Chapter 13
Chapter 13
"Faruq baka da hankali ne daga kawo yarinya zaka nuna mata halinka, da kake kiciniyar k'wace mata towel din jikinta fyade kakeson yi mata kome? Tambayarka nake ka bani amsa." Hadiza data ke gefe tace "kiyi hakuri Aysha ki daina d'aga murya kar hajiya taji," "ai gara taji baba hadiza " tana gama fad'in haka tabi bayan Hibbah. Aunty Aysha na shiga taga hango Hibbah acan k'arshen katifar dake d'akin ta kifa Kai da gwaiwa tana ta rera kuka, k'arasawa kusa da ita Aunty Aysha tayi ta zauna a kusa da inda take tare da d'ago kanta tace "kiyi hakuri Hibbah don Allah," Hibbah cikin kuka tace "Aunty Aysha ki daina bani hakuri don allah ni nasani ahaka zan k'are *RAYUWA*ta, ko wanne namiji burinshi kawai yaga ya yaga min rigar mutunci....." Ta kuma sakin kuka Aunty Aysha tana lallashinta tare da bata hakuri. Hadiza ce itama ta shigo ta zauna a gefen katifar tace "haba Hibbah mai yasa zaki fita da wannan d'an towel d'in a jikin ki?" D'ago kanta Hibbah tayi tace "wallahi baba Hadiza banyi hakan da niyya ba ni shaf nama manta da abinda ke jikina nafito na tambayeki yarda ake kunna famfo d'in band'akin bansan yarda ake kunnawa ba." Hadiza ta kalleta yarinyar ta bata tausayi tace "kiyi hakuri Hibbah wannan ma tsautsayi ne kinji?" Aunty Aysha tace "ba wani tsautsayi baba hadiza, tun yaushe yake wannan halin? Ni wallahi nayi tunanin Faruq yabar wannan halin tuntuni ashe be daina ba. Kiyi hakuri Hibbah yanxu zanje na fad'awa momy komi don yaga yanxu daddy baya zama shiyasa kenan ya cigaba da halinsa." Murmushin takaici Hibbah ta k'ak'alo tace "babu komi fa baba Hadiza Ku daina bani hakuri, aini haka tawa k'addarae take kuma na karbeta hannu bibbiyu, kuma don allah aunty Aysha karki fad'awa kowa" ta mik'e tare da cewa "Dan baba Hadiza kunna min famfon bansan ya ake kunnawa ba." Hadiza ta mike tare da cewa "to", tare suka shiga ta nuna mata yarda zata kunna sannan ta fito, koda ta fito ma ba zama tayi a d'akin ba ta fita tabar Aunty Aysha ita kad'ai a d'akin tana tunanin furucin Hibbah. Tana nan zaune Hibbah ta fito daga wanka ta wanke kanta, gashin duk ya barbaxu a fuskarta ruwa sai d'uga yakeyi. Kallon Aunty Aysha tayi tace "au Aunty Aysha kina nan har yanzu?" Murmushi Aunty Aysha tayi tace "ina nan Hibbah akwai abinda nake so na tambaye ki ne," Hibbah ta kalleta da d'an mamaki a fuskarta tace "wace irin tambaya zakiyi min Aunty Aysha?" "So nake don allah ki bani tarihinki, kuma don allah karki boyemin komi," shiru Hibbah tayi ta ta tsaya da shafa man datake yi. Aunty Aysha tace "kiyi hakuri Hibbah kiyi wani furucine Dana kasa fassara shi shiyasa nake bukatar jin labarinki," hawayene ya fara kwaranya a fuskarta tace "haba aunty Aysha wai me yasa kike bani hakuri? A k'asanki fa nake zan baki tarihina yanxu." Nan ta shiga karanta mata labarinta. Aunty Aysha ta tausayawa Hibbah ta kalleta da hawaye a fuskarta tace "Hibbah insha Allah daga yau kinbar kuncin *RAYUWA*, kuma ba wani namiji dazai keta miki haddi na kyaleshi koda kuwa Faruq d'in ne wallahi sainayi Shari'a dashi. Kema yanxu kinzama 'yantacciya don na d'aukeki tamkar su Safiyya" Hibbah taji dad'in kalaman Aunty Aysha cikin happy ta rumgume ta tana godiya, Aunty Aysha tace "ke 'yar uwata ce Hibbah munzama jini d'aya ni dake" cikata Hibbah tayi tana murmushi, Aunty Aysha tace "tashi kisa kayanki." Mikewa Hibbah tayi ta jawo k'ullin kayanta ta d'auko wata kod'add'iyar atampa zatasa Aunty Aysha tace "baki da wasu kayan ne Hibbah wannan ai sun lalace," kasa Hibbah tayi da kai tace "Aunty Aysha duk cikin kayana wannan ne masu kyau." Tashi aunty Aysha tayi tace "jirani ina zuwa." Sama Aunty Aysha ta hau ta nufi d'akinta ta d'auko wasu kaya dasukayi mata kad'an ta had'a zata bayar, ta dawo d'akin su Hibbah ta bata tare da cewa "gwada su mu gani," wani baby pink material ta bata ta gwada ai kuwa sai gashi skirt d'in yayi mata rigar take k'okarin sawa Aunty Aysha tace "Hibbah ina bra kuma a haka zakisa rigar?" Rufe fuska Hibbah tayi tace "bani fa da ita Aunty." Dariya Aunty Aysha tasa ta kuma fit............. *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:22 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page2⃣1⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION* D.B.W.A *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* D'akinta ta kuma komawa ta d'auko mata bra ta Nuna mata yarda zatayi amfani dashi sannan ta bata waje ta saka, tana fita Hibbah tasa kayan saiga Hibbah ta dawo kamar ba ita ba. Tana gama saka kayan ta taje gashinta da kum d'in kan dressing mirror ta cureshi waje d'aya kamar yadda ta Saba ta daura d'ankwalin kayan ta tsaya a gaban dressing mirror tana k'arewa kanta kallo gani take kamar ba ita bace. Ita kuwa Aunty Aysha tana fita ta nufi bedroom d'in momy, da sallama ta shiga, momy ta amsa mata zama tayi kusa da momy tayi shiru ta rasa ta inda zata Fara, littafin da momy take karantawa momy'n ta ajiye ta kalli 'yar tata tace "Aysha fad'a min me kike so?" Da d'an mamaki Aunty Aysha tace "momy ya akai kika gano abinda ke tafe dani?" Murmushi mommy tayi tace "haba Aysha nifa uwace hak'k'i nane na fahimci duk wata matsalarku, kuma dukkannin ku idan kuna cikin matsala ina ganewa don haka meke damunki fadamin pls ina sauraron ki," kasa Aunty Aysha tayi da kanta tace "momy dama wata alfarma nakeso na rok'a a wajenki dan Allah," kallonta mommy tayi na fahimta tace "wace irin alfarma kenan Aysha?" Shiru Aunty Aysha tayi nad'an dak'ik'u kafin tace "momy akan wannan yarinyar Hibbah da aka kawo miki aiki yau," "to me kike so ayi mata?" Momy ta tambaya, Aunty tace "momy Dan allah so nake kisata a school both boko da islamiyya, na tausayawa yarinyar momy ta taso cikin k'iyayyar kishiyar uwa da kuma ta uba, ta rabata da uwarta yanzu mafa ita ta turota aikatau kuma ta gargad'e ta karta sake ta koma k'auyensu," momy cikin mamaki tace "kamar ya bangane ta rabata da mahaifiyarta ba, kince kuma ta taso da k'iyayyar mahaifinta, kiyimin bayani yadda zan fahimta" nan aunty ta fara bata labarin Hibbah kamar yadda Hibbah ta fad'a mata sannan ta d'ora da cewa "wallahi mommy yarinyar ta bani taudayi sosai, na tausayawa *RAYUWA*RTA shiyasa ma na d'aukarwa kaina alkawari kula da ita, najiyar da ita dadin *RAYUWA* koda ta hanyar bata ilimine momy pls ki taimaka min, ki bani k'arfin gwuiwa," momy tayi shiru tana jinjina hali irin na wasu matan komene ribarsu don sun sa uba ya tsani 'yarsa daya haifa? Mene amfanin ma bin bokaye da 'yan tsibbu? Ta kalli Aysha tace "bake kad'ai ba Aysha nima Zan bada gudun mawa wajen ceto yarinyar nan," d'ago Kai aunty tayi cikin happy ta kalli momy tace "da gaske momy?" D'aga mata Kai momy tayi itama tana murmushi. Aunty tace "na gode momy sosai allah ya k'ara girma da tsawon rai mai amfani," momy taji dad'in addu'arta tace "amin Aysha, in anjima idan malam Jamil yazo ki turata wajensa itama ya dinga yi mata lesson
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63