Chapter 41
Chapter 41
tuna ka kusa illata yarinyar nan tun da ka d'ana mata tarko Allah ya tserar da ita, shine ka b'ullo ta wannan sigar to babu kai babu auren Hibbah 'yar mutunci bata cancanta da kai ba, kawai kaje ka cuceta da zalincinka na 'yan bariki, nasan bazata soka ba koda bata fito k'arara ta nuna maka k'iyayyarta ba don tana jin nauyi a matsayinka na k'anina, bazan goyi da bayanka ba don nasan daka gama cin moriyar gagga zaka yarda k'wauronta, tayi miji mai sonta don Allah Jabeer iyayenta sunsan da maganar auren bazan tab'a yadda ka dagula zancen ba wallahi, babu kai babu ita zan ganta itama sai naci ubanta shashashar banza kawai bata San inda yake mata ciwo ba, wato ita bata tausayawa kanta bata nemawa kanta 'yanci." Ya mik'e yana wani irin huci iyakar fusata ya fusata fuskar nan tayi jawur "Ashe ke mak'iyiyata ce a yau na tabbatar ni ba jininki bane ai hannunka baya rub'ewa ka yanke ka zubar duk lalacewata ni naki ne, kince ni d'an iskane uban bariki ne ni ba d'anta ba, wallahi saina auri Hibbah idan yaso ki dinga yankar naman jikina kina k'onawa ko kuma ki fad'i ki mutu don bak'in ciki. Wallahi zamusa k'afar wando d'aya dake koda zamu k'ulla gaba ta har duniya ta nad'e, aurena da Hibbah ba fashi don ra'ayi nane kuma babu abinda kika isa kiyi." Yayi awon gaba da center table d'in dake parlor'n glass cups d'in dake kai suka fad'o suka farfashe, ko juyiwa baiyi ba yayi tafiyarsa don ya d'au zafi. K'ofar fita sukayi karo da Sagir mijin Aunty Aysha saida ya gogi kafad'arsa, yaja baya yana kallon Faruq da mamaki, gaba yayi ko waigowa baiyi ba bare ya kula sa, ya kad'a kansa ya shiga ciki yana mamakin Faruq, ya zauna tayi masa sannu da dawowa. Ya gano tana da damuwa cikin sigar rarrashi ya matsota "haba amarsu na kiyi hakuri nasan fad'a kukayi da d'an uwan naki, kinsan su sai ana hakuri dasu a hankali zai canza" ta numfasa "kayi hakuri naga har bangajeka yayi, Faruq fitinannen yaro ne ya damu family'n mu, kullum bama shiri jituwa dashi sai fad'a don na fad'a masa gaskiya ni kuma bazan fasa fad'a masa ba sai dai muyi ta fad'a dashi" Ta fad'a mishi abinda ke faruwa. Yayi murmushi "ku mata wani lokacin tunaninku kamar na k'aramin yaro yake, Aysha ai ba'a fad'in abinda ba alkhari ba a lamarin aure idan ita kuma yarinyar tace shi take so sun had'a kansu fa, yaya zakiyi sai kiji kunya kuma har abada zai ta kallonki da wannan abin tunda bake kika haifeta ba na dai gane abinda kike hango mata, kina sonta kuma ke kin fita sanin halin d'an uwanki amma kamata yayi ki nuna goyan bayanki ki tayashi murna, ba yadda zakiyi dashi naka nakane saidai kiyi masa ta masa add'a da fatan auren ya zama sanadiyyar shiryuwarsa." Aunty ta numfasa "my dear abinda ka fad'a hakane amma karka manta fa akwai maganar aure a tsakanin yarinyar nan da Jabeer kuma har manya sun shiga sa rana kawai za'ayi sai yanzu zasu zo min da maganar banza daga ita har shi, ai itama zan sameta ne saina ci mata mutunci" "kibi abin a sannu, kum idan ita Hibbah tace bata son Jabeer ai dole ya hakura ko zakiyi mata dole ne?" Ta girgiza "to kingani kawai saidai muyi fatan Allah ya zab'a abinda yafi alkhari" "to ameen muje ka watsa ruwa ko?" Suka mik'e a tare suka shiga ciki. Faruq kuwa yana fita daga gidan Aunty cikin b'acin duk inda ya wuce sai an dube shi kamar mai shirin barin garin, gudu yake sosai a mota bai tsaya a ko ina ba sai a night club, idanuwannan a hargitse banda masifa babu abinda yake ji ransa a mugun b'ace yake ji yake kamar ana tsigar gashin kansa, tabbas da yana da bindiga da sai yayi gangancin harbin Aunty Aysha mene amfanin mak'iya a duniya ya tabbatar yanzu bashi da makiyi kamarta. Kid'a ne yake tashi kamar zai tsaga ginin wajen, ya zauna yana muzurai kamar wani kumurcin maciji, ya d'auko sigari ya kunna mata wuta wai ko zai rage zafin abinda yake ji, ya dubi mashaya barasa kala daban daban yakanji a wajen abokansa wai giya na gusar da mummunan tunani da kauda bak'in ciki ga d'an karan dad'i amma shi bai tab'a sha'awar Shanta ba, ya kansha ganye da wasu kwayoyin shima tun lokacin yana secondary school tare da tak'adiran abokansa da suke kiran kasu bad boys, amma tuni ya manta dasu shidai burinsa yaga macen da yake ra'ayi kawai yayi mu'amalarsa da ita. Hankalinsa ya kasu biyu ya kalli barasar yana kwad'ayin lasawa ya wurga idanunsa yana kallon kangararrun matan dake shawagi wurin duk baiga Wanda ransa ya biya ba don haka ya yafito hadimin wajen da hannunsa. Da harshen turanci ya gaisheshi cikin ladabi "barka da dare me kake buk'ata" ya mik'a mishi wata takarda da jerin nau'ikan barasa, ya karb'a yana d'an nazari sai ya yatsuna fuska "kowanne ka kawo" don bai san wanda xai zab'a ba. Ya dire tray da manyan kwalaban giya masu sanyi, ya d'auki guda d'aya idanunsa sun shige ciki ya k'ura mata idanu, yana tunani zuciyarshi yasha ko karya sha, ya sha kawai koya huce zuciayarsa ta raya masa. Yana kaiwa bakinsa ta karb'e kwalbar, ya cira ido da k'yar ya dubeta, siririya ce doguwa Fara Sol, tana sanye da wani bulun skirt iya cinyarta da wata 'yar figigiyar riga data manne a jikinta. Ta zauna gami da rik'o hannayensa da wani asirtaccen murmushi akan fusakarta tuni tayi awon gaba da tunaninsa, Rita kenan yana son yarinyar don tasan ta kanshi sosai da ranshi ya b'aci zata sauko da fushinsa. Ya kewaya hannunsa a k'ugunta suka mik'e suka hau sama don cin karensu babu babbaka. **** Bak'in hadarin daya taso da wata iska mai k'arfi, sannan ruwan ya sauko yana tarwatsewa bisa glass d'in motar yana sauraron wak'ar Dr Mamman shata, yau dai yana cikin annashuwa yana tunanin maganganun Umman Hibbah sun sashi farin ciki har yana hangen wata *RAYUWA* a gaba da zasuyi dole ne yayi azumin godiya ga Allah daya cika masa burinsa ya mallaka masa abinda yake matuk'ar so,shikenan ta zama mallakinsa. "Karka damu komai nufi ne na Allah, nayi farin ciku da jindad'i tsakaninku da yarinyar nan amanace, wannan ita ce k'auna domin Allah sai addu'ar alkhari, Allah ya tabbatar da alkhari zan fad'awa Alhaji yanzu daya shigo ayi komai a yau d'in nan a gama." Yayi ajiyar zuciya ya tuna maganganun masu dad'in sauraro, wannan wani sirri ne daga shi sai Allah sai kuma Umma data share masa hawayensa, tura ce takai bango har yaji bazai iya zama da kashi a ciki ba don baya maganin yunwa, don haka ita kad'ai tasan maganar ya dad'e da gamsuwa da halin dattako irin nata, don yasan zata taka rawar gani ta magance masa matsalar data addabeshi shi, shiyasa ya kai mata ziyarar gaisuwa da rok'on iri kamar uwa ya d'auketa ba suruka ba. Yana parking ya k'ura mata idanu ta cikin glass d'in motar, tana rik'e da lema tana tarar ruwan saman a wani bokitin roba shi kuma Nawaz yana Tara nashi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63