Chapter 49
Chapter 49
a kaina ashe duk yaudarace yana sone ya aure ni daya samu abinda yake so sai ya rabu dani, don yaga bani da gata bani da galihu yanson ya wulakanta min rayuwa don kawai ya cika burinsa akaina." Sai kuma ta fashe da wani kuka mai ban tausayi, Aunty ta janyota jikinta "Hibbah kiyi shiru Allah yana tare dake shine gatan mu kuma nima ina tare dake" da hawaye tab a kan fuskarta ta d'ago tana kallon Faheem dasu mamy sannan ta dubi Aunty "na gode Aunty da kulawar da kika nuna min Allah ya saka da alkhari, Aunty wai da gaske ne Daddy ne mijina yaushe aka d'aura auren?" "Waya fad'a miki Hibbah?" Ta d'anyi shiru "Faruq ne ya fad'a min, don Allah Aunty idan da gaskene ki rok'a minshi ya sake ni don wallahi Aunty bazan iya auren mijin Aunty Kausar ba kuma na d'auki Daddy kamar uba taya zan iya zaman aure da mutumin da nake jin nauyinsa nake bashi girma fiye da kowa a duniyar nan Aunty kuyi hakuri don Allah bazan iya zaman aure bashi ba" maganar Hibbah ta d'aga hankulansu duka musamman ma Faheem da yaji wani abu ya tokare shi, Aunty ta dubeta duk tayi sanyi "Hibbah ki tausayawa rayuwar d'an uwana wallahi Yaya yana sonki sosai wannan rashin lafiya da kika ganshi duk a sanadinki yake yi saboda Daddy yace lallai saiya rabu dake......" Nan Aunty ta kwashe komai ta fad'a mata, Hibbah ta kafa ta gumi ta ma kasa cewa komai tana tunanin wannan hukuncin na ubangiji, wato abinda baka tab'a zato ba saikaga ya sameka, matsayin da baka tab'a tunanin zaka taka ba sai Allah ya baka shi. K'ofar aka bud'e Kausar ce rik'e da kwandon abinci Saudat ta rik'o hannun Nawaz ita da Safiyya suna biye da ita, da gudu Nawaz yaje ya rumgume ta "Aunty kinga daddy bashi da lafiya baki zo kin dubashi ba kin gudu gidan ummanki, Aunty nima bazan kuma zama a wajen momy ba idan zaki tafi ki tafi dani zan biki" ta k'ank'ame Nawaz tana shafa kansa tace "Nawaz ba inda zan kuma kowa ina tare da kai" yayi tsallan murna "da gaske Aunty Hibbah?" Ta gyad'a masa kai ya kuma rumgume ta. Kausar ta ajiye kayan ta tsaya tana kallon su cike da tausayin kanta tabbas tayiwa kanta da yanzu duk wannan soyayyar da Nawaz yake yi Mata da ita zai yiwa. Ta kalli Faheem shima kallonsu yake yi yana murmushi, yaji dad'in kalaman Hibbah hakan na tabbatar masa data amince zata zauna dashi kenan, su Aunty ma dasu momy sai murmushin jindad'i sukeyi. Hibbah kuwa ta kasa d'aga ido ta dubi Kausar saboda nauyinta da take ji, kuma bazata iya kallon idanun Aunty tace bata son d'an uwanta ba hakan zai zama kamar butulci da cin fuska shiyasa bata da wani zab'in daya wuce ta amince da auren, ikon Allah kenan wai akanta har Faheem yake da ciwon zuciya gashi a gadon asibiti a kwance yana ciwon so. Saudat ta k'araso kusa da Hibbah tana murmushi cikin sigar tsokana tace "Aunty Hibbah matar Yaya" dukansu suka sa dariya banda Kausar da duk abin duniya ya isheta duk danasani da nadama ta addabi zuciyarta, yayin da Safiyya take bak'in cikin faruwar wannan abun take kuma jin tsanar Hibbah a zuciyarta sai wurga mata harara take yi. Hibbah tayiwa Saudat hararar wasa, Saudat tayi kamar bata gani ba ta cigaba "mamy da Aunty nasan kune akan komai don momy ba shiga zatayi ba, yanzu yaushe ne zamu sha bikin babban Yaya kusan mune manyan k'awaye" wani bak'in ciki ya tsayawa Safiyya ji take kamar taje ta doki Saudat, Hibbah tayi k'asa da kanta cike da kunya da kuma jin wani iri don gani take kamar cin fuska ne abinda Saudat take yi, tana yi ne saboda Kausar wanda ita tana ganin rashin dacewar hakan. Aunty tace "Kai Saudat irin wannan zumud'i haka ki bari su Daddy su dawo sai su tsaida mana rana" Saudat ta gyad'a kai "sai mu fara shiye shirye kenan." Tsayuwa ta gagareta ta samu gefen gadon Faheem ta zauna kanta a k'asa tana tunani yanzu shikenan Faheem ya zama nasu su biyu, ta d'ago kai ta dubeshi shima ita d'in yake kallon yana tausaya mata don yasanta akwai zafin kishi yayi mamaki ma da bata wani tashi hankalinta ba sosai yayi mata murmushi, ta kawar da kanta gefe. Su Abba ne suka shigo da sallama suka amsa musu tare da yi musu sannu da zuwa, Abba ya dubi inda Hibbah take Nawaz yana zaune akan cinyarta kanta yana k'asa yana murmushi yace "surikarmu ki d'ago fuskar taki mu gani mana kinsa mana yaro kwanciya ciwon so, naga ma ya samu lafiya saboda ya ganki" cikin sigar barkwanci Abba yake maganar saboda Abba akwai shi da barkwanci, Hibbah ta kuma k'asa da kanta cikin kunya, su Daddy dasu momy sai murmushi suke yi Faheem kuwa shima k'asa yayi da kansa don jin nauyin maganar Abba. Saudat tace "surikar su Abba ki d'ago kanki su ganki" ta fad'a tana mata dariya, mamy tace "kai Saudat kin takurawa surikata fa, zan fara rama mata" momy tace "gaskiya kam Saudat kin takurata da yawa ke a haka ake Matar Yayan?" Daddy yayi dariya "nifa na k'osa naga fuskar wannan mai sa'ar data sace min zuciyar Faheem haka har ya kasa nutsuwa saboda rashinta" su aunty suka kwashe da dariya. Gaban Hibbah ne ya shiga fad'uwa jin muryar da bazata tab'a mantawa ba zuciyarta ta shiga harbawa da sauri ta d'ago kanta don tabbatar da muryar da taji, a hankali ta d'ago kanta ta zubasu akan Daddy cikin mugun hargitsi da rikici ta tashi tsaye tana kallon daddy murya na rawa tace "baa.......baa? Baba kaine?" Jin muryarta ya hargitsa Abba muryar da yafi so a duk duniya kuma bazai tab'a manceta ba har *Abadan* ya jiyo cikin fargaba yace "Aysha....." Hibbah ganin fuskar Daddy yasata zubewa a k'as............... *by* *Mamyn Najmah* [10/26, 9:27 PM] Maman Najma Author P1: 📝🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *RAYUWA* page4⃣6⃣ *NA* *MAMYN NAJMAH* 🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓🍓 *DEDICATED TO AYSHA ALIYU GARKUWA* Aunty ce tayi saurin tarota ta fad'o jikinta, Faheem besan sanda ya diro daga gadon ba yayi wajenta da sauri yana ambaton sunanta su momy ma suka matso suna jijjigata, mamy ce ta d'auko ruwa ta fara shafa mata a fuskarta. Abba kuwa da hanzari ya fita ya kira Dr, suna shigo Hibbah tana farkawa Dr ya k'araso ya shiga dubata ko da wata matsala, ya gama dubata ya tabbatar musu da lafiyarta sannan ya fita. Hibbah tayi shiru kawai kallon Daddy take yi tana son ta gano wani abu game da Daddy tana kuma tambayar kanta, me ya kawo babanta birni dama babanta yana da aure a birni amma bai tab'a gayawa su Inna ba kuma akace bai tab'a haihuwa ba sai akanta idan haka ne su Aunty Aysha kuma 'ya'yan waye? Bata da amsoshin wad'an nan tambayoyin nata ya zame mata dole ta tambayi daddy don shi kad'ai ne zai iya amsa mata wad'annan tambayoyin. Daddy da Abba sun shiga tunani Daddy ya tafi wani tunanin akan Hibbah yana son yasan wani abu game da wannan razanar da tayi ta ganinshi don ta bashi tsoro, yayin da Abba kuma ya tafi tunani
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63