci mana" "kayi hakuri Abba ka kyaleshi ai dama yayi niyyar barwa d'an uwan nasa ita to Dan nace a kirata ta zab'i zab'inta ai ba lefi bane" Abba ya gyad'a kai kawai dama

Table of Contents

Chapters

63 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});