Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 43

Chapter 43

Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ajiye a gefen gado. "Zan fita ne tunda ruwan ya tsagaita" ya d'anyi murmushi ya kad'a Kai wannan yanayin bazai manta shi ba don a yanzu Hibbah ta zama mallakinsa, ya fice. Ta k'urawa kud'in idanu har yanzu k'amshin Faheem ke mamaye a d'akin, wani murmushi da bata san dalilin yinsa ba ya sub'uce a leb'enta, wannan shine k'auna da so Wanda yake daga Allah ne, ta dad'e tana son bincike da bin k'wak'wk'wafin abin amma sai zuciyarta ta dak'ile zargin, domin abune da take ganin har abadan bazai faru ba taya ma Faheem zaice yana sonta har ya aureta. Wannan ikon Allah da yawa yake, surar Faheem ta fara hango wa sai taga kamar abinda wuya cikakken mutum mai mutunci wayayye, shi komai nashi a tsare yake ta duba tsarin gidansa da yadda yake tafiyar da rayuwarsa. Ko Kausar matarsa ta isa ta firgita 'ya mace, idan banda ita da ta zauna da su ta karanci tsarin Kausar akwai abubuwa da dama data kuskure su bata kuma damu data gyara ba, wai kuma cikin ikon Allah ita d'in dai yake ra'ayi to me take dashi daya ja hankalinsa. Kausar da Faruq sune k'adangaren bakin tulu, ita dai baza ta iya auren mijin Kausar ba kuma Yayan Faruq, don haka batun Faheem fa sai hakuri. Hibbah lallai Allah ya bata baiwa, wasu lokutan tana ganin Kausar takai k'arshe a sawun had'ad'd'un mata, wai me mace 'yar gayu irin Kausar yaya za'ayi ita ta burgeshi. A shirmen tunaninta kenan Allah sarki Hibbah rashin sani yafi dare duhu soyayya had'uwar jini ne, Faheem shi yaga abinda ya burgeshi harya yamutsashi da rud'ashi akan 'yar budurwar daya kira Hibbah. Sark'a Mai rikitaniya ya ta iya da Faruq idan yaji labari ga kuma bawan Allah Jabeer da ya mik'a wuya magana tayi k'arfi don kowa yasan dashi, furucinsa ya shiga ranta. " _Hibbah ba zan tab'a wulakantaki ba har abada ni nasan darajarki, a yadda na ganki kinyi min kuma in sonki kamar raina shiyasa nake so muyi aure donki samu 'yancin kanki, Hibbah kina da daraja da baiwa amma sai mai hankali da nazari ne zai gane nasan ke baki san haka ba_" Tana jin fitarsa saita samu........... *Ga wannan ba yawa, banjin dad'ine ina barar add'ar Ku* *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:26 PM] Maman Najma Author P1: πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“ *RAYUWA* page4⃣1⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“ *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION* D.B.W.A *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* *Fans naga dukkan sak'onninku na gode da addu'o'in ku Allah ya saka da alkhari, ya k'ara donk'on k'auna🀝* Taro ne na mutane hud'u kacal don tattauna muhimmiyar magana domin kowanne a cikinsu zai bada gudunmawa da kuma taka rawar gani. Ya gyara xama yana kallonsu d'aya bayan d'aya don sun bada dukkan hankulansu don sauraronsa "kin bani mamaki Aysha zumunci fa babban abune Wanda zai iya Kai mutum aljanna ina so ku zama tsintsiya d'aya mad'aurinku guda dole ne ka sowa d'an uwanka abinda zaka soma kanka shine cikar imani, abubuwa suna ta faruwa ba akan idanuna ba saboda ni ba maxauni bane. Amma banji dad'in abinda kikayi ba Aysha kinsani komai lalacewar Faruq naki ne koda d'an ta'adda ne mai kisan mutane don haka ni d'innan zan tirsasaki dole kiso abinda yake so koda ke baki sonshi, indai har kinason ki gama da ni lafiya, ni banga dalilin zak'ewarki ba don Hana ruwa gudu kice bazai auri yarinyar da yake so ba, ke ba Wanda kike so muka amince kika aure shi ba? Waya hanaki? Haka ake rayuwar duniya idan jifa ya wuce kanka ya fad'a kan ko waye ko? Wato ke kinsamu shiya rasa. To bara na fad'a miki matuk'ar kina son shiri dani to karki sake saka baki a cikin maganar indai ba alkhari xaki fad'a ba wannan shine dalilina na Tara Ku anan gobe insha Allah zanje mu gana da marik'in yarinyar Alhaji Sani, Kai Faheem kai zaka wakilceni ka jagoranci komai babu shakka nasan baka da wata matsala. Next week zanyu tafiya kuma sati biyu zanyi insha Allah, kayi k'ok"arin gama duk wani shirye shirye za'a d'aura aure ne kafin Faruq ya tafi Germany Inda zaiyi contract d'insa bazai wuce wata biyu ba zai dawo idan ya dawo sai ayi binkin, shikenan idan babu Mai magana zaku iya tafiya" Aunty Aysha ta girgiza kanta don ranta ya b'aci d'aci take ji a ranta tamkar ta rushe da kuka don bak'in ciki shikenan ta faru ta k'are, gashi Daddy ya d'ora mata laifi don shi daman a duniya babu abinda yak'i jini kamar ka tab'a Faruq to fa bashi da mak'iyi kamar kai, Faruq baya laifi a gurinsa duk abinda akace yayi zai k'aryata ya dinga bad'an da bashi da dalili wai ansa mishi yaro a gaba, wannan shine sanadiyyar lalacewar Faruq. Ya ilahi, babu tsimi babu dabara sai daga Allah, kansa kamar ya rabe biyu ga zuciyarsa data tsananta bugawa bai tab'a shiga tashin hankali irin na yau ba, ya rasa a wane hali yake ciki sai dai hakuri, don Faruq k'aninsa ne kuma babu yadda zaiyi don tuni ya yanke hukuncin sadaukarwa da Faruq soyayyarshi, sai dai son Hibbah ya illatashi ainun don allah ne kad'ai yasan yadda yake matuk'ar son Hibbah a ransa, ji yake inama bai furtawa Hibbah Kalmar so ba ya barsa cikin ransa, dominzata zama Matar k'aninsa kuma dole akwai abinda zai had'asu yasani tunda son gaskiya yake mata duk sanda suka had'u dole ne wani abu ya motsa zuciyarsa. Sai yaji wani abu marar dad'i domin yaci burin *RAYUWA* da Hibbah. Ya katse masa tunani "baka ce komai ba Faheem" bai yarda sun had'a idanu da Daddy ba don zai iya fahimtar yanayinsa ya sauya, har shima ya ja masa bak'in layi kamar yadda ya yiwa Aysha yanzun nan, ya d'anyi gyaran murya don yawun bakinsa ya bushr akan harshensa "insha Allah babu matsala Allah ya tabbatar da alkhari" "ameen Faheem Allah ya yi muku albarka, ka gaishe min da abokina Nawaz" yayi murmushin k'arfin hali yayi musu sallama. Faruq ya bishi da kallo yana wani tunani akwai abubuwan da ya jima yana nazari da son ganosu akan Faheem ya sanya mishi ayar tambaya, labarin zuciya a tambayi fuska ya gano Faheem baya son mu'amalarsa da Hibbah, yana ganin wani yanayi a tattare dashi a duk sanda ya gansa da Hibbah sai dai kawai bai tab'a fitowa k'arara ya nuna da'awarsa ba balle ya tofa wata kalma Mara kyau. Aunty Aysha ce 'yar Hana ruwa guru saidai ta manta gaba da gabanta shima shiyasa ya kawo k'ararta wajen Daddy inda ko tak'i ko taso dole tabi, ko d'an shaid'an ne shi ba d'an bariki ba saiya auri Hibbah. Ba k'aramin dad'i yaji ba shiyasa yake k'aunar tsohun nasu mutum ne mai jajircewa akansa baya k'aunar b'acin ransa, Daddy ya dafa kafad'arsa fuskarsa da murmushi, tunaninsa ya katse yayi dariya "na gode Daddy banson me nayiwa Aunty Aysha ba bata sona yanzu." "Ya isa banson wannan ba kaga nayi mata barazana da fad'aba kace zaka kawo mata raini babu ruwanka kabar ni, ni da ita tunda duk ni na haifeku kuma nasa albarka a cikin wannan aure nayi addu'a, Allah ya albarkaci lamarin ka kwantar da hankalinka idan kaga ba'ayi ba to Allah ne bai k'addara za'ayi ba.

Table of Contents

Chapters

63 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});