Chapter 7
Chapter 7
ganin ta kauda kai bata takurata ba ta ajiye kwanon, tare da maida ta ta kwanta ta rufa mata zanin data rufa dashi tace "kiyi hakuri insha allah yanzu zazzab'in zai sauka," kallon ta Hibbah tayi tace "gwaggo kaina fa?" Sannu gwaggo tayi mata tare da mikewa tace "ina zuwa," bayan kofa ta nufa tadauko ruwan zafi a buta da take ajiyewa ta zuba a roba ta sirka dana sanyi ta kawo gaban Hibbah ta ajiye taje gaban buhun bakkonta ta dauko dankwalin kayanta sabo. Kasancewar ita bata daura dankwalin atampa. Ta rabashi biyu ta karaso kusa da Hibbah ta zauna ta janyo robar ruwan ta tsoma dankwalin a ruwan ta matse ta d'ora a goshin Hibbah ta shiga gogewa a hankali. Haka tayi tayi mata har wajen daya kunbura yad'an koma Hibbah sai raki take mata. Bayan ta gama ta dauko d'ayan d'ankwalin ta daure mata wajen dashi sannan ta kuma kwantar da ita. Gwaggo ta d'auki ruwan robar takai bakin kwata tace da safe zata zubar itama tazo ta kwanta a hankali barci yayi awon gaba dasu. Baba kuwa koda ya koma d'akinsa shiru yayi yana ta tunani yarasa meke masa dad'i kuma ya rasa tunanin me yake yi da haka shima barci ya d'aukesa. B'angaren Inna kuwa koda ta ja Rahmatu tana zuwa cikin dakin ta shiga zakinta ta inda take shiga bata nan take fita ba. Ita kuwa Rahmatu ko a jikinta tace "to amma Inna me yasa wai baki k'aunar Hibbah ne, nifa gaskiya abinda kike yi mata Sam bana jin dad'i kawai dai ina boyewa ne kawai kita wani sata wahala haka kawai?" Inna kallon ta take cike da mamaki wata dabara ce ta fado mata tace "ke wai bakya kishin yarda kowa yake yabonta ke ba'a yabonki kuma baki ga tafiki kyau da farin jini ba ko a wajen k'awayenku?" Shiru Rahmatu tayi can tace "eh wallahi nima fa shiyasa wani lokacin nake ji bana sonta, amma kuma me yasa kikayi mata sharrin nan kika sa baba ya koreta?" Inna tayi murmushi tace "ai duk saboda ke nayi, ke kin damu da *RAYUWA*rta ne bayan ita bata k'aunarki ta tsaneki ke kuma kina nan kina tausayinta," ta karashe da tsaki. Rahmatu tad'an zaro ido waje tace "dama bata sona?" Inna tace "ina zata soki bayan uwarta ta tusa mata tsanarmu shiyasa nayi waje da uwar itama kinga gashi ta tafi, kinga yanxu dana yi haka ai sunanta ya b'aci a gari kinga yanxu kowa zai tsaneta, saboda abin kunyar da tayi sannan ke kuma su dawo sonki" Dariya Rahmatu tasa tare da ihun dad'i tace "Kai amma naji dad'in haka inna Ashe itama bata sona shiyasa d'azu da ina tambayarta meya sameta tayi banza dani, to nima na tsaneta inna." Inna cikin happy tace "yauwa y'ar gari" daga haka suma sukayi bacci. *Dan allah kuyi hakuri da wannan, muna biki ne bansamu time nayi typing dayawa ba.* *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:22 PM] Maman Najma Author P1: πππππππππ *RAYUWA* page1β£0β£to1β£1β£ *NA* *MAMYN NAJMAH* πππππππππ *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* Da hanzari baba ya fito daga dakin cikin bacin rai da tsana yake bin Hibbah da mugun kallo, Hibbah ta tsorata da kallon da yake mata. Abu ta matso kusa da ita ta kunce Dan kwalin kanta ta mika mata tana cewa "rufe k'irjin ki da wannan," karb'a Hibbah tayi ta daura shi a k'irjinta. Cigaba baba yayi da binta da mugun kallo yana karasowa kusa da ita hannunsa ya daga ya yarfa mata wani gigitaccen mari, kafin ta dago ya kuma dagota da dayan b'angaren, cikin kakkausar murya yake magana "ni zaki wulak'anta ki batawa suna a gari Eye? Wato kinyo gado koh?" Ya cigaba da dukanta. Inna lami cikin kissa tazo ta shiga gaban baba tana cewa "haba malam kaima kasan barewa bazatayi gudu d'antq yayi rarrafe ba, taga uwarta nayi itama dole tayi." Cikin muryar kuka har tana sarkewa Hibbah take cewa "wallahi baba fyade zai yi min bani na gayyato shi ba, kaga rigata ma ya yaga min saboda naki bashi hadin kai." Abu ce taje gaban baba ta tsugunna tana bashi hakuri "kayi hakuri baba, da gaske ne ba ita ta kawo shi ba shi ya kawo kansa kuma wallahi baba fyade yaso yayi mata." Kallon Abu yayi yace "me kika sani? A gaban ki akayi?" Girgita masa Kai tayi tace "a'a baba ba agabana akayi ba," dauke kansa baba yayi daga gabanta yace "kinga kenan kema baki da tabbacin ba ita ta kawoshi ba, tunda baki da wata sheda daza ta tabbatar min da hakan." Cikin daga murya da b'acin rai ya nuna Hibbah dake gefe a tsugunne tana ta rusa kuka yace " baza ki maida min gida bariki ba ki tattara kayanki ki barmin gida!!" Furucin baba ya tsorata kowa dake wajen, cikin rudu Hibbah ta taso da gudu ta rike kafafun baba tana kuka tace "don allah baba kayi hakuri wallahi bantaba aikata abinda kake zargina dashi ba, fyade zaiyi min baba idan nabar gidan nan ina zani baba babu inda nasani." "Kibi uwarki kema ki shiga duniya!" Muryar inna lami sukaji tana bada amsa. Kallon ta su Abu sukayi, cikin tsana Abu take hurga mata harara ta kalli baba tace "Baba ina da sheda," "mece shedar taki?" Baba ya tambaye ta. Karasawa tayi kusa da Hibbah ta tallafo fuskarta tana nuna goshinta tace "Baba kalli koshinta inda ta yanke," Baba ya kalli goshin nata tare da kawar da kai. Abu ta cigaba"saboda taki bashi hadin kai ne ya buga mata Kai da kofar dakin ta yanke, sannan ga rigarta ma inda ya yaga Mata duk saboda bata bashi abinda yake so ba. Na tabbata Baba da ita ta gayyato shi baza ta bari ya yaga mata sutura koya ji mata ciwo ba. Da kuma shima bazata............" "Malama wannan duk zancen banzane!" Inna lami ta katseta cikin fada. Shiru baba yayi yana nazarin kalaman Abu ya kalli inna lami yace "lami lamarin yarinyar nan fa akwai k'amshin gaskiya," cikin fada Wanda ya zame mata jiki inna lami tace "eh dama dole ka fadi haka kai ga mai 'ya koh? To wallahi ni bazan zauna da mazinaciya fasik'a a cikin gidan nan ba idan ita bazata bar gidan nan ba toni saina tafi," ta fada tana girgita jiki saboda tsabar masifa. Kallonta baba yayi yace "a'a lami wai da a duba lamarin kafin........." "A duba lamari koh? To bari kaga idan na tafi gidan mu Kai saika zauna da mazinaciyar," ta fada tana yin hanyar dakinta. Ita kuwa Hibbah kuma fashewa tayi da kuka tana karanto _inna lillahi wa inna ilaihira ji'un_, su Abu karime da dije ne suka karaso kusa da ita suna lallashinta. Shi kuwa Baba da sauri ya Sha gabanta yace "haba lami ai ko bata aikata komi ba kikace tabar gidannan saita Bari," ya juyo ya k'araso kusa da inda Hibbah take ya nuna ta "ki tashi ki barmin gida tun kafin na b'ab'b'allaki," Hibbah ta kalleshi hawaye na bin fuskarta tace "Baba idan na bar gidan nan ina zani yanxu ga dare, baba baka tsoron wani abu ya cutar dani?" Baba yace "ni dai kawai nace ki barmin gida!" Ya kuma d'aga murya. Rahmatu wadda ta shigo yanxu ta kalli Hibbah
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63