Chapter 15
Chapter 15
had'a abubuwan da wasu manyan babies din ma basu dashi duk da cewa yanxu suka fara tasawa abubuwan nata, amma tana da diri mai kyau da d'aukar hankali, ya tuno yadda ya ganta d'aure da towel sai ya kuma matse pillow gam a jikinsa, haka yayi ta tunaninta har dare ba mafita daya rufe idanunsa ita yake gani ga wata muguwar kasala da sha'awar kasan cewa da mace data saukar masa kasa jurewa yayi, ya tashi ya shiga toilet ya sakarwa kansa ruwa na wani lokaci kafin ya fito ya tsala wanka cikin k'anan kaya ya feshe jikinsa da turaruka masu kamshi ya zari key din motarshi ya nufi club. Su kuwa su Hibbah sunje sun kaiwa tailor d'inkunan yace nanda kwana biyar zai kawo, daganan Aunty tace zasu wuce super market zasuyi siyayya, wani babban shop na kayan mata suka shiga Aunty ta yiwa Hibbah siyayya ta had'a da kud'in hannunta duk tayo mata siyayya haka suka d'auko hanyar gida da kaya nik'i nik'i. Suna shigowa gida ana kiraye kirayen sallah don haka kai tsaye Aunty tabi Hibbah bangarensu suka ajiye kayan anan ma sukayi sallah sannan Aunty ta shiga nuna mata yadda zatayi amfani da komi har pad tace mata wannan idan kina al'ada shi zaki dinga amfani dashi ta nuna mata yadda ake sakawa. Sai bayan isha'i malam Jamil yazo bayan sun gaisa dasu momy ya tashi ya nufi d'akin da suke karatun a ciki, su Saudat suka mike kowa ya d'auki kayan karatunsa suka bi bayansa dayake hadda sukeyi a wajensa suna zuwa suka shiga Bashi hadda. Aunty tazo tayi kiran Hibbah suka tafi d'akin, bayan sun gaisa da malam Aunty tayi masa bayanin komai yace "ba matsala Aysha insha allah za'ayi yadda kikace kuma gobe in allah ya kaimu su tafi tare dasu Safiyya makarantar sai ayi mata komai zan karbi sunanta yanzu", Aunty tayi masa godiya ta koma ciki. Su Saudat sai harararta suke yi suna jin haushin yayar tasu wai akan me zata dinga had'a su da 'yar aiki. Malam Jamil ya kalli Hibbah yace "mene sunanki?" Hibbah tace "sunana *Hibbah Mukhtar Muhammed*" malam ya girgiza Kai alamar gamsuwa yace "izufinki nawa?" "Izufina sha bakwai" Hibbah ta Bashi amsa yace "hadda kikayi ko kuma biye?" Hibbah tace "hadda nayi," malam ya kalleta yace "zaki iya karanto min naji?" Kai ta d'aga, ya kalli Safiyya da take shirin fara Bashi haddarta yace "kiyi mana hakuri Safiyya bara ta biyamin naji," Safiyya tace "to malam" ya kalli Hibbah yace "bismillah" nan Hibbah ta shiga biya masa har ta gama yayi mamakin karatunta yarda take da tajwidi take fidda kowane hukunci ya jinjina mata, ya kuma yi mata k'arin karatu, saida ya tambaye ta shafi take so ko rabin shafi tace yadai biya mata kawai shafi d'aya ya biya mata, saida yaji ta iya sannan ya k'arbi haddar Safiyy........... *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:22 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page2⃣2⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION* D.B.W.A *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* *Idan kaji ana a marmatsa giwa ce ta iso, gaba dai gaba dai uwar gayya karo da karo sai rago waye zai bada tauranshi _AYSHA ALIYU GARKUWA_ ke kad'ai kike baki da sa'a.* *D*a haka malam Jamil ya gama biya musu karatu ya tafi. Hibbah tana zuwa d'akinsu tayi ta bibiyar karatun batayi bacci ba sai da ta tabbatar ta haddace sannan ta samu tayi bacci mai dad'i cike da mafarkin ummanta, tunda take bata tab'a yin barci akan abu mai taushi ba kamar nayau don katifar tana da taushi. Ta Saba k'arfe hud'u da rabi take tashi, haka yauma ta tashi, ta d'auro alwala tazo ta rik'a jero nafilfili tana godiya ga allah bisa wannan ni'ima dayayi mata. Kiran sallah assalatu ne ya d'agata daga wajen ta tada sallar asuba, bayan ta idar ta tashi Hadiza tayi itama sallah bayan ta idar ta zauna tana jan carbi, ita kuwa Hibbah karatunta ta bibiya sannanta d'ora da azkar na safiya dayake ta haddace su. Sai gari ya fara haskr suka fito da Hadiza ta nunnuna mata inda zata share bayan tagama shara ta nuna mata yadda ake mopping da goge kayan kallo, ita kuma ta shiga kitchen don had'a breakfast. Bayan ta gama gyara ko ina ta koma nasu d'akin ta gyara ta wanke toilet, Hadiza ta bata turaren wuta tace tasa a parlor kafin su tashi ta gyara musu can saman, Hibbah ta amsa tasa tuni parlor ya d'auki k'amshi. Kasan cewar yau weekend ne da wuri yaran gidan ke tafiya islamiyya don k'arfe takwas na safe suke tafiya, hakan yasa bayan sun gama breakfast suka shirya zasu tafi. Hibbah tasan tare zasu tafi don haka tayi wanka da wuri ta shirya, powder ta shafa tasa kwalli kamar yadda taga jiya aunty tayi mata, bata da hijjab d'in sakawa, ta d'auko nata tasa ta fito tayiwa Hadiza sallama. A parlor taga aunty Aysha dayake yau sunday bata da lectures, a zaune tana kallo, taje tace "aunty barka da safiya kin tashi lpy?" Murmushi aunty tayi tace "lafiya lau Hibbah ya kwanan bakunta?"murmushi Hibbah tayi tare dacewa lpy aunty" gani tayi aunty tad'an harareta tace "kinyi kyau amma kin bata kwalliyarki da wannan hijjab d'in, cireshi kizo muje sama na baki wani," tana gama fad'in haka taja hannun Hibbah suka hau sama Hibbah na binta a baya, Saida suka Fara zuwa ta gaishe da momy sannan aunty ta bata wani Hibbah Mai hannu tasa yayi mata mugun kyau, sannan ta sauko suka tafi. Safiyya tayi gaba tace "nifa wallahi bazan jera da 'yar k'auyen nan ba haka kurin ajina ya zube," Saudat tace "ai kuwa adai yanayin dressing d'in datayi babu Wanda zaice Mata 'yar k'auye, kuma ni wallahi ma k'awance zamu kulla da ita naga tana ja," kamar wadda aka zabura Safiyya tace "ke dawa zaku kulla k'awancen?" Saudat tayi dariya tace "da Hibbah mana" tsaki Safiyya ta buga tare dayin gaba abinta. Su Hibbah kuwa suka jero da Saudat, Hibbah ta rikee Hisham suna tafiya Saudat tana ta janta da hira har suka isa makarantar. Anyiwa Hibbah komai kuma an kaita ajinsu Saudat, ta Fara d'aukar darasi. Haka *RAYUWA*r Hibbah ta cigaba a gidan su Auntyn tata cikin kulawar Auntyn ta, mommy da kuma Hadiza. Sosai take jin dad'in zama a gidan, malam Jamil ma ya Fara koya Mata karatun boko kuma yaga kwazonta don idan ya biya mata nan da nan k'wak'walwarta take d'auka, makarantar islamiyyar tasu malamai nata yabon k'wazonta. Yau saura kwana biyar Faruq ya koma school, kuma yau ya kama ranar Friday, gidan ya kasance babu kowa sai Hadiza da Hibbah. Wannan al'ada ce tar 'yan gidan duk ranar Friday suke tafiya family house nasu dake zoo road, tun safe suke tafiya basa dawowa sai dare, Aunty Aysha kuwa bata zuwa sai yamma saboda yanayin karatunta. Da misalin k'arfe hud'u na yamma bayan sallar la'asar kenan Hibbah da Hadiza sun shiga kitchen zasu fara had'a dinner dayake tare sukeyin komai na girki kuma alhamdulillah Hibbah tana k'ok'ari wajen ganin ta fahimci komai, Faruq ne ya shigo fuska a tsuke sai wani muzurai yake kamar gaske ya kalli Hibbah wanda tunda ya shigo jikinta ya Fara kyarma, yayi mata duban wulakanci yace "keh!!" Da sauri
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63