Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 59

Chapter 59

Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

daina ba, ita kuwa Hibbah duk kunyar Faheem take ji shiyasa ma ta kasa sakewa a haka har dai suka yi bacci. Inna lami kuwa sunkai wajen 3hours a ciki ita da boka kafin............. *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:27 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page5⃣3⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* ```watpad@mamyn_najmah2222``` Kafin su fito ya had'a musu wasu k'ullika ya bata "ga wannan ki barbad'a a wajen da kika tabbatar zata tsallaka daga yanzu da kika amsa karya awa d'aya baki yi amfani dashi ba sannan da kinje gida ki barbad'a tana tsallakewa da mintuna biyar ki share, karki karya k'a'ida ko guda d'aya idan aka samu matsala d'aya a cikin mu zai mutu ko ni na mutu ko ke ki mutu" babu ko d'ar a zuciyar Inna lami ta amsa suna k'ok'arin zube masa k'ud'i y katse su "wannan aikin naku yana da had'ari ku bari sai aiki yayi kyau sai ku kawo" nan suka tashi sukayi godiya suka tafi. Suna tafiya suna ta hira a kan maganin da bokan ya basu, sunzo tsallaka wani d'an k'aramin titin da zai sadasu da k'auyen katsalle da yake titi guda d'aya ne sai ji kake k'uuuuuuuuuu wata k'atuwar dab tayi shoki da su delu ma'ana tayi sama dasu a take suka zube a wajen. Can gidan kuwa ana kiraye kirayen sallah dukkanninsu suka tashi mazan suka nufi masallaci yayin da matan sukayi a gida bayan sun idar kuma suka shiga tattare gidan don Daddy yace yau zasu koma gida, suna shirin d'ora girki sai gashi gwaggo ta aiko musu da breakfast mai rai da lafiya. Nan suka amsa tare da godiya aka zauna aka nad'i girkin gwaggo bayan sun gama kuma sukayi wanka Ana ta shirin komawa birni. Ita dai Hibbah bata so komawarsu ba taso zuwa gidan Abu kodan suka juna ta kuma fad'a mata abinda yake faruwa tasan abu zata tayata murna. Haka ba don tana so ba suka gama shiryawa suka nufi gidan gwaggo don d'aukota su tafi sannan su yiwa malam sallama, da suka je ma itama ta shirya suka kuma yiwa malam godiya suna shirin fita saiga Abu ta shigo ta gaishe dasu momy sannan ta rumgume Hibbah tana murnar ganinta ita ma Hibbah cikin d'auki da murna ta rumgume Abun, Abu tace "na tayaki murna Hibbah naji dad'in wannan al'amari ashe dama rabon kiga dangi ne ya kaiki birni" Hibbah ta kuma k'amk'ameta sai dai taji bata rumgume Abu sosai ba don wani abu ya tokare tsakaninsu Hibbah ta d'an saketa ta d'an matsar da ita daga jikinta tana son ganin mene abun da ya hanasu had'a jiki sosai. Ido Hibbah ta zaro da mamaki tana kallon Abu tayi k'asa da murya tace "Abu me nake gani ciki?" Abu ta d'an buge kafad'art "ni har kin bani tsoro wallahi ji nake wani abun ne, to cikin bashi bane ribar aure" Hibbah ta rik'e baki tana mamaki wai Abu ceda ciki kenan itama dole ne ta k'unshi nata?" Ta girgiza Kai Anya kuwa zan iya? Abu ta dafata "tunanin me kike yi?" "Ba komai waya fad'a miki nazo garin nan?" Hibbah ta tambaye ta "Abban Amina ne ya fad'a min" kallon ta Hibbah tayi da mamaki "waye kuma Abban Amina?" Abu tace "au a shefa baki santa ba, 'yar da na Haifa ce ta rasu" "au wai kina nufin wannan cikin bashi ne na farko ba? Tab kina k'ok'ari" "k'ok'arin me?" "K'ok'arin d'aukar wannan cikin" dariya ma Hibbah ta Bawa Abu tace "kema zaki d'aukane" Saudat dake gefensu tana jin duk abinda suke cewa tace "tab har na hango Hibbah da k'aton ciki nan kina tafiya da k'yar" ta kuwa kwashe da dariya. Hibbah ta harareta bata ce komai ba, Saudat ta cigaba "kinga dama Daddy yace nan da sati biyu zaki tare kinga kenan nan da wata tara zamu so suna" Abu ta kalli Hibbah da mamaki "au Hibbah kinyi aure kema?" Da Sauri ta katseta "k'arya fa take yi" Saudat tayi zaraf "wallahi da gaske nake sanadin auren ne ma yasa muka zo garin nan kuma ki tambayi su gwaggo" "na yarda ma wallahi, to ke Hibbah ai ba'a b'oye abin alkhari" ita dai Hibbah bata ce komai ba sai hararar Saudat da take yi. Suna nan zaune sukaji sallama babban mutum ne wai baba yake nema, baba ya tashi ya fita abinda ya gani ne ya sashi juyowa gida da sauri ya shigo duk a hargitse kallon mamaki su Abba duk suke masa suna tambayar lafiya? Yama kasa magana waje kawai yake nuna musu ganin ya kasa magana yasa suka mik'e suka fita don ganin abinda ya rikita baba. Inna lillahi kawai suke kira duk sun firgita da abinda suka gani, Inna lami ce da delu a kwance a k'ofar gidan inna k'afafunta sun cire fit babu hannaye ga idanunta ba duk bata gani sai surutai take yi "wallahi Hibbah saina ga k'arshenki dama saida boka halakakke yace karna sake na bari ki dawo k'auyen nan idan kika dawo akwai mummunan al'amari da zai faru kuma na gargad'eki karki dawo amma sai da kika dawo gashi nan munje wajen bokan mun tadda shi yana ci da wuta don haka kema sai na k'onaki" sai kuma tasa wata muguwar dariyar da ta tsorata su duka wajen ga 'yan k'auyen duk sun zagayeta. Sai da tayi mai isarta sannan ta tsagaita dariyar "na tsaneki Hibbah bazan iya barinki kiji dad'in rayuwa ba shiyasa muka tafi wajen wani bokan yayi amfani dani ya bani wasu k'ullika yace ina komawa gida na barbad'a miki kar na huce awa d'aya ban barbad'a ba, kuma idan na barbad'a miki kina tsallakewa na share kar yayi mintuna biyar ban share ba idan ba haka ba ni ko shi d'aya a cikinmu zai mutu, mun tawo akan hanyar mu ta dawowa mota ta bigemu........" Sai kuma tasa wata muguwar dariya can kuma tasa kuka kamar yarinya wai ciwo jikinta yake mata "wayyo malam jikina ciwo" sai ta kuma sa dariya "malam kaima nice nayi maka asiri don karka koma garinku saboda inasonka bayan nayi maka asiri ne na fad'awa baba shine ya aura maka ni. Kuma nice na rabaka da Aysha da Hibbah nasa ka tsanesu nayiwa Aysha sharrin zina nasa ka rabu da ita Hibbah ma nice na tura mata kwarto d'akintaaaaa!" Sai ta kuma fashewa da da dariya. Gaba d'aya jikinsu yayi sanyi sai kallonta suke yi hauka take sosai tana ta fad'in abinda ta aikata, delu kuwa dake can gefe ko numfashi bata yi da alama ma ta mutu. Rahmatu da Hibbah sun had'a Kai sai kuka suke yi Rahmatu wani zugi take ji a zuciyarta ace mahaifiyarka na aikata shirka yanzu kuma ta haukace a wajen bin bokayen nata gashi ba hannaye ba k'afafu ba idanu wannan kad'ai ya ishi masu yi isara. Mijin delu dake gefe ya dubi baba "malam Mukhtar kaga *RAYUWA* ko kaga aikin bin bukaye ko wallahi nayi danasanin kasancewarta mata a wajena Allah ya isa tsakani na dake delu bazan yafe miki ba" daddy yayi saurin kace shi "a'a malam ba'ayi haka ba ba'a bin mamaci da mummunar addu'a kayi mata fatan rahmar ubanjgiji kawai" mijin delu ya gyad'a kai zuciyarsa na k'una yace "Allah yayi

Table of Contents

Chapters

63 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});